← Book details Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 84

Sashe 57

Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya isketa kwance a kan gado, gaba aya ta kashe wutar akin, da alamama bacci take, sai kawai ya aje mata abincin akan coffee table in dake akin, ya juya zai fita. Ina zaka je ? Ya tsinkayi muryarta cikin magagin bacci, hakan yasa ya tsaya da tafiyar da yake, ya juyo ya kalli kan gadon, akin babu isashen haske, sai na bed side lamp kawai, kuma shine ya temaka masa wajen ganin fuskarta. Abinci na kawo miki, ki tashi ki ci Tana daga kwancen ta girgiza masa kai sannan tace. No na ci abinci a gida Sai ya gya a mata kai ya juya zai fati. Ina zaka je ne ? Sai ya kuma tsayawa ya juyo ya kalleta, yanda daren nan ya yi kam ai tasan de ba shi da inda zaije da ya wuce dakinsa, zuwa ze yi ya kwanta. Kwanciya zanje na yi Sai yaga ta mi e zauna, tana murza ido. Kazo ka kwanta a nan Ta fa i tana nuna masa gefenta a kan gadon, kamar me tantance abinda take fa i, uchenna ya kalli kan gadon sannan ya kalleta. Gadon zai ishemu fa Dariya ta kusa sub'uce masa, ita ta auka cewar gani yake kamar gadon ya musu ka an, sai kawai ya jinjina mata kai, ya fara takowa zuwa jikin gadon, ta ayan b'arin ya za gaya, ya zana a bakin gadon yana cire crocs afarsa, sannan ya kwanta yana jan bargon ya bata baya. Yana jin yanda itama ta ja bargon, kafin yaji sau umin numfashinta a bayansa, sannan hannayenta suka zagaye cikinsa, sai kuma kanta ya sau a a gadon bayansa. Mu kwan lafiya, Harees Uchenna zaki ce Ya ji sanda ta aga kan ta daga jikinsa, alamun ta kalleshi, sannan ta mayar da kan nata, tana ara ma ale hannunta dake kan cikinsa. Harees yafi da No Uchenna ne yafi da Ya ji sanda ta kuma aga kanta sannan tace. Baka san sunayen musulmai ? Itama tanaga sanda ya girgiza kai, dan shi take kallo, sannan muryarsa ta fito a hankali cikin shirun daren. Ina so mana, kawai dai nafi san Uchenna, sbd uchennna yana nufin sarki, Harees kuma me gadi yake nufi, da sarki da me gadi wannene ya fi ? Yana jin sautin murmushinta, sannan muryarta ta biyo baya. Sarki kam yabfi A hankali Uchenna ya saka hannunsa akan na Hanam, sannan ya raba shi daga ri on da ta masa, hakan yasa itama ta aga kanta daga bayansa, sai kuma ya juya yana fuskantar ta, sannan ya saka hannayensa biyu, ya janyota jikinsa, kanta ya sau a a kan pillownsa, yayin da hannunsa na dama ya ankameta daga baya, hannunsa na hadu kuma yana kan ugunta ne. ya jata jikinsa sosai, ta yanda hatta da bugun zuciyarsa tana iya jiyowa, Zuciyarta ta shiga rawa, tana jin sak abinda take ji a duk sanda zata shiga jikinsa irin haka. Me ya sameki A kalance muryar sa ta fito, kuma ya tambaya ne ganin jikinta na rawa, kanta ta girgiza masa, alamun ba komai, daga haka shima bai ara cewa komai ba, ya rufe idon, sannan bacci ya yi gaba dashi. Hanam taci gaba da kallon kyakyawar fuskarsa, da taga itama hakan bazai kaita ba sai ta lumshe idonta ta ara gyara kwanciyar ta a cikin jikinsa. __________________ _Kai Allah sarki Baby Arya, My people shin akwai wanda ya taya Hanam kewar Arya?, ni de ina ta ya ta, ba Abba ba Arya_ _Nagode da goyon bayan ku_ -SAI KASKA CE YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Tiktok @SAI_KASKA Arewabooks @18saikaska Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *Wannan kuma naki ne Amina Ahmad Isah* *BABI NA TALATIN DA BAKWAI (37)* MARYAM POV. Sallayar da ta gama sallar asuba ta ninke, bayan ta idar da sallah tare da azkar inta na safiya, ta saka sallayar a cikin bed side drawer, yau sauri ta ke, dan haka bata da time in yin tilawa. Ta shiga bathroom ta yi brush sannan ta fita zuwa asa, store ta shiga ta auko kayan da take amfani dasu wajen tsaftace gidan. Sannan ta koma akinta, ban aiki ta fara wankewa, sannan ta share akin tas, ta goge ko ina,, balcony akin ta koma ta share shi shima, sannan 'yan flowers in nan nata ta yi musu bayi. Daga nan kuma ta dawo corridor, ta shiga balcony in corridorn, ta share shi, ta yiwa flowers in wajen bayi, ta bawa akun nan abincinta sannan ta kashe neon light strip in nan, tun da gari ya fara haske. Baya nan corridorn ta soma sharewa, har zuwa kan stairs sannan ta share falo, ta gareshi tsaf, ta fesa air freshener, Daga nan sai ta koma kitchen, ta aje kayan sharar da zummar sai ta gama girkinta za ta share. Store ta shiga inda ta zubo dankali a cikin wani aramin basket, sai noodles guda hu u data auko. Ta fito ta zubesu a kan island, ta shiga ha a breakfast, jallof in noodles in ta yi, wadda ta saka mata smoked fish, ta kuma awata ta da daffafen wai. Dankalin kuma ta dafa shi, sannan ta yayyanka shi ananu ta saka masa anyan wai da species, taruhu, albasa da kuma kayan amshi, sannan ta soya shi a masa pan, ya tashi kamar masa. Coconut and pineapple juice ha a, duka ta auko kayan da ta yi amfani dasu ta jeresu a cikin dishwasher kana ta kunnata. Kitchen in ta share, ta kuma goge ko ina, ta auki kayan sharar, Sannan ta fita zuwa akinta, bayan ta aje kayan sharar a store. Zuwa yanzu rana ta gama fitowa, kuma tana da tabbacin Fidar Yara ma ya dawo daga masallaci. TAFIDA POV. Yana zaune a akinsa, ya ji sautin takunta tana tako stairs, dan haka ya mi e ya bu ofar akin nasa, a dai-dai lokacin da ta shigo corridorn ta tsaya tana kallonsa kamar yanda shima yake kallonta. Wani ash in hijabi ne a jikinta wanda ya sau a har asa, be san me yasa ba amma har yanzu fuskarta akwai kumburi. Maryam ta arasa takowa tana ci gaba da kallonsa, Sanye yake da da wasu ba en jogger set, hannunsa na dama sanye cikin aljihun rigar hoodie in, hular hoodie in ta kwanta a bayansa, sumar kansa ta sau asa kamar kullum. Hannunsa da baya cikin aljihun ya kai ya tura sumar baya, amma saida ta dawo kan goshin nasa. Ina kwana! Bai amsata ba, shima ya tako har zuwa gabanta, sannan ya kai hannu ya zare hijabin dake jikinta, yana kallon raunin dake kanta. Maryam ta rintse idonta tana kawar da kanta gefe, Allah ya temaketa wata maxi dress ce a jikinta, yau da ta sha kunya, wai dan Allah me yake damunsa ne ?, itafa ya sauya mata gaba aya, sai kace ba Tafida ba, yanzu waye zai yarda idan tace wannan kyakyawan jiya ya yi kissing inta, ai sai dai ma a mata dariya. Tafida ya kalli gashin kanta, Ta masa parking cikin ponytail, jelar da da take me an tsayi tana reto a bayanta, ga wannan hair pin in sa ale a gefen kan nata, idonsa ya zamo kan raunin dake gefen kan nata, ya kai hannu ya ri e goshin ta ya jujjuya kan nata, sannan ya dawo ya duba na fuskarta. A sannan ne kuma Maryam ta tambayi abinda ta kwana da shi jiya a ranta. Sundar!, wacece Heleen ? Ta lura kamar ya ha iye wani abu, amma still be ce mata komai ba, sai da ya gama duba raunikan nata sannan da kansa ya mayar mata da hijabin. Sai a sannan ya amsa gaisuwar da ta masa azu. Lafiya, fatan kin tashi lafiya Itama sai bata ce komai ba, ta gya a masa kai kawai, ta rab'a shi zata wuce, ya ri o hannunta sannan ya dawo da ita gabansa yana kallonta. Heleen ? Bata ce masa komai ba, kanta sunkuye a asa. Wata yarinya ce da bata da kamun kai bare sanin darajar kai, karuwa ce, mazinaciya, yar shaye-shaye, me kisa haka kuma yar daba. Shekaru biyu da suka wuce, aka kawota asibitinmu, sun yi fa a da 'yan wata ungiyar daba, sun harbeta, kuma ni ne na karb'eta a time in, har aka sallameta ni ne nake kula da ita, Bata bar asibitin ba saida ta fa a min cewa tana sona, a lokacin sai kawai na bita da kallon bata da hankali, wata ila wayar da take afawa ta tab'a mata walwarta Sai ya yi shiru yana aga kansa sama, sannan ya tura sumar kansa baya, sai kuma ya sau e kan nasa, duka Maryam na tsaye a gabansa tana kallonsa, sai yaci gaba. Tun daga lokacin ta shiga bibiyata, kuma a duk sanda zata zo wajen da nake bana ko kallanta bare na mata magana, a haka har muka shafe shekaru biyu, ita bata gajiya da bibiyata, ni kuma bana fasa manna mata(Shariya). Sanda akayi auren mu bata gari, ta aiko a fa a min wai ta tafi abuja, bata dawo ba sai a satin nan, khabir shine ya fa a mata cewar na yi aure, shashancin dake cikin kanta ya fa a mata cewar tazo ta kasheki, tunda kin wace mata Tafida Yanzun ma shirun ya yi, ya ifta idon yana kamo hannun Maryam na dama. Bata sanni ba gaskiya, shekaru biyun da ta yi ta bibiyata a banza suke, tunda har bata san waye ni ba, Miriam idan har ina san abu, to rayuwatama zan iya sadaukarwa a kansa, in har ina numfashi koda inuwarsa bazan bari a rab'a ba, zan tsaya na bashi kariya duk wuya duk da i, idan har kuma wani ya samu damar cutar dashi..... Ya tsaya kallon Maryam na 'yan sakkanni, sannan ya murza hannunta, ya ora hannun na dama kan kuncinta, Maryam ta lumshe ido sannan ta bu e, tana zuba fararen idanuwanta a kansa. Bazan bar mutum ba, hakace ta kasance da Heleen, da ace ni ta cutar, ba lalle ne ma na kalleta ba, amma kuma sai ta cutar min dake, ke in da bana jin zan iya yafewa koda kaina ne ya cutar dake, koda nine
Chapter 57 · 0% Book details