← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 84

Sashe 18

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

taje gidan Anti Fati ta tayata girki, amma a gidansu babu irin wannan cimakar. Cikinta ta bawa hakkinsa sosai, dan bata ci abincin ranaba, rabonta da abinci tun na safe data an caccakala, sannan ta rage wanda ta rage ta na e shi ta aje sai kuma da safe hannunta ta shiga toilet ta wanke. Sannan ta auro sabuwar alwala ta dawo ta kwanta akan lallausan gadon da zatace kusan a irinsa ta kwana jiya, duk da bata samu tayi wani baccin arzi iba jiyan, dan tunani ne fal ranta. Sai kuma ta kasa baccin, sbd wata sabuwar kewar gida da ta kamata, Allah ya sani tana kewarsu tun jiya, hannu ta kai ta kashe wuta amma kuma sai ta kasa kwanciya sbd wani tsoro daya kamata, dan haka ta kashe wasu ta bar wasu a kunne, tana tasbihi a ranta har bacci yayi gaba da ita. HANAM POV. Tashi tayi yau Arya baya jin da i dan haka saida ta kaishi asibi sannan taje wajen aiki, kuma a wajen aikin ne aka kawo musu kwangilar inkin atamfofi na wani biki da za'ayi a villa. Ita kuma ma'aikatanta basa inka atamfofi, wanda yake in ma baya gari,dan haka tana bu atar wanda zai inka mata atamfofin, da wannan tunanin ta dawo gida, yau ji tayi bazata iya zaman aki ba, ai itama gidan gidan ubanta ne, dan haka zata iya zama a ko ina taso. Dan haka bayan taje tayi wanka tayiwa Arya ma sai suka sau o parlon asa, bata sakawa Arya riga ba sai ta barshi daga shi sai diapers, ta fito da system inta dan akwai aikin da zatayi, ta zaunar da Arya a cikin baby floor seat insa, dan yanzu ya fara wayo ga ta'adi a cikinsa. Ta tafi kitchen taje ta zubo abinci sannan ta dawo ta zauna kusa dashi a asan, ta ora laptop dinta akan coffee table, farar shinkaface da Stew wadda taji naman sa, sai coslow, data tashi sai take bashi shinkafar da coslow in kawai, dan tana so ya fara cin abinci tun yanzu, dan ya kusa shekara, kuma a yanda ta yanke yana cika shekara zata yayeshi. Tana ci tana bashi tana masa wasa har suka cinye tas, sai ta kira aya daga cikin masu aikinsu tazo ta kwashe plates in, sannan ta cireshi daga cikin floor seat in, ta koma kan kujera tana dudduba aikin nata. Arya ya kama kujera ya mi e ya fara rirri e kujerar yana tafiya. um um kace sai munyi tafiya zamuyi magana Ta fa i tana masa dariya, ya juyo ya kalleta shima yana dariyar, sai kuma ya saki kujera ya koma rarrafe a tsakiyar parlon, duk inda yayi tana binsa da kallo. Nabila ar Mero ce ta sau o, babbar mara kunya cikin an mero, ta sau o tana wani taunar chewing gum, sai wani kallon tara saura kwata take bin Hanam da shi. Arya ya kai wajen da aka aje wasu kaya a leda Hanam bata lura dashi ba ya shiga janyo ledar daga ashin kujera. kai !!, du**n uwarka zakayi da ledar da kake janyowa? ura masa ashar in tana finciko shi daga gaban kayan, tsawar da tai masa yasa Aryaan fasa kuka, 'dan ya tsorata, ta wancakalar dashi a gefe har ya kusa fa uwa, duk abinda take Hanam na binta da kallo, sai kuma tazo ta tsaya a gaban Hanam tana wani girgiza irin ta tashen balagar nan. Ki jawa shegen anki kunne, babu ruwansa da kayan mu a cikin gidan nan A hankali Hanam ta kai hannu ta aje system in a gefen inda take zaune, ta mi e tsaye kuma ba tayi wata-wata ba ta auke Nabila da maruka har uku warara. Naga kamar ranar da nayiwa uwarki da yayanki warning akan ana ba kyanan, to kema ga naki warning in, a da kunyi min rashin kunya na jure, kun zageni na jure, but now baku isa ba, kuma har yanzu idan rashin mutuncin ku akaina zai tsaya bazan ce muku komai ba, but if you dare touch my son, hmmm hmmm Tayi wani irin murmushi, tuni matan gidan suka fito sbd kukan da Nabila ta saka, Mero ta kamota tana fa Kede Hanam wallahi baki da mutunci, ki tab'a uwa ki tab'a anta, wannan ai wula anci ne, dama ai barewa baza tayi gudu anta yayi rarrafe ba, haka uwarki ma take Hanam ta ba banza ajiyarsu, ta kamo anta ta shiga bashi mama, sannan taci gaba da aikinta. Bayan abba ya dawo Mero ta sameshi da orafi akan Haman kamar kullum, shima sai ya bata ha uri kamar kullum in, sannan kuma ya ira Hanam in ya yi mata nasiha, bayan ya gama ne tace Abba an kawo mana kwangila na inka atamfa daga villah, to kasan musa ya tafi garinsu, su kuma sauran ba iya inka atamfa sukayi ba, shine nake so ka duba min wanda ya iya inki Abba yayi shiru yana nazari Akwai amma ki bari sai nayi magana dashi gobe duk yanda mukayi zaki ji To Abba Allah ya kaimu Abba ya shiga yiwa Arya dake kan cinyarsa wasa, Hanam ta tsaya kawai tana kallonsu, wani abu na yawata a walwarta. Duk duniya bata da wani farin ciki bayan wannan abu biyun, sune rayuwarta, domin su take farin ciki, bata da komai bata da kowa sai su, a da tana addu'ar Allah ya ara bata wani sabon fata, sai kuma ta samu Arya a lokacin, sai ta auki Arya a matsayin wannan sabon fata. *ALARO CITY* *Da misalin arfe 09:00am* Dogayen yatsun hannun Tafida suka wasa kofar akin da maryam ke ciki, yau lahadi amma dole yaje aiki, sbd kwanakin da yayi baije ba, duk da yana bu atar ya huta, dan jiya bai samu yayi wani baccin arzi i ba. Dan yana aje mata kayan nan suka fita shida drivern nan, ya aike shi yaje ya siyo musu abinci, daga nan kuma ya wuce masallacin block insu, kuma bai dawo gidan ba sai bayan isha, dan ya tsaya sunyi magana da ma ocinsa wanda shima ya kasance bahaushe an arewa. A lokacin daya dawo gidan har drivern ya dawo ya karb'i aiken da ya masa ya ware wanda zai bata sannan ya nufi ofar akinta. Kuma tun kafin ya wasa ofar yaji bugun zuciyarta, yana buga ofar bugun zuciyar ta ya sauya, wani irin sauti dayafi na ainahin yanda zuciyar tata take bugawa da in saurare, idan zuciyarta tana bugawa a tsorace sautin yafi da in saurare. Ya Rab!! Shine abinda ya furta a lokacin, sai kuma yayi sauri ya aje mata ledar cikin wani irin sauri daya zarce na normal an adam ya shige akinsa. Bai samu yayi bacci da wuri ba sbd bugun zuciyar tata dayaci gaba da saurare. Kuma yau da safe daya fita masallaci yaga wutar akinta a kunne, alamun ta tashi, bayan ya dawo kuma bai fito ba sai yanzu, shine yake san ya sanar mata da zaije aiki.......... _Kamar kullum jama'a, ina mi o godiya sin i-sin i, sannan gaisuwa ta musamman zuwa ga mrs Zak's, naga sa onki, Maryam tana zuba ido _Ayi dropping comments dan Allah_ _And pls share it -SAI KASKA CE- YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Arewabooks @18saikaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *BABI NA GOMA SHA HU U (14)* *Babin mu na yau kuma naki ne, Badi'a Ahmad Sulaiman* .........Tunaninsa ya katse a sanda Maryam ta bu ofar, abu na farko daya fara shiga ofofin kunnuwansa shine wannan bugun zuciyar, kuma a tsorace yake bugawa, kenan tsoransa take, tana tsoransa a matsayinsa na haka ina ga idan tasan waye shi, ainahin shi. Sai kuma ya kalleta, hijabi ne a jikinta har asa, hannunta da fuskarta ne kawai a bayyane, idonta ya kalla, wani abu dayafi komai kyau a fuskarta. Maryam na ha a ido dashi ta sunkuyar da kai, dan bata tab'a sanin haka kalar idonsa take blue ba sai yau, cikin tsoro da rawar murya ta sunkuya asa tace Ina kwana Lafiya Ya amsa mata cikin muryarsa me zurfi, kuma sautin muryar tasa kamar akwai gajiyab a ciki, Maryam ta mi e kuma har yanzu kanta a asa zuciyarta na tsere a irjinta. Shi kuma ya kasa kunnensa sai sauraren bugun zuciyarta yake, koda wu a za'a ora masa a wuya a tambayeshi me yake ji a bugun zuciyar tata bazai iya fa ar komai ba, dan baisan me yasa yake san sauraren sautin ba. Kawai de yana jin kamar akwai wani abu a cikin sautin bugun zuciyar tata na musanman, kamar yanda fuskarta take very Innocent hakama zuciyar tata ke bugawa, musamman ma idan tana bugawa da sauri. Zanje aiki ne, shine nace bari na fa a miki, akwai kitchen a asa, zaki iya shiga ki girka abinda zaki ci, ko idan na fita na aiko miki ? Ya bata zab'i biyu ne dan be san me ya kamata yayi a cikin biyun ba, idan yace sai ya fita ne lokaci zai ure, kuma bai sani ba ko bata makara wajen cin abinci, idan kuma yace ta girka wata ila bata iya girkin ba, dan haka ya yambayeta. Kamar Maryam zata ce masa ta rage abincin jiya kuma shi zata ci sai kawai ta fasa tace. A'a zan girki Muryarta ta fito da irin innocent dinta, a hankali ya gyada mata kai. Sai na dawo Allah ya tsare, Allah ya kiyaye hanya Maryam ta fa i bayan ya juya, maganar tasa Tafida an dakatawa da tafiyar da yake, addu'ar ta dakeshi sosai. A hankali yaci gaba da tafiya cikin takunsa na izza da asaita, tausayin yarinyar na ara kama zuciyarsa. Maryam tabi bayansa da kallo, tana kare masa kallon da bata samu damar masa ba jiya, bata san cewa dogo bane sai yanzu data tsaya a gabansa, kuma wani abu data lura dashi shine yana da rukon al'ada, dan daga jiya har yau duka kayan hausawa take ga yana sakawa, amma ita a ganinta sai take ga kamar kayan basu wani karb'e shi ba, da a ce zai saka kayan indiyawa sai yafi karb'arsa, dan gaba aya kamar indawace dashi. akinta ta koma ta cire hijabin jikinta dan dama sbd ya kwankwasa kofar
Chapter 18 · 0% Book details