← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 84

Sashe 33

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maganganu da yawa, daga karshe yace kada na ara kiransa.... Sai kuma ya yi shiru, Hanam dake jin duniyar ta mata shiru tun a maganarsa ta farko ta ago ta kalleshi, idan ba Jabeer aka aura mata ba to waye ?!!. Hanam, na aura miki wanda na aura miki ne dan na isa da ke, nasan da cewa ke me biyyayace ga duk abinda nake so, nasan baki tab'a bijire min ba, kuma nasan cewa wannan karon ma bazaki bijire ba.... Ya kuma yin shiru yana ci gaba da kallon reaction inta, har yanzu bata ce komai ba kallonsa kawai take, ita bu atarta taji waye ya aura mata. Hanam, ba kowa na aura miki ba face UCHENNA! MARYAM POV. Tafe suke akan titi, ita da sabbin awayenta ne, Aisha da Zara, hira suke ta yi amma Maryam bata saka musu baki ba, dan hira suke akan wani kyakyawa dake a block3. Tun da Maryam ta fara zuwa makarantar ta lura da an matan ajinsu basu da aiki se hira akan wani kyakyawa, kuma ita jikinta na bata cewa Tafida ne, kuma tunanin nata baije ko ina ba ta tabbatar da hakan lokacin da Zara tace. Wai ke Maryam baki sanshi ba ?, a block3 inku yake fa, sunansa Tafida Damm!, gaban Maryam ya fa i, wani abu me kama da kishi nasan taso mata, ji take kamar ta koma Makarantar ta tara duka an matan ajinsu, musulmai da Cristian, turawan da ba ar fatar duka tabisu da mari aya bayan aya, ciki kuwa harda su Zara dake tareda ita.... Ya za'ayi tace bata san shi ba, ke babu budurwar da bata san shi ba a Alaro city gaba Maryam ta juya ta kalli Aisha, sai kuma ta kawar da kai taci gaba da kallon hanya. Ke nifa wannan gashin kan nasa kawai nake san tab'awa, daga nesama fa har she i yake, gashi jiya dana ganshi naga gashin nasa ya ara tsayi Cewar Zara, idonta har wani kyallin murna yake. Kede bari Zara, wallahi sumar nan tasa tana burgeni, shi tsiyarsa aya, ba ya yiwa an mata magana sai de maza, kuma mazan ma ba sosai yake musu magana ba, ke nifa ina ganinma jinin sarauta ne Maryam tayi shiru, sumarsa ?, itama de taga a kwanakin nan ya fara tara suma, wata ila so yake ya tara kamar ta wannan hoton, sai tunanin yaso ya bata dariya, taji itama tana san ta tab'a sumar tasa ta ji, ita zata iya hakan, amma su fa?, kawai de suna karanta wasi ar jaki ne. Hmm aisha sai kingan shi yana magana, damn!, i can't wait to sit on that mouth.... Sai goben ku Maryan ta fa i tana jara saurin tafiyarta ha i da shan kwana ta shige block finsu, dan idan ta tsaya ta ci gaba da jin zantukan da suke zuciyarta kan iya bugawa, ko wata ilama ta yanke jiki ta fa i, ko kuma ta make aya daga cikinsu, tafiyar tata itace mafi a'ala. Me yake damunta ? Aisha ta tambaya girarta a ha e waje guda tana duban Zara, Zara ta dage kafa a alamun bata sani ba tareda fa Ni ya za'ayi na sani, wata ila bata da lafiya ne wani irin rashin lafiya kuma ?, bayan alau muke tare da ita yanzu Zara ta tab'e baki cikin fa Allah yasa lafiya, kinsan ita Maryam ba san surutu take ba, wata ila damunta mukayi Daga haka sukaci gaba da tafiyar su suna ci gaba da hirar da suka fara. Maryam ta tsaya a ofar gate in gidansu, sannan ta saka hannunta a cikin jaka ta zaro remote control in da Tafida ya bata domin ta ri a amfani da shi wajen bu e gate din gidan. Ilham ce ta fito daga gidansu hannunta ri e da leda, tana wala mata kira, Maryam ta tsaya daga bu aramar ofar da take shirin yi, ta juyo ta kalli ilham Ina yini Anti Maryam Ilham ta gaisheta yayinda ta araso kusa da ita, Maryam ta alo murmushi tana amsawa, ilham ta mi a mata ledar hannunta tareda fa Wai gashi inji Mamanmu, tace na kawo miki wai mamarta ce ta aiko mata daga kano Maryam tasa hannu ta karb'a, a lokacin da itama tata mamar ta fa o mata a rai. To ki ce nagode Ilham ta fa i bayan ta juya. Maryam ta arasa bu ofar ta shiga. A parlo ta aje jakarta ta makaranta, ta shiga kitchen ta aje ledar da Ilham ta bata, sannan ta shiga fito da kayan dake ciki. Kub'ewa ce da kuka, kanwa, sob'o harda jan lalle, Maryam ta yi murmushi, tana hango yanda za ta yi amfani da kayan, dan dama tana bu atar irinsu, kuma bata san inda zata samu ba. Maman Ilham kamar da ta bu e zuciyarta ta gani, aiko idan an jima za taje tai mata godiya kafa da afa. Ma'aji tai wa kowanne, sannan ta auki lallen ta fita a ranta take fa in, yau kuwa tuwo za ta yi, dan dama tayi missing insa, lalle kuma sai jibi za ta yi, jakarta ta auka a inda ta aje sannan tayi sama. Ta shiga akinta ta aje jakar a inda ta saba, sannan ta aje lallen a cikin bed side drawer, ta cire hijabin jikinta ta shiga ban aki, bayan fan wani lokaci ta fito, yau azumi take, dan haka ba abinci zata ci ba, koda safema iyaka na Tafida kawai ta girka, yanzun ma bazata tsiri yin tuwan ba sai anjima. Balcony in corridor in nan ta tafi ta zauna akan lilon dake wajen, tana jin da in iskar garin, dan ba'a jima da sukewar yayyafi ba. Sai kusan shida ta tashi daga wajen, ta nufi kitchen bayan ta dauko wayarta da ring light din naan, ta jona Ring light in, sannan ta saka wayarta a ciki, ta shiga daukan vedio tana recording girkin da take, ita bata iya editin ba, sai idan Tafida ya dawo yake mata sannan tayi posting. TAFIDA POV. You...._ _you got the keys to my heart, my baby never let me down_ _My baby never lets me down, my baby never_ _You...._ _You deserve a crown, my baby never lets me down_ _My baby never lets me down, my baby never_ _Baby you're my dealer, you my energy _ _I will give you my love, i will give you all of me..... Sassanyar wa ar my baby, wanda Ayra Star da Bien suka rera ce ke tashi a cikin motar tasa, a kwanakin nan yana cikin nisha i sosai, kuma ba sai an tamabayi daliliba, Maryam ce sila. A da shi ka ai yake rayuwarsa, yanzu kuma ya samu abokiyar rayuwa, jinsa yake enough, baya bu atar ari, ji yake ya gama samun komai na duniya, bashi da wani wayo lokacin da iyayensa suka rasu suka barshi, ya taso a wajen Fulani, saide sam babu wata sha uwa a tsakaninsa da ita, me martaba kuwa yakan kwana uku ma bai saka shi a idonsa ba a lokacin. Bayan ya gama secondary kuma ya koma india, a can ne ya samu kulawa, soyyaya da aunar an uwa, duk a da inma yakanje indian ziyara, amma zai iya cewa gidansa a india yake, domin farin cikinsa gaba aya yana can. Tinaninsa ya katse, a sanda ya araso ofar gidansa, gidan da a yanzu ya fi masa haske fiye da da, a duk sanda zai tako afarsa cikin gidan sam baya san fita, yana so yaci gaba da zama da Maryam, koda babu wani kusanci tsakaninsu, sautin bugun zuciyarta ma ka ai ya isheshi kasancewa cikin farin ciki. Yasan i yanzu tana kitchen, dan haka yana shiga sama ya yi, ya yi wanka ya sauya kaya zuwa ash hoodie da ba in chinos trouser, ya sau asa cikin farin ciki da aukin ganinta. Hannu ya kai ya mur a handle ofar, tsaye ya ganta a jikin cabinet tana aukan plate. Tafida ya kasa kunne yana sauraron bugun zuciyar ta, yana jin abinda ya saba ji a kullum idan yana hakan. A lokacin kuma ta jiyo ta kalli ofar dan taji lokacin daya turo ofar, tana ganinsa zantukan su Zara suka dawo mata, sai ta yi saurin kawar da kanta taci gaba da abinda take. Sannu da zuwa Muryarta ta fa i sanda ya araso cikin kitchen Yauwwa Na gama recording Ya gya a kansa sannan ya arasa zuwa jikin socket din data jona ring light in ya cire, ya auke ring light in da wayar ya fita. A kan danning ta jera masa abincin nasa kamar kullum, bayan ta gama, tana kallonsa a parlon yana daddana wayarta, da alama editing in yake. Na gama abinci Tafida ya jiyo ya kalleta, sai kuma aje wayar akan sofa ya taso ya araso zuwa danning in, zama yayi akan kujera yana kallonta, ita kuma ta shiga bu e warmers in tana arin zuba masa abincin, amshin miyar ya daki hancinsa. Tuwo kika yi ? Muryar sa ta fito a lokacin da yake kallonta, itama ba tare da ta kalleshi ba tana saka tuwan semolina in da tayi a plate tace. Eh, da miyar kuka A ina kika samu kuka ? Maman ilham ta aiko min ya gyada kansa a hankali, rabonsa da tuwo ya manta ko a hadejia baya samu yaci shi. ________________ _wani abu yana konewa a nan , shin kunaga Hanam zata amince da auren Uchenna, itafa kallon Cristian take masa har yanzu, amma de ban sani ba ko har yanzu yana ruwa_ _bari de nayi nan, kuyi comment ra'ayin ku pls, ngd sosai_ -SAI KASKA CE YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Arewabooks @18saikaska Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *This one's for you 'Yar Hajiya* *BABI NA ASHIRIN DA BIYU (22)* Lokacin da akayi sallar magariba Maryam na zaune a parlo ta aje kayan shan ruwanta a gabanta, tuwan azu ne sai sob'on da ta yi, tana addu'a Tafida ya sau o daga sama da alama masallaci zaije, ya tsaya yana kallonta da mamaki. Wifey wai azumi kika yi ? Maryama ta shafa addu'ar wadda rabinta gaba aya akan samun sau in Tafida ne,
Chapter 33 · 0% Book details