Sashe 42
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
10:00am* TAFIDA POV. Me ki ka dafa yau ? Muryar Tafida me zurfi ta tambaya, yayinda yake karb'ar wayar da Maryam ke mi a masa bayan ta fito daga kitchen, yayinda shi yake zaune a parlo bayan ya dawo daga wajen buga cricket. Maryam ta zauna a arshen kujerar tana amsa masa da. Shinkafa da wake Bana cin shinkafa da wake Miriam an juyo ta kalleshi, a sannan ne kuma taga abinda bata lura dashi ba azu, gefen fuskarsa ya yi ja da shatin circle, kamar an daki wajen da wani abu. Me yasa baka cin shinkafa da wake? Ya shafa sumarsa yana ci gaba da danna wayarta sbd yana mata editing vedion da ta yi recording na jiya dana yau, dan bai samu zama ba jiya. Haka kawai, dan ban tab'a ci ba, kuma babuma a inda zan ganta bare nace Har Maryam za ta yi magana sai kuma ta yi shiru, to a ina kuwa zai ci?, shida yake gidan sarki, sai ta sauya zance da. Da wasa nake maka ma, ba ita na yi ba, pancake ne da salad sai fried chicken Ya jinjina mata kai ka an, yana ara godewa Allah da ya sako Maryam a cikin rayuwarsa, kyawawan halayenta sune a kullum suke bata matsugunni me kyau a zuciyarsa. Bugun zuciyarta ya fara saurare, kafin ransa ya raya masa ya yi abinda zai saka zuciyar tata ta buga da sauri, dan idan zuciyarta na bugawa da sauri sautin yafi masa da in saurare. Karshen kujerar ya kara matsawa sannan ya kwanta, Maryam bata zata ba taji kansa a cinyarta, zuciyarta ta buga da arfi, wani abu ya shiga kaikawo daga zuciyar ta zuwa walwarta yana fa a mata cewar bazata tab'a sabawa da wannan yanayin ba. Wata busashiyar iska ta ha iye a ma ogwaronta sannan ta sunkuyar da kanta ta kalleshi, amma kuma shi ba ita yake kallo ba, Wayar dake hannunsa yake kalla yanaci gaba da dannata. Kafin taga ya ago hannunsa ya kamo nata hannun wanda ke auke da guntun jan lallen da ta yi da be ko e ba. Maryam ta rintse idanunta. Sakamakon hannunta daya sauka kan lallausa kuma me taushin sumarsa, sai kawai maganar su Aisha ta shiga dawo mata a walwarta, ranar da suke fa in suna so su tab'a sumarsa. Sumarsa nada laushi da santsi fiye da tata dan shi tasa naturally haka take, ita kuma tata an dabarune akayi ta koma kamar hakan. Muryarsa ta fito a hankali, cikin wani irin yanayi daya haddasa bugawar zuciyar Maryam sau biyu a lokaci guda. Wifey ki sosa min kaina, sumar ta min yawa yar ta iya lalubo sautin muryar ta, sannan tayi arfin halin furta. ayi take maka ? Yanayin yanda muryar tata ta fito, da yanda zuciyarta ta buga saida ya kusa saka shi dariya, amma sai ya dake, dan da gaske yana bu atar a sosa masa kan nasa, a hankali ya girgiza mata kai, wadda ya haddasa motsawar cinyarta. A'a ba ayi take ba, kawai de banajin da in yawan sumar dake kan nawa ne To me yasa ba zaka aske ba ? Sbd na yiwa Daadi al awarin bazan aske sumata ba sai naje india, kuma dama mun saba haka da ita, idan tana so na zo india sai tace tanaso na tabbatar mata da al awarina, ni kuma dan na tabbatar mata da zanzo in sai nace mata zan tara sumar kaina, tasan cewa bana so gashi ya min yawa, shiyasa take yarda dana fa i hakan, idan ina india kullum ita take min susar kai, dan ina so Duk da Maryam bata san wacece Daadi in ba, amma kamar ta fahimci cewa kakarsa ce, dan haka taji indiyawa suna fa awa kakaninsu a film, Da yar ta iya motsa hannunta a cikin tarin sumar kan nasa, hannunta ya nitse a ciki. Tafidah ya lumshe idonsa sannan ya bu e, ya yi kewar hakan sosai ba kadan ba. Dalilan da kam ara sakawa yaji Maryam har ransu shine tana sakawa yaji kamar yana india. A hankali take motsa hannun nata a cikin sumarsa. Wai ni Miriam da wani suna kike amfani ne ? Maryam Tijjani Muhammad Kansa ya girgiza mata wanda yasa cinyarta motsawa yanzuma. Ba'a school ba, a page inki, naga kamar babu suna ma Kai ta gya a masa tana motsa hannunta a cikin sumarsa. Umm, babu suna, na rasa wani suna zan saka ne Ya kamata ki saka suna Me ya kamata na saka, da ina tunain na rubuta 'MARYAM'S KITCHEN' A'a 'DAASO'S KITCHEN' dai Sai ta yi dariya yayinda shi kuma ya yi murmushi. Seriously ki saka 'MRS TAFIDA' Yanzuma dariyar ta yi. A'a 'MRS ESHAAN' dai Ummm yafi kam, bari na rutuba miki to To kuma iyaka Mrs Eshaan in za'a rubuta? Ya tambaya a sanda hannunsa ya danna edit account. MRS ESHAAN S KITCHEN MEK kenan ? Shiru Ya ratsa parlon, kafin Maryam ta tambayi abinda take san tambaya tun ganinta da shi a yanzun. Sultan (King), menene wannan a gefen fuskar ka? Tafida ya ago da idonsa ya kalleta, tareda lumshe idonsa, sbd yanda ta motsa hannunta a cikin sumar kansa dan ta tab'o har fatar kansa, sai kuma sunan da ta kirashi dashi 'Sultan', idon nasa ya bu e sannan ya kalleta da kyau. Joakim ne ya bugomin ball in cricket Ya juya idonsa yaci gaba da kallon wayar yana latsawa. Baka saka helmet bane ? Mantawa nayi Ai ko gashi wajen yayi ja, harma ya kumbura.... Wayarsa da ya baro a akinsa tana cahrgy ce ya ji kamar tana ara, dan haka ya motsa kunnensa ya tabbatar da aran wayar yake ji. Kansa ya aga daga cinyar Maryam sannan ya mi e, kafin yace mata komai aka wasa ofar gidan, a tare suka kalli ofar shi da ita. Bari na auko wayata, naji tana ringing Ok to nima bari na duba waye Shi ya yi sama ita kuma ta arasa ta bu ofar. Surprise! Abin da muryaryoyi biyu dake tsaye a ofar gidan suka fa i kenan, zuciyar Maryam ta takarkara ta yi tsalle a kirjinta, ta ji kamar zuciyar tata zata fito daga kirjinta ne. Zara da Aisha ne, ba wai bata san zuwansu gidan bane, bata so suga Tafida ne, dan har yanzu a cikinsu babu wanda yasan cewa ita matarsa ce, kuma har wa yau basu fasa zantuka akansa ba. yar ta lalubo murmushi ta yab'a akan fuskarta. Sannan ta ha iye wani guntun yawu, ta arasa bud ofar tana fa Ku shigo daga ciki Har ranta ba haka ta so ba, duk da ta ji da in zuwan nasu, sam bata fatan Tafida ya sau o yazo ya iskesu, zama suka yi akan kujera suna ta mata murmushi wanda itama take meda musu martani. Wai dama Maryam ke a gidan ma da hijiabi kike zama kullum? Maryam bata amsa Zara dake wannan batu ba, sai kawai tace. Bari na kawo muku abun sha... Ke bar abun shan nan wallahi Maryam ta gya a musu kai ka an, a lokacin kuma Tafida ya sau o daga sama, hannunsa ri e da aramin littafi da kuma pen, sai wayarsa data Maryam a ayan hannun nasa. Wifey ai wayar taki ba data.... Zuciyar Maryam ta dungura ta ara dungurawa, ta rintse idonta gam, a lokacin da take da tabbacin su Zara sunga Tafida, kuma sunji sunan da ya kirata dashi. Shima sai yanzu yaga cewar ba ita ka ai bace a falon, su uku ne, abinda yasa wayar tasa bata jima ba shine, me martaba ne ya kirashi, yake sanar masa da cewa Galadima bashi da lafiya, wai wani abu ya sameshi kamar junnu, yanzu haka ma sun Tafi india shida Fulani Sadiya da kuma Galadiman. Addu'ar samun sau i yabyi masa sannan wayar tasu ta are, ya auko wani aramin littafi da pen sbd yanaga kamar sunan nan da suka zab'a be dace ba, ya kamata ace sun iri wani sunan da ban, shine ya sau o yanzu. Cikin falon yaci gaba da takaowa yana fa i mukayi ne ? Zara da Aisha wa an da suka daskare a wajen suka kalli juna a tare, Tafida ne fa wannan a gabansu, Tafidan da a koda yaushe suke kwana da tunanin sa, yau shine tsaye a gabansu, kuma sune a cikin gidansa, bama wannan ba, awarsu Maryam da a koda yaushe suke yawan mata hirar Tafida dan suna ganin cewa block insu aya itace matarsa?, matarsa ta aure, Maryam fa ?. Gaba aya kuma sai kunyar Maryam in ta kamasu, dan sun tuna yanda suke yawan maganganu akan mijinta, amma me yasa btaa taba fa a musu ba?. awayena ne, wanda muke department a ya Kusa da ita ya zauna. Sannun ku da zuwa Abu aya yake yawo a tunanin su biyun, dama ance musu yana jin hausa, amma basu auka har haka ba, duk da suna ganinsa cikin kayan hausawan, amma basu tabbatar ba sai yau. Ki kawo musu abin sha mana Miriam Kai ta gya a masa sannan ta mi e ta nufi kitchen, shima kuma sai ya mi e yabi bayanta. Zara da Aisha suka ha a ido, kuma ba tare da suncewa juna komai ba, suka mi e da sauri suka bar gidan. Maryam ta gama jere drinks in data ebo a fridge akan tray, sannan ta juyo ta kalli Tafida dake tsaye a bayanta. Kin gama ? Ta gya a masa kai tana shirin wucewa, saida tazo wucewa ta gabansa taji sau ar hannunsa akan kafa arta ya dafata, zuciyar Maryam tayi rawa kirjinta, ta aga kai ta kalli fuskarsa, taga yanda yafita tsayi sosai, kamar tana tsaye a gaban wani dogon gini ne. Tafiya suka fara shida ita a tare kamar wata awarsa. Mamakine ya kamasu sanda suka tarar da babu kowa a falon, abun yaso ya bata dariya, dan tasan guduwa suka yi. Ah-ah ina kuma ba in suka shiga? Maryam tana ri e dariya tace. Sun tafi Sun tafi ?! Ya dawo mata da tambaya, ta gya a masa kai tana cije lebenta na asa dan ta hana dariyar dake neman kufece mata fitowa. __________________________ _To!, su Aisha dai anji kunya an ofe_ _wai ni meke goin a ha ejia ne ?_ _Ina godiya masoya