← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 84

Sashe 41

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jawabi. Kamar de yanda na sanarwa da kowanmen ku, mun ha a wanna zamane domin mu samu wani abinyi a wannan watan, kullum muna cikin aiki, bamu da abinyi sai shi, ba kuma ma hutawa sai weekend, wani lokacin ma a weekend in bama hutawa, dan haka yau muka shirya wannan fita dan musamu mu mi afa mu kuma ara sanin juna Yayi jawabin ne a cikin harshen turanci, Dr.Abubakar ne ya yiwa waiter magana, waitern ne ya kawo abinci kala-kala da suka yi oder aka zube musu shi akan dogon teburin dake aje a gabansu. Maryam ce tsaye a jikin balcony in dake wajen cin abincin, dadda ar iskar dake busowa daga tekun dake tsallaken balcony in take sha a, tana kallon yanda ruwan ke kai komo, ga fitilun wajen da suka fara haske sbd uratowar magariba, ga mutane na wucewa akai-akai. Ko a mafarki bata tab'a zaton rayuwarta zata sauya kamar haka ba, bata tab'a zaton zata wayi gari ta tsinci kanta a cikin irin wannan rayuwar ba, iskar wajen dake ka awa ce ke tuno mata da rayuwarta ta baya da kuma waddama take ciki a yanzu. Maryamu Daaso! Ta juya a hankali ta kalleshi, duk da tasan shi in ne, domin koda a bacci za'a tasheta ta ji muryar sa zata gane muryar tasa, shi in ne tsaye a bayanta, hannunsa sanye cikin aljihun chinos trouser in dake jikinsa, ga wani dan gajeren murmushi dake playing akan lebensa. Kamar wani jarumin film in india wanda director in yasa shi yayi irin tsaiwar, itama an guntun murmushin tai masa tana juyawa taci gaba da kallon tekun, sakamakon takowa da yake zuwa gareta. Bakyajin sanyi ? Muryarsa me cike da kamewa da aji ta tambaya, yayinda ya arasa kusa da ita ya tsaya, shima yana kallon wajen. Babu sanyi, view in akwai kyau Kansa ya gyada mata a hankali, kuma ba tare da ya kalleta ba. Ko inama a lagos yana da kyau wifey, akwai wajaje masu kyau sosai, ki bari wata rana zamu zaga gari Tayi murmushi me sauti tana sau e kanta asa sannan ta ago. Muje magariba ta kusa Ta gya a masa kai a hankali, sannan suka juya a tare. UCHENNA POV. Ya matarka take ? Muryar mahaifiyar sa ta tambaya daga cikin wayarsa, ya yi murmushi yana shafa sumar kansa me karfi irin ta sauran Africans. Yana zaunene a balcony ofar entrance in gidansa. Matarsa?, abunma ya bashi dariya, matar da babu wani abu na kusanci irin na mata da miji da ya shiga tsakaninsa da ita, ba wata hira suke ta arziki ba, maganarsu biyuce a rana, daga gaisuwa sai sannu da zuwa, sai kuma yanzu da ta fara girki idan ta gama zabtace masa yazo ya auki nasa, bai san me yasa take haka ba, amma ya san cewa Hanam bata sansa, kuma baisan dalili ba. Tana lafiya Ka gaidamin da ita Inshallah zataji Daga haka wayar tasu ta are, mi ewa ya yi ya koma cikin gidan, yanzuma bata parlo, sam yau be ji motsinta ba, sau aya ya ji kukan Arya a akinta. Rashin ganin nata ya arsa masa shakku a zuciyarsa, Hanam ba irin wannan matan bane, tana bawa aikinta muhimanci, koda wasa bata fashin zuwa wajen aiki, sai de idan wani uzurine me arfi ya taso mata, duk yanda akayi ba lafiya ba. Shawara ya yanke akan zaije ya duba yaga ko lafiya, akin nata ya nufa, saida ya isa ofar akin, ya ora hannunsa akan handle in, sai kuma ya samu kansa da kasa bu ofar. Tunda tazo gidan bai tab'a shiga akinta ba, tun ranar da aka sauya kayan gidan bai ara shiga ba. Sai da ya furzar da wani numfashi sannan ya mur a handle in, ya tura ofar gaba tare da bugawar zuciyarsa, dan baisan me zai tarar ba, akin ya shiga arewa kallo. Baiga kowa a ciki ba sai Arya dake zaune akan gado yana wasa da teddy, aran zubar ruwan da yaji a ban aki yasa ya fahimci cewa tana ban akin. arasawa ya yi jikin gadon, ya kai hannu ya auki Arya dake aga masa hannu alamun ya daukeshi, zuwa yanzu ya fara iwa amma kuma shi baya masa, wasu lokutan har idan ya karb'eshi baya yarda ya koma wajen Hanam. Shi kansa aunarsa da yaron na bashi mamaki, wasa ya shiga masa yana fa Yau ina kashiga ban gan ka ba ?..... aran bu ofar ban akince ta dakatar da maganar tasa, ya juya idonsa zuwa ga ofar bandakin, ya kalleta. Sai da zuciyarsa ta dungura fiye da irgensa a lokacin da ya ora idonsa akanta, wata pleated maxi dress ce me gajeren hannu jikinta, gashin kanta nanna e cikin bun, wanda ta ora claw clips a samanta. Ba shigar jikintace ta haddasa dungurawar zuciyarsa ba, abinda yake gani a fuskarta shine ya haddasa masa bugawar zuciya sau biyu a lokaci guda. Wani irin yanayi ne auke a fuskar tata, irin yanayin da yake gani a fuskar mom insa a duk lokacin da babansa ya daketa, irin yanayin da yake gani a fuskar mahaifiyar tasa idan bata da lafiya. Idanuwanta sun fa a ciki, kuma sunyi ja, haka kuma yanayin fuskar tata a raunane yake, fuskar tata fayau. Kallonsa take kamar yanda shima yake kallon nata, a hankali ta fara takowa zuwa wajen da yake. Tun safe ta tashi da zazzab'i, yau ta aura niyyar samun Abba akan batun Uche, dan tun rannan baya gari, ya yi tafiya. Jiya ya kirata yake fa a mata ya dawo dan haka zata iya zuwa ta ganshi, kuma tace masa zata zo ta ganshi yau, sai kuma Allah beyi ba, ta tashi da zazzab'in. Ta saba a duk lokacin da take jinya babu me damuwa da halin da take ciki sai Abba, idan kuma baya gari ko baya gidan saide taci ciwonta ita ka ai ta cinye, ta saba da hakan tun ba yau ba, dan haka a nan in ma da babu wanda ya le ota bata damu ba duk da tasan Uche in yana gidan, kuma ba ta yi mamakin ganinsa a akinta ba. Arya ya aje akan gado yana ci gaba da kallonta, ta araso har gabansa ta tsaya tana kallonsa da idanunwanta dake nuna cewar bata da lafiya arara. A hankali ya yi ya i da abinda yake ji a zuciyarsa yace. Baki da lafiya ne ? Muryar tasa ta fito cike da kulawa, kulawa irin wadda bata samunta daga wajen kowa sai Abba, Abbanta ne kawai ke mata magana cikin irin wannan kulawar, idanuwanta ta an juya ka an, sannan tace. Zazzab'ine kawai Kansa ya girgiza mata a hankali yanaci gaba da kallonta, a hankali ya ago da hannun sa ya yi abinda daga ita harshi ba su yi zato ba, shi da kansa da ya yi abun saida ya bashi mamaki. Da hannun nasa ya tashi sau a, bai sau a a ko ina ba sai akan goshinta, Hanam ta ri e numfashinta da yar, wanda ke shirin zarcewa ma ogwaranta, sbd wani abu daya ratsa tun daga hannunsa har zuwa fatar kanta, wani abu kamar shock in wutar lantarki. Abinda ya fa i bayan hakan shine ya ara saka zuciyarta kokwanto a kansa. Subhannallh, jikin akwai zafi sosai Anya kuwa taji da kyau ?, kamar subhannal taji yace ?, Anya kuwa ba a baibai take kallon Uchenna ba ?, shin da gaske shi Cristian ne kokuwa ?. ______________ _Helloo!, Hanam na tambaya, someone should answer her please_ _Game da ESHAM(ESHAAN DA MARYAM). Bani da ta cewa_ -SAI KASKA CE YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Arewabooks @18saikaska Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *Gareki na sadaukar da wannan babin Maman Ihsan* *BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI (27)* *Cogrove Estate,st 3, house NO 334* Malaria ce kawai, amma babu wata damuwa ki tabbatar kinsha wa anan magungunan, in Allah ya yarda zaki ji sau Muryar Dr. Hasina likitan asibitin Cosgrove estate ke korowa Uche da Hanam wannan bayani, bayan Uchenna ya yi amfani da wayar kiran emergency ya kira can asibitin sun turo musu ita. Hanam dake kwance akan gado rabin jikinta lillib'e da bargo ta gya a mata kai. Bani takardar sai inje na siyo mata Muryar Uchenna dake tsaye daga baya ta fasi cikin irin wannan kulawar ta azu, ri e yake da Arya a hannunsa yana kallonsu, Dr. Hasina ta juyo tana masa murmushi. Kada ka damu Uche zan siyo sai na aiko maka, ai kai kafi da haka Uche anyi murmushi, kirkinsa na saka a masa alfarma a lokauta da dama, dan Uchenna na kowa ne, kowa nasa ne, bashi da abokin fa a kona gaba, ga haba-haba da kowa, kuma kullum cikin barkwanci ya ke. A'a Dr. Ki bari de naje A'a ka zauna da matarka kawai, tana bu atar ka A hankali ya jinjina kai, Dr. ta gama ha a kayanta sannan tai musu sallama ta fita Bari naje na rakata ya fice hannunsa ri e da Aryaan, Hanam tabi bayansa da kallo tunanika iri-iri na yawo akanta, wai meke shirin faruwa ne ?, ya zama dole ta nemi Abba su tattauna. Jim ka an ya dawo, zama ya yi a kusa da ita cike da kulawa irin ta azu yace. Me zaki ci ? Kai ta girgiza masa a hankali tanaci gab a da kallonsa. No you need to eat, how will you take medicine without eating? Baki na nake ji da aci.... Ta amsa masa a hankali muryarta na fita cikin zafin zazzab'in dake jikinta. Duk da haka, ya kamata ace kinci Bata san musun, dan haka ta gya a masa kai, dan yawan maganar zai iya saka mata ciwon kai, ita dama can ba me yawan surutu bace, yanayin rayuwane ya sa ta zama me yawan magana. Baki da zani na goye shi?" Babu zani saide towel Kansa ya gya a mata sannan ya shiga bathroom ya auki towel in, bai fito ba saida goyon Arya. Hanam taji zuciyarta ta motsa, wani abu daga can asan zuciyar tata ya gangara zuwa asa, asa can inda bata san da shi ba. *Alaro city lekki, lagos, B3 house No. 122* *Da
Chapter 41 · 0% Book details