Sashe 17
Yadda Ƙaddara Ta So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
me yasa rayuwa zata mata haka ?. Har jirginsu ya sau a a lagos Maryam nata sa e-sa e a ranta, shi kuma Tafida ya bada himma wajen sauraren bugun zuciyarta ne, shi abun har mamaki yake bashi, ya rasa me yake tsinta a bugun zuciyar tata. Drivernsa na asibitine yazo ya auke su zuwa ALARO CITY, Tunda Maryam tazo duniya gari uku ta ta6a zuwa bayan ha ejia, daga auyen su Abbansu sai kano sai kuma malam madori da ta tab'a raka Badar wani biki, amma kuma bayan su bata tab'a zuwa ko ina ba. Ita manyan gine-gine irin wanda take gani a yanzu sai a waya ko a tv, suma in dan ta kasance ma'abociyar kallon finafinan india ne, amma da bazata tab'a sanin akwai kalar wannan abinda take gani ba, kuma irin wa an nan inma tana ganinsu a tiktok, dan akwai wani a tiktok wanda yake posting kyawawan wurare a nigeria. Ta tuna yanda suke ta musu itada Badar akan wasu wajejen ba nigeria bace, amma kuma a yau, sai gata a gaban wa annan manya-manyan gininnikan. Da ace bata san abinda take ba, kuma bata da wayewa da ta zuba auyanci. Ta lekki link bridge suka wuce, ita batama san akwai ta a nigeria ba, tasan de akwai irinta a mumbai, kuma itama in a waya ko tv take kalla, wato inda ranka ka sha kallo, ta fa i hakan a ranta. Mamaki bai cinyetaba saida suka iso ALARO CITY, wani babban estate me kama da wani garin, a babban symbol in dake manne a saman wajen ta karanta sunan estate in, haka sukayi ta wuce blocks kala-kala, kuma ta lura da kowani block ginin gidajesu iri aya ne. Maryam taga kamar sun shiga wata duniya ne da ban ba earth ba, abun akwai ban mamaki ga wanda bai taba gani ba, gaba aya tsarin estate in irin ginin asar turai ne. Block 3, suka shiga, drivern yayi parking a kofar wani gida wanda yake shima gininsa iri aya ne da sauran gidanjen cikin block d'in, ta waya Tafida ya bu e musu gate in, drivern ya shiga cikin gidan, yayi parking suka fito, ya kalli Maryam. Ki shiga ciki Ya fa i cikin wannan muryar tasa me zurfi, da yar maryam ta gya a kai, sannan ta kama hanyar shiga cikin gidan, hannunta ri e da hand bag inta, hannunta na rawa ta kai ta bu e kofar gidan, bakinta da sallama ta shiga cikin gidan. Bazata iya cewa komai ba akan tsaruwar gidan, gidan ya ha u ta ko wani fanni, shida drivern ne suka shigo auke da jakukunansu, sannan taga sun haura sama, da hannu yayi mata alama da ta biyoshi, haka tabi bayansu har zuwa ofar aya daga cikin akunan dake saman, daga inda take tsaye a corridorn ta le asa ta kalli parlon, a ranta tana jinjina girman gidan, shida drivern ne suka fito daga akin da suka shiga sannan yace mata. As from today this will be your permanent room Her permanent room ?, kenan yana nufin zai zauna da ita har abada ko me ?, itafa ta kasa ganewa, amma sai ta gya a masa kai, asan taga shima yayi yabi bayan drivern yayinda ya bar jakarsa a wajen, batayi gigin tab'a masa ba. Tasa kai ta shiga akin, Allahu adirun ala man yasha'u, shine abinda Maryam ta ayyana a zuciyarta, bayan da tayi arba da akin, ba wani me girma bane can, amma kuma ya ninka akinta da take kwana na gidansu, gidansu ?, kalmar ta maimaita kanta a walwarta, yanzu ita aya zata kwana a wannan katafaren akin ?, ko a wani hali gidan nasu ke ciki ?. Sai kuma tabi akin da Kallo, komai na cikinsa ja ne da ba i, babu abinda yafi aukar hankalinta irin kofar balcony in, wadda ta kasance ta glass ce, hand bag dinta ta aje a kan gadon sannan ta taja a hankali zuwa balcony in ta kai hannu ta kawar da curtais in sannan ta zuge kofar glass in, ta taka zuwa balcony in, wata iriyar iska me cike da ni'ima ta bigi ofofin hancinta dama na fatarta, kyakyawan garden in gidan dake back yard yayi mata sallama, daga saman da take tana iya hango kyan garden in. Ga wata kujera me kamar lilo a balcony in, sai wasu flower vase masu kyau da aka jera a kasan wurin, wurin ya tafi da imaninta...... -SAI KASKA CE- YADDA ADDARA TA SO *Magical love story* By Sai Kaska Wattpad @Sai_Kaska Phone number:08130172702 Arewabooks @18saikaska _________________________________ *Proud of my first novel* TAURARI WRITER'S ASSOCIATION *BABI NA GOMA SHA UKU (13)* *Na sadaukar da wannan babin zuwa ga, mrs zak's* ......Tunawa da tayi batayi sallar magriba da ake ba yasa ta koma cikin akin da sauri, sai kuma ta shiga toilet, duk jikinta a gajiye take jinsa dan haka ta yanke cewar harda wanka zatayi. A yau ta godewa Allah, social media da novels da take karanatawa, dan badan suba ba zata iya tab'uka komai ba, a ranta ta tuno da cewar da ace wata daga area insu aka kawo wannan gidan, wai da anga auyanci, tayi murmushi a bayyane tana bu e kofar shower stall Wankan tayi sannan ta fito tayi alwala ta maida kayan da ta cire ta fito, jakarta data zo da ita ta bu e ta auki hijabi ta saka, taji wani da i na ratsata, dan tayi kewar hijabinta, abayar ma ta yarda ta saka ta ne sbd tanada fa Sallar ta gabatar, sannan kamar yanda ta saba ta zauna tayi addu'o'inta ta shafa, sai kuma ta mi e ta cire hijjabin ta ninke, jakarta ta kuma bi ewa ta auki wata sabuwar dark navy midi prom dress wadda Anti Fatice ta bata, rigar bata da nauyi kuma hannun rigarma ba wani dogo bane. Ta sakata sannan ta mi e ta shiga bubbu e lokokin data tarar a akin, bata samu komai a ciki ba, har ta bu e doguwar drawer in dake manne da wani bango, kuma wardrove in yar bangoce, amma kuma kamar closet dan sai kayi taki aya.... biyu.... Sannan zata tarar da inda zaka jera kaya a cikinta, nan inma babu komai. Goge lokar da tayi sbd ar kurar data gani a ciki, ta dawo kan akwatunanta ta shiga bu ewa, mamaki kawai take da ta'a jibin abinda take gani, gaba aya kayan atamfofine da lesuka kuma duka an inka. Wani abu daya ara bata mamaki shine data gwada su a jikinta duka daidai itane, daga tsayin har fa i, akwati hud'u na tsaddadun kayan sakawa ne inkakku sai abayas, sauran biyun kuma data bu aya daga cikinsu takalma ne da jakukuna a ciki, ita kuma ayar kayan kwalliyane harda jewelleries. Maryam ta rasa ma abunyi, data gaji da kallon kayan ta mi e ta shiga na ewa tana jerasu a wardrobe in, har ta gama jeresu kaf, takalma da jakukunan kuma gaba aya ta jeresu a lokokin kasa, wani aramin flat kawai ta bari a cikinsu wanda zata dinga sakawa na zaman gida, tana shiryasu tana mamakin kayan, ga shi kuma harda gyalulluka, kuma ita ba ma'abkciyar saka gyale bace, duk da gyalullukan na matan aure ne, dan suna da girma sosai, daga can gefe ta jere wanda tazo dasu, har ta gama shirya kayan wardrobe in bata cika ba, kuma batayi mamakin hakan ba, dan wardrobe in ta kusa cinye fa in bangon da take jiki. Gaban drassing mirror ta dawo wanda babu komai a kai, ta jere kayan kwalliyar sannan ta dawo ta zauna a bakin gadon ta auko hand bag din data zo da ita ta fito da qur'an in dake ciki ta saka shi a bed side drawer, ta auko wayarta da ear piece inta harda charger inta, sai kawai ta shiga jujjuya wayar a hannunta, gaba aya screen in wayar ya fashe daga sama, duk bata lura da hakan ba sai yau da safe. Wayar ta kunna taga babu chargy, gashi tana san iran Anti Fati ko Badar, dan a gidansu babu me waya, su Hussain dama basu da waya, dan dokace maanmu ta kafa musu akan bazasu tab'a ri e waya ba sai sun gama secondary. Kuma tun kan Anti Fati har zuwa kanta basu ri e wayar ba sai da sukayi candyn, jiki a sab'ule ta mi e ta saka wayar a chargy jikin wani socket dake kusa da bed side drawer, bata san lokaci ya ja ba saida taji ana kiran sallar isha, ta ri e alwalarta dan haka kawai ta mi e ta saka hijjabin data cire azu ta gabatar da sallar ishar sannan ta zauna tana addu'o'in ta. ofa taji an wasa dan haka tayi saurin shafa addu'ar ta mi e a hankali ta bu e kofar gabanta na wani irin bugu, sai de bataga kowa ba, har zata juya ciki idonta ya sau a a kan wasu ledoji guda biyu, ta tsugguna ta auka sannan ta meda ofar ta rufe. Tana ta mamaki, duk da tasan de babu me mata hakan sai shi, shi in da a yanzu yake amsa sunan mijinta, mijinta ?!!, sunan ya maimaita kansa a ranta, shekaran jiya take fa in cewa batada niyyar yin aure kwana kusa, amma cikin kwana aya komai ya sauya, rayuwarta ta juya up side down, tana kaikawo a kan sira in rayuwa. Ledar farko ta bu e, kuma tun kafin ta gama bu e take a way in dataga a ciki amshin wani abu da umin abin ciki ya daki hancinta da fatarta, wani gasashen cat fish ne da kuma fried potatoes tun kafin ta kai abincin bakinta yawunta ya tsinke, ta auko wata roba da itama take cikin ledar ita kuma tun kafin ta bu e taga abin ciki kasan cewar rober is transparent, wani ha in cake parfait ne a ciki, maryam ta aje shi shima gefe, ta bu ayar ledar kuma ita drinks ne a ciki. asan carpet ta dawo ta zauna ta baje kayan abincin, sannan ta shiga toilet ta wanko hannunta ta dawo ta zauna ta fara cin abincin, tabbas tasan ta iya girki, amma kuma bata saba cin irin wannan abincin ba idan har ba Badar ce ta kawo mata girki ba, ko kuma