← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 84

Sashe 3

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin muryarsa ma abociyar kamewa da nutsuwa,me taushi da kuma zurfi wai wani mara lafiya ne aka kawo shi, kuma ana bukatarka, shine dr. ola yace a kiraka ok to muje na ganshi Daga haka suka wuce inda aka kwantar da mara lafiyar, dubashi yayi yaga kuma matsalar tasa tana bukatar tiyata, dan haka ba b'ata lokaci suka shiga dakin tiyatar dashi. Cikin nasara akayi aikin aka gama, ya fito yana bawa nurse bayanan magungunan da ya kamata a bawa mara lafiyar, office dinsa ya shiga, daga nan ya zarce ban aki. Hannunsa ya shiga wankewa a gaban sink, bayan ya gama kamar da akace kalli mirror idansa yakai wajen, gabansa ne yayi mummunar fa uwa, sbd abinda ya gani, hankalinsa yakai kololuwa wajen tashi, a dugun zume yayi gaban mirrorn yana dudduba fuskar tasa, wayar idansa wadda take light blue itace ta riki e ta koma ja, wannan abun ba ba o bane a wajensa, amma kuma a kwanakin nan abun ya fara yawa, a da sai yayi wata nawa abun bai tashi ba, amma yanzu kusan kullum sai ya tashi, yanzu har takaima idan nasa na sauya kala ba tareda yaji a jikinsa ba, hannu yakai ya ri e kansa tareda lumshe idanunsa, addu'a yake san yayi amma bakinsa yayi masa nauyi kamar kullum, yasani dole abun nasa ne zai tashi, haka ya bude idonsa ya arasa ya fita waje, da hannunsa yayi nuni ga inda wayoyinsa suke nan take suka tashi suna yawo a iska har suka karaso kan hannun nasa, da kyar ya samu ya fice daga asibitin, kuma yanata jugewa hada ido da kowa, dan kada wani ya samu yaga kalar idon nasa. Cikin motarsa ya shiga, ya sakata a lock, ya dafe kansa a jikin sitiyari, yanajin abinda ya saba ji a duk lokacin da abun zai tashi, bayan wani lokaci ya dago da kan nasa, ya fita hayyacinsa gaba daya, kwayar idanun nasa ta ara komawa ja, bakinsa ya bu e nan take wasu dogayen fi i suka sauko daga ha waransa na sama, ya riki a ya koma dodo, me ban tsoro, gaba daya jikinsa rawa yake, sai ya fara fisge-fisge, yana barazanar kifar da motar, wannan shine halin dayake tsintar kansa a ciki a wasu lokutan. *BINYAMINU USMAN POLYTECHNIC, HA'DEJIA, JIGAWA STATE NIGERIA* Wasu an matane guda biyu tafe akan titin fita daga makarantar, yanayin tafiyar sune kadai zai nuna maka cewa a gajiye suke gaba aya. aya bakace sanye da atamafa da kuma mayafi, yayin da ayar ta kasance fara amma ba sosai ba, sanye take da hijabi har kasa, wanda ya 'boye atamfar dake jikinta. wadda ke sanye da mayafin ta buga tsaki tana fa akin banza, wallahi buzuwa bai sanni bane, shiyasa yakemin abinda ransa ke so, amma bari yazo sai na masa wankin babban bargo, yanzu haka shashanci ya tafi da motar, ni ya barni nan ina fama da rana wadda ke sanye da hijjabin ta kalleta, yayin da suke ci gaba da tafiyar, dan har suna hango gate din fita daga makarantar ke kuma wallahi Badar baki da hakuri, dan allah ki dinga shan ragowar ruwan alwalar yamma Badar ta kuma yin wafa Ai ni Maryam ba zan iya da wannna halin naki ba, ke baki san mutanen yanzu idan baka ci uban su ba bazaka zauna lafiya ba kide dinga ha Maryam ta fa i tana dubanta, basu kai da arasawa gate din ba sai ga motar da ake zuwa daukan Badar din ta shawo kwana, Badar na ganinsa tayi wafa. Tun kan ya karaso yasan cewa dama yau ya shiga tara, dan Badar ba zata kyaleshi ba, wata ila yau yayi ta aikinsa dan yaya abokinsa ya biyewa har suka auki wasu an mata a motar, sa'arsa aya akwai Maryam, yasan zata tausheta, a gabansu yayi parking, Badar ce ta fara bude kofar motar a fusace ta shiga, sannan Maryam ta zagaya ta ayan bangaren ta shiga itama, aiko bai shaba saida Badar tai masa tass, kuma wai duk da hakan ma Maryam in na bata ha uri. Da haka har suka araso unguwarsu wato unguwar garko, a bakin wani lungu suka tsaya Maryam ta sauka Zaki zo an jima ne ? Badar ta tambaya wata ila ki ganni, amma bande sani ba ko wani aikin zai ri dan allah kizo fulanys kitchen fa ta saki wasu sabbabin recipes gaskiya Badar kinci amana, wannan ai cin amana ne, taya zakiyi tiktok baki fa amin ba? ke wallahi jiya da daddarene nayi, amma ai nayi saving vedios in, idan kinzo sai na nuna miki amma ai azu baki fa amin ba ke mantawa nayi amma idan kin zo zan nuna miki to sai na zo Ta fa i tana rufe musu kofar, buzuwa yaja motar sukayi gaba, dan ita gidan kakar Badar in a gaba yake, dan a gidan kakarta take da zama, iyayenta kuma suna kano, itace ka ai ta dawo hadejia tun tana karama, kuma tun suna yara suke kawance da Maryam, duk da ita mahaifin Maryam ba wani ku i gareshi ba sa'banin mahaifin Badarriya wanda ya kasance me dukiya. Maryam tayi ta shiga cikin layin nasu wanda yake dauke da kwatanni, har ta kawo kofar gidansu sannan ta sa kai, da sallama a bakinta ta shiga mahaifiyarta ce ta amsa mata ah-ah har kin dawo ? kai maanmu, yanzun ne har ?, na jima fa Haka suke kiran mahaifiyar tasu, da mamanmu suke ce mata, bayan haihuwar annentane suke cemata maanmu, dan basu iya kiran sunan ba, shiyasa suma suka koma cewa maanmun, gaba aya yaran gidan biyar ne, babbar yayarsu fati wadda aka mata aure shekara hu u baya, tanada yaronta guda aya, sai ita Maryam in, bayanta kuma sai kannenta an biyu hassan da hussain, sai kuma auta muhsin. Maryam ta cire hijjabin dake jikinta ta rataye a jikin igiyar shanyarsu a lokacin maanmu ke cewa ai ni gani nayi kunyi sauri wallahi Ta fa i tana gyara wake a cikin wani farantin silver, Maryam ta shiga akin dake a mazaunin nata a gidan, bayan auren yayarta fati, dan da su biyu suke kwana a akin, jakar data saba zuwa makaranta da ita ta aje akan yar karamar katifarta, wadda take ame da bed sheet, ko ina a akin tsaf, duk da ba wasu kayan tarkace a ciki, domin jakarta ta kayace kawai sai dan abinda ba a rasa ba, da wasu littatafan ta na makaranta da dai sauransu, wayarta kirar huawei 6A irin london use din nance,wadda screen gard dinta ya faffashe ta saka a chargy, Badarce ta bata ita lolacin da babanta zai saiya mata wata wayar. aramin hijjabin data saba sakawa idan tana gida ta dauko ta saka sannan ta fito waje, kujera ar tsugunno ta janyo ta zauna a rumfa tana karbar tray in dake hannun maanmu tareda fa ina auta ne ? Ta tambaya ganin bataji ko motsinsa ba a gidan baki ganshi a waje ba ?, wai yashi aka kawo a gidan malam isa za'ayi gyara shine su khalil suka zo suka ja shi ya fita Maryam tayi dariya tana watsar da dattin data tsinto a cikin waken auta kenan kinyi sallah ne ? eh munje hostel munyi Tun daga bakin kofa suke jiyowa hayaniyar hassan da hussain, sai gasu sun shigo gidan da sallama, maanmu da Maryam suka kallesu a tare, a fuska kammaninsu daya, amma a hallaye kam sun banbanta sosai masha allahu, kace yau de bazamuyi asarar cefane ba, tunda ke zakiyi girki yau hussain ya fa i cikin zolaya, dan shi dama akwaishi da zolaya da kuma sakin fuska, ba kamar hassan ba wato ni idan ni nayi kenan asara kuke ? Hussain ya nemi kujera ya zauna shima, hassan kam dakinsu ya shige nifa bance ba maanmu, kawaide nasan idande yaya ce zatayi girki a gidan nan to bamu da haufi Maryam tayi musu dariya, dan idan da sabo sun saba wannan fa an nasu ince dai ko kunyi sallah ? haba maanmu sai kace wasu su muhsin, tun tuni ai mukayi sallah aa hussain ba haka bane, ya kamata na ri a tambaya sbd halin zamani hakane kam, ina wannan abun? kaji wala anci irin na hussain, yanzu autan ne wannan abun ? se kace wani kayan wanki ? Maryam ta fa i tana dubansa ah wannan abun mana, wannan yaron himmm yana waje akan yashin gidan malam isah, ni je ka ka o min shi ma, nasan ana jimawa zaka fara jin ana doke-doke, wasa ya koma fa a, daga haka kuma sai iyayen a su fara fitowa har fa an ya koma na iyaye yalo ne dama na siyo masa, bari naje na ka o keyarsa cewar hussain yana mi ewa tsaye saura kuma ka dokarmin shi ai wannan shine dole maanmu, sai na moreshi hussain ya fa i yayinda ya kai bakin kofa kai allah shirya mana Maryam na dariya ta mike da trayn a hannunta. Wata yarinyace tayi sallama hakan yasa su kallon kofa a tare Anti Maryam wai inji lawusa zata kawo kayan ha inta kayi mata miti fayif Maryam tayi murmushi, bata san sanda an area insu zasu waye ba, wai miti fayif kije kice mata yaushe zan mata ? Yarinyar ta fa i tana ficewa da an tsallenta, Maryam ta karasa zuwa rumfar da sukeyin girki, ta aje tray din waken a gefe ta shiga kiciniyar hura wuta, kukan muhsin taji yana dosowa kofar gidan, ya shigo hannunsa a akan idonsa, gaba daya kayan jikinsa a turbu e da yashi, hatta da kansa ya baci da yashin, takalminsa a hannu ya shigo ya fa a kan maanmu, hussain na biye dashi a baya, shi kuma yana shigowa yayi wuf ya fa akinsu, dan kar maanmu tai masa fa a akan dukar mata auta da yayi yi hakuri me sunan baba, ya hussain bai kyauta ba, ga yalon daya kawo maka Da kyar maanmu ta samu ta lallashi autan nata, dan dama ko ba'a taba shi ba ya iya kukan rigima, ina kuma ga an taboshi. Maryam ta girgiza kai tana ci gaba da aikinta, rayuwar gidansu na mata da i, duk da basu dashi amma suna cikin farin ciki, kuma haka halin mahaifinsu bai hanasu jin da in rayuwa ba.
Chapter 3 · 0% Book details