← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 84

Sashe 19

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne yasa ta saka, wajen data saka wayarta a chargy ta koma ta cire wayar. yar ta samu ta lalubo lambar Anti Fati, dan wayar bata dannuwa da kyau, alamun taci sensor, gaisawa sukayi sannan ta tambayeta ya su maanmu suke, Anti Fati ta ara mata nasiha, sannan sukayi sallama ta nemo lambar Badar za ta kirata amma sai aka sannar da ita bata da isasshen kati. Tayi tsaki sannan ta aje wayar mi ewa tayi ta ara saka hijabin data cire sannan ta fita daga akin, ta tsaya a ofar akin tana kallon corridor in dakunan, daga karshen corridorn daga dama kuma balcony ne, wanda yake facin kofar gidan. A hankali take takawa zuwa wurin, balcony in yanada fa i sosai, ga wasu flower vase da aka jera daga asa, ga grass carpet shimfi e a kasan wurin, ga kuma wani lilo a wajen, sai wasu flower vase din rataye a sama. Daga jikin bangoma wasu ne jere kala-kala, karfen balcony in an masa ado da neon strip light, hakama wasu daga cikin flower vase in, Maryam har ta hango yanda wajen zeyi kyau da daddare idan aka kumma neon strip light in, daga an sama kuma kejin aku ne kuma akwai akun a ciki. Maryam taji wani abu na farinciki na ratsa mata zuciya, sai kuma ta kalli sauran gidajen dake tsallaken nasu da ma na kusa da su, ko wani gini iri aya ne hatta da fenti, view in kasan akwai ban sha'awa. Ta koma wajen akun nan, tana kallonta, can tace. Barka Akun ma ta maimaita. Barka Dariyar farin ciki ta sub'uce daga bakin Maryam, gaba aya wajen ya gama burgeta. Fita tayi daga wurin ta ci gaba da tafiya a corridor in, bata bu e dakin da taga ya shiga jiya ba, dan bisa ga dukkan alamu nasa ne, sai ta bud'e na kusa dashi, shi ma kamar nata yake, amma kuma babu gado sai katifa kawai, kuma komai na dakin an lillibe da kyalle alamun ba'a amfani dashi, ta jawo ofar ta rife. Amma kuma sai taji tana san taga ya nasa akin yake, dan haka ta koma da baya ta bud'e kofar Kawai ta iya furtawa da tayi arba da akin, tsarin akin kamar nata yake amma kuma yafi nata girma, a hankali afafunta sukaci gaba da takawa zuwa cikin akin, tana ta santin kyan akin a zuciyarta. Ta kalli inda yake aje cricket kit bag dinsa, ga Jersey dinsa rataye a saman jakar, a ranta tace ashe an wasan cricket ne, dubanta yakai kan wani bango a akin wanda yake cike taf da hotuna, kafafunta sukayo kwana zuwa jikin bangon, ta tsaya tana bin hotunan da kallo aya bayan aya, duka hotunansa ne, tun na yarinta har zuwa girmansa. Idonta ya tsaya akan wani hoto guda aya, kuma wanda yafi kowani hoto girma a cikinsu, wani ba in fatane an africa sanye cikin suit irin tasu ta lokacin, sai kuma wata ba'indiya fara tas da ita, sanye cikin sari hannun ta ri e da wani yaro da ba zai wuce 3 yrs ba. Abu aya ne ya fa o a tunaninta, tabbas wannan iyayensa ne, kenan babarsa ce ba indiya ?, ga zahiri kinga tunda kamarsu aya da matar, wani sashi na zuciyarta ya amsa mata, Fulani ta fa a mata cewa iyayensa sun rasu. Sai kawai tayi musu addu'ar Allah gafarta musu, taci gaba da bin hotunan tana kalla, tun yana arami suke hoto da wata budurwa itama kuma ba'indiyace, kode kanwarsa ce ?, to amma kuma ai bashi da anwa a wannan hoton, wata ila yar uwarsace, dan suna kama hatta da kalar idonta irin nasa ne, amma ita nata idon ba light blue bane, nata dark blue ne, kuma duk da kasancewarta mace yafi ta kyau. Ya samu gata sosai, ta fa i a zuciyarta, sakamakon hotunansa da take gani na celebrating birthdays dinsa. Saida ta gama masa tsurku akan hotunan nasa sannan ta bar akin, ta sau asa. Kamar jiya, yauma ta tsaya tana ta kallon tsaruwar parlon, ofar farko da idonta ya sau a a kai ta fara shiga. Sai taga store ne na a jiyar kayan amfanin gida, akwai irin su wheelbarrow, watering can, spade (shebur), hose (tiyo din ruwa), vacuum cleaner, pruner (abun yankan ciyawa), spenner, hammer, broom inma wata doguwa ce, bucket, dustpan, squeegee mop(mofar goge glass), mop (mofa), scrubbing brush da dai sauransu. Wasu abubuwan ma bata sansu ba, kuma komai a killace yake, akan kantoci, daga arshen akin kuma washing machine ne har guda biyu, wata chest drawer ta gani a gefen washing machine in, ta bud'eta sai taga laundry detergent, bleach, pegs ( clips in shanya ), ta mayar da rufe, sannan ta fita daga wurin. Sai kuma ta shiga ayar ofar shi kuma bashi da girma dan guga kawai ake a ciki, daga ironing board sai wasu lokoki, ta shiga ta bubbu e lokokin, wasu kayane a ciki ba'a goge ba, wasu kuma an goge amma ba'a auke ba, sai wasu iron guda biyu babba da arami. Ta fito daga akin ta bu ayar ofar dake a tsalleken dakunan, shi kuma data bu e gym ne kawai, katangu biyu da suka zagaye wajen gaba ayansu auke suke da mirror, batama shiga ba taja ofar, dan a ganinta babu abinda za tayi a wani gym. ar wata kwana dake bayan ofar gym in tayi, taja ta tsaya baki bu e tana kallon danning table in dake wurin, danning in ya burgeta fiye da misali. ofar dake kusa da wajen tayi sbd ko tantama ba tayi ofar kitchen ce, abinda take aukin gani kenan a gidan, kusan sumewa Maryam tayi, bayan tayi arba da kitchen A rayuwarta tana san kyakyawan kitchen, wasu lokutan kawai sai ta tafi gidan Anti Fati sbd kitchen in gidan, yau sai gashi idonta na gane mata kitchen in daya ninka na gidan Anti Fati girma da kyau, kuma wai na gidan mutumin da ake kira da mijinta ne, wani abu yazo ya tsaya mata a zuciya na murna, taji kamar tana yawo a gajimari, ita da ganin kitchen irin wannan sai a film, ko a social media. kalar cabinet din kitchen din ash ne, ga wani kitchen island wanda aka kewaye shi da kujeru guda hudu, biyu daga kowani b'angare, wani abu da ya auki zuciyar Maryam ya jefa a cikin ruwan sanyi shine. Daga tsakiyar cabinet in sama da na asa wanda yake setin inda gas cooker take glass ne a wurin,a bayan wajen kuma garden din gidan ne, ga wasu flower vase da aka jera akan wajen, ga haske a cikin kitchen in ta ko ina, kuma daga asan cabinet in sama akwai wasu led strip light dake haska kan cabinet asan. Maryam ta rasa ina zata saka kanta dan murna, a hankali afafunta da babu takalmi suka shiga taka tiles in kitchen in, babu inda zuciyarta ke raya mata ta fara zuwa sai wurin glass in nan. Ta kai hannu ta zuge glass din zuwa gefe, dadda ar iskar da bishiyoyin garden in ke bayarwa ce ta silalo zuwa cikin kitchen in, a hankali ta lumshe idonta, sannan ta bu e, sai kuma tabi vase in dake laye a wajen, green leafy vegetables ne dangin mint, coriander, rapini da dai sauransu, Maryam ta maida dogon glass in ta rufe. Sai kuma ta dawo ta shiga bud'e cabinet in, gaba aya dangin kayan aikin girki babu wanda bata gani ba, spoon, fork, knife , pot har set biyu kuma duka non stick ne, juicer, tray, tongs, bottle opener, blender, ladle, pestel and morter, choping board, plastic containers dama wadan da bata taba gani ba. idonta sai yallin murna ya ke, ga ba aya kayan sau awa mutum wajen aikin girki akwai a kitchen in, tun daga toaster, coffee maker, oven har guda biyu, mixer, deep fryer, dish washer, microwave oven, hand blender hatta da dishwasher akwai. Maryam kamar ta taka rawa dan da i, sbd wasu kayan ma ba'a ko bu e su a ledar su ba, sabbabi dal, hakan ya nuna mata cewar ba sosai yake girki a kitchen in ba, ta bu e fridge ta ganshi cike da fruits da veggies, ga kayan miya ga kuma drinks amma komai a hargitse yake a ciki ga wasu kayan rober, shi kuma tasa kalar azantar kenan ?. Wata ofa ta gani a kusa da fridge in ta bu ofar ta shiga taga store ne, kuma akwai kayan abinci amma ba da yawa ba, ta shiga cikin store in ta shiga dudduba kayan ko zata ga abinda zata iya ci. Aiko tayi kyakyawan gani, wata rice stick wadda tun sanda ta ganta a wani recipe na tiktok ta shiga santin taliyar, yau sai gata ga taliyar, a da kullum bata da zance saina idan tayi aure zata ce mijinta kullum ya dinga siyo mata ita, sosai taliyar ta tafi da ita, sbd a ido idan ka ganta kafin a dafata sai kace zarene ba taliya ba. Maryam ta kai hannu tana auko taliyar yayinda idonta ke cika da kwallar murna, sai kuma ta tuno gida, nan take murmushin fuskarta ya auke, ko me suka dafa yau ?, ko waye yayi musu girki ?. Sai kuma ta tuno makarantar ta, yanzu shikenan babu ita ba makaranta ?, Lalle rayuwarta ta sauya sosai a cikin anin lokaci, ta samu abubuwa da dama kuma ta rasa abubuwa da dama. A hankali wata walla ta sulalo mata, ta daure ta share, sannan ta dawo cikin Kitchen in, ta shiga arin dafa taliyar rice stick Saida ta ha a komai sannan ranta ya raya mata me zai hana ta duba garden in ma, sai ta rage wutar gas Sannan ta bu ayar ofar kitchen in wadda take da tabbacin garden in zata kaita. am, ta ame tana kallon yanda wajen ya bala'in tsaruwa, shuke shuke ne fal wajen, ga wani water falls wanda aka kewaye shi da stones. Maryam taji kamar ta nitse a gun dan da i, wajen ya ha u, ya ha u karshen ha uwa, wata rumfa dake tsakiyar wurin ta shiga, wadda ke auke da kujeru da kuma table a tsakiya, kamar de balcony in saman nan, shima nan wajen akwai wannaan neon strip light in, an
Chapter 19 · 0% Book details