← Book details Tsintacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 116

Sashe 106

Tsintacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Bayan an gama karantawa ne Bar Adnan yace "Ka tuna sanda kuka kirani? Akan in shiga jikin Akeem ko meke faruwa na faè“·a maku? Kafin nan nace ko faè“·a min dukkan abinda kuke shiryawa da kuma abinda kuka aikata? To anan kuka faè“·i kisan da akaiwa Baffana, sosai naji kaina ya sara na shiga tunani kamar nasan mai suna har ruwa sai da kuka bani nasha, kana nace ai rubutu akan kune kuka kashe sa babu sa hannuna koda wani abu ya faru,
Daman kuma kun fa蓷a min Papi wato Abdul-茩hadir Azeem bashi da masaniya na kisan, bayan kunyi rubutun kuka mance ducoment 蓷in ni kuma na 蓷auka, tun a lokacin na shiga tunani, ina kuma jin Akeem a jinin jikina da zuciyata, bana iya bacci ko matata ta tambaya ina ce mata babu komai tayi min addu'a, lokacin da idanuna ya sauka akan Abbu ranar 蓷an 茩aramin hauka nayi ga ciwon kai ga yawon ganin reflection na wasu 苼oyayyun fuskoki,
Ranar kowa da Amani ta fa蓷a ruwa na cirota ranar nasan waye ni, ranar memory na kai na ya dawo, a kuma lokacin na fahimci ba komai yasa nake ganin kamar nasan Meema ba sai fuskar Akeela dake kama dana Meema, kasantuwar fuskar Akeela na fara gani tun a lokacin naji ina son fuskar amma 茩addara ta rabani da fuskar, ina ganin Meema kuma duk soyayyar da nakewa Fuskar Akeela ta koma kanta, naci gaba da 蓳oyewa ne nima har lokacin da gsky zatai halinta, na girgiza sosai lokacin da naji labarin abinda Mami taiwa Akeela, har kuka nayi ta wahalar masu da Yarinyar duk tasan cewa jinin Abbu ce bata da tabbacin abinda Baba Rabi ta fa蓷a, ni kuma ina dangin Akeela sunyi min gata a lokacin dana rasa nawa, sun mai dani mutum babu cuta babu tsangwama sai zallar soyayya, son da suke min suka bani 拼arsu na aura, na kuma yadda cewa da 茒A da DUKIYA ba'a san me mura ba sai Ubangiji hakan ka蓷ai ya isa mai tunani yaji tsoron Allah, 蓷a a duk inda yake ba abin wula茩anta wa bane,
Babu wanda yasan wane zai zama gatansa 蓷an daya haifa ko kuma 蓷an wani, ko babu 茩addara ta zuwan Mutum sanadiyyar fya蓷e ko zina, akwai 茩addara ta mutuwa da zata rabaka da dukkan yaran daka haifa, wazai ri茩e su baka sani ba, ka ri茩e 蓷a da zuciya 蓷aya shine imani da kuma jin茩ai.
Nimcyluv tayi gsky da tace tsammaci abinda bakai tsammani ba, ba zan ta蓳a shu蓷ewa ba, ba tare dana shi mata albarka ba.
Da ace 蓷an daka haifa shine mutum da Oumuu Ayman bata ri茩e Julde ba, da ace 蓷ana kowa ne da Deen bai raini Moon har ya aureta ya kaita masarautar su ba.
Haka kuma da ance 蓷ana kowa ne da YA LEE bai 蓷auki NOOR daga cikin 茩abilan da ko addini bai je musu ba, ya kawota Barack 蓷in su ya ajjiyeta ba tare da sanin even his parents ba bare abokan aikinsa na sojoji su samu damar lalata mata rayuwa ba (SOJOJIN 茦ASATA). A madadin Mamina ina mai baku hqr akan kuskuren da tayi dan Allah ku yafe mata, ina mai jin kunya sosai 茩warai da gaske"
Shiru yay yana goge hawayen daya sakko masa, Mami kowa kuka take sosai Abbu farin ciki na bayyanar è“·an nasa yasa ya kasa cewa komai, sai yanzu kuma ya fahimci Meema zaman da tayi dashi tai masa mugun sabo yasa ta saka aka bawa Adnan irin fuskarsa.
Ajjiyar zuciya ya sauke yace "Bisa 茩wararan shaidu dana bayar ina ro茩an Wannan Court mai adalci data 蓷auki mataki akan wannan mugwayen mutanan,kuma ta wanke Dr Abdul-hakeem Bukar Bello akan zargin da ake masa my bro is Innocent, sauran baya nan shigar da farar da sukai yana cikin wannan recording 蓷in, domin ina zaune akai maganar komai" ya fa蓷a yana bada memory hannunsa al茩ali ya amsa.
Jama'a suka fara tsinewa su Tijjani domin tuni an fito da Alhj Atiku waje, nan aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya domin sun kashe Baffa kuma sun kashe jama'ar Wudil kusan guda biyar zuwa goma. "Section 221 of Penal Code ta yanke musu wannan hukuncin bisa tarin shaidun da aka bayyana" al茩ali ya buga guduma kana yace "Su kuma Wannan 拼an sandan da basu san aikinsu ba, sun gabatar da abu ba tare da bincike ba suka tafi da babban mutum a gaban ahlinsa suma Court ta yanke musu hukuncin gidan 蓷an kande na gyara halinka" farin ciki Sosai akai kuma aka wanke Akeem tare da cin tarar 蓳acin suna da sukai masa ku蓷in yace akai garin Wudil a bawa wanda aka lalatawa gonakin su..
A hankali Akeela ta mi茩e daga kusa da Meema tana tafe a hankali idanunta cike da hawaye kai tsaye wajan Akeem ya nufa da yake bawa wasu 拼an jarida hqr akan ba zai iya Shira dasu ba.
Tunda ya ganta ya gyara tsaiwarsa domin jama'ar da suke wajan rabin hankalinsu yana wajan Akeem è“·in.
Tana zuwa zata shige jikinsa yay saurin kama hannunta tare dayin waje da ita.
Murmushi kawai Dad yay yana jinjina soyayyar da yakewa Akeela, Aalam daman bai zo da 茩yar ya zauna ma zuwa bayan shari'ar domin hankalinsa yay gida.
Sosai Mami Akeela kuka har sai da tace "babu komai na yafe maki baki min komai ba"
Akeem na zuwa waje ya samu P.a shida Aleema a tsaye sai a lokacin ya kula da Karim da Ajmal, ganin zasu nufi wajansa yay saurin amsar key è“·in hannun P.a da sauri Ajmal yabi bayan Akeem shi kuma Karim ya tsaya da Afaf suna gaisawa.
Bayan ya sanya Akeela a mota yana 茩o茩arin juyawa Ajmal yace.
"Ba wani abu ya kawo ni wajanta ba, kawai i came to tell her something"
Hannu Akeem ya har蓷e yace "Uhm About?" Ajmal yace "her property, dukkan abinda Papi ya bari nayi bincike duk halak ne companyn da suke 茩o茩arin yine kawai haram kuma ban sa lissafi dashi ba, anyi rabon gado daman nazo mata da dukkan takardun filayen data mallaka guda 30, da kuma tsabar ku蓷i 250m" numfashi Akeem yaja baice komai ba,ya juya ya kalli Akeela da kanta ke 茩asa yace.
"Hubb come out"
A sanyaye ta fito tana jin duk wani iri a Zuciyarta ga kuma aman dake tasu mata.
Da 茩yar ta bu蓷e baki tace "Ina yini bro" Murmushi Yay mata yace "Lfy, ya jikin naki?" Tace "Allahamdulillah" Akeem kawai jinsu yake amma baya son tsaiwar da suke.
Gaba è“·aya takardun ya haè“·e a wani file ya bata,kana yace "kuè“·in kuma ki bada acct number a zuba maki"
Juyawa tayi suka ha蓷a ido da Akeem tana 蓷an langwa蓳ar da kanta gefe tace "Zauj" fuskarsa babu yabo ba fallasa ya 蓷aga mata gira alamar mene, wajansa ta 茩arasa ganin yadda take 茩o茩arin sanya idanunta cikin nasa yasa ya 茩ara yin 茩asa da idanunsa ji tayi duk babu da蓷i tace.
"Your details bank" a ta茩aice yace "ki bada na Momma" kamar zatai kuka tace.
"Na san da ita ai Zauj ka bani we'll talk later" banza yay mata ganin haka yasa Ajmal yace.
"Babu komai tsakani na da Akeela, koda rashin sani ne yanzu kada ka manta 茩anwata ce uba 蓷aya, kallon sister nake mata, abeg don punish her sbd ni" gently ya 蓷ago kansa ya kalli Ajmal kamar zai magana sai kuma ya fasa, yana maida Wayarsa aljihu yace "I'll send it to you later" yana fa蓷in hakan ya jata zuwa mota ya zaunar da ita,shi kuma ya shiga wajan driver yaja motar da gudu suka bar cikin Court 蓷in sai tsaki yake ja, yana hargitsa sumar kansa.
Gajiya tayi ta è“·ura hannunta akan nasa tace.
"Zauj me nai maka ne?"
Banza Yay mata tasan halinsa idan ransa ya 蓳aci baya iya Magana, amma duk da hakan sai da ta 茩ara shagwa蓳e fuska tace "dan Allah kayi hqr kaji Zauj my teacher told me cewa fushin miji hatsari ne ga matarsa kayi hqr Zauj"
Still Shiru yay mata sai kawai ta fashe da kuka tana 蓷ura kanta a cinyarsa da sauri yay parking jin kan motar na neman 茩wace masa.
Wani wawan numfashi yaja da 茩arfi tare da sanya hannunsa ya 蓷ago ta gaba 蓷aya zuwa jikinsa yana matseta a 茩irjinsa yana sauke numfashi.
"I'm sorry Zauj ban sakewa" ta fa蓷a tana 茩ara narke masa a hankali yake jan Numfashinsa yana sauke wa, har yaji zafin zuciyarsa ya dai-dai-ta, a hankali dai-dai kunnanta yace "Please Hubb kada ki barni kinji, ina Sonki da yawa ina tsanin kishin ki"girgiza masa kanta tayi tace "Kai ne duniya ta Zauj, kai ke farin ciki na, kaine kuma tubalin rayuwata, ba zan iya barinka ba, dan Allah ka daina nuna fushi akai na zuciyata babu da蓷i Zauj" vail 蓷in kanta ya zame ya shiga sha茩ar 茩amshin sumar kanta yana shafa bayanta kafin a hankali ya 蓷ago kanta ya manna bakinsa akan ya shiga kissing 蓷inta yana jan numfashi, wani kalar da蓷i Akeela keji wanda yasa gaba 蓷aya ta narke masa, ga 茩amshi turarensa dake kwantar mata da tashin zuciyarta, ganin yana neman ficewa hayyacinsa ya zame bakinsa da 茩yar tare dayi mata 茩uri da ido, itama shi take kallo cikin nutsuwa tace.
"I love You Zauj" Daman abinda yake jira kenan yace "I love you too Hubb Allah yay maki albarka ya bamu zuri'a na gari" tana shafa sajan fuskarsa tace "Ameen ya rabbi, Allah ya 茩ara maka arzi茩i,da kuma wadatar zuciya, ya tsare min kai daga sharrin shaidan sharrin mutum da aljan, ya baka halak ya raba ka da haramun Zauj" da蓷in da yaji yasa ya kasa magana sai kawai ya sumbaci goshinta tare da kwantar da ita a 茩irjinsa yace "Sleep" kwanciya tayi tana rungome sa tare da shafa fuskarsa zuwa gemunsa, a haka yaja motar yana sakin Murmushi kafin su 茩arasa gida har tayi baccin nata, wanda kuma ciki ne yake sata yawan bacci.
A ranar ma cikin dare yaje ya è“·auke matarsa, washe gari nayi jirgin su Aalam ya tashi bayan Azumi ko cikin Azumi kuma Akeem zaibi bayansu.
Ranar Akeem yay kewar iyayensa duk da ba wani sabawa yay dasu ba, Mami kuma ta koma gida ta fa蓷awa Dada duk yadda akai, har sakin da Abbu yay mata yanzu kuma babu abinda take 茩auna kamar mijinta.
Wata washe garin Abbu shima ya koma gida shida Didi dasu Aleema da Ummi, da Adnan wanda zaije ya fara gyara gidan da yayi domin kafin azumi Meema ta tare, shi kuma Akeem yana gidan Dad sai jikin Akeela ya 茩ara sau茩i zasu tafi.
Ranar da aka 蓷auki Azumin farko na watan Ramadan ranar Akeem da Akeela suka sauka a Kano, an gyara komai na gidan musamman part 蓷insa, dake cikin dare suka sauka sai kawai ya shige da Akeela zuwa part 蓷insa, lokacin da 茩ara fari da 茩iba duk da cikin dake cikinta yana mugun wahalar da ita.
Sai da akayi azumi goma Adnan ya è“·auko Meema zuwa gidanta dake gaban na Abbu gidan Akeem kuma a gaban na Adnan, suka fara soyayya hankali kwance lokacin cikinta ya fito.
Yau ne aka 蓷auki azumi na 29 tara wanda kuma shine na 茩arshe gaba 蓷aya Azumin kuma guda goma kawai Akeela tayi ansa mata ruwa yakai sau biyar cikin watan Ramadan, yau an samu ta nayi fitowa tayi daga kitchen tana sanye da abaya lokacin gab ake da kiran sallar magrib, kai tsaye kuma part 蓷in Akeem ta nufa sbd wayarta data manta tana shiga ana kiran sallar magrib 蓷in, gani tayi baya Parlo sai kawai ta shige ciki tana kiran "Zauj! Zauj" rungometa da akayi daga baya yasa ta juya shine sai zabga 茩amshi yake cikin wata tattausar jallabiya, kwa蓳e tayi tace.
"Uhm Allah ka sakeni" hancinta yaja yace "bance kada ki è“·auki azumi ba?" Shiru tayi masa sakinta kawai yay yace "Jira na dawo kada ki fita, akwai milk ki è“·auka kisha kada kuma kisha ruwa sosai" yana faè“·in hakan ya fita bayan yaci dabinon ajwa a bakinsa...
Bayan anyi sallah suka dawo gida tare da Adnan da Abbu Meema anan za tasha ruwa, coffee kawai yasha da kunun tsamiya mai da蓷i ya nufi part 蓷insa Ummi dai ko tambayarsa Akeela ba tayi ba, daman Baba Rabi tuni ta tafi 茩auyen su.
A kwance ya sameta tayi wanka tana è“·aure da towel è“·insa, tunda ya ganta yaji yanayinsa ya sauya, yana zuwa ya è“·auke ta cak zuwa kan bed tare da kashe wutar è“·akin, idanunta cike da bacci tace..
"Zauj me zakai?" Yana wura mata iska yace "kekam kwana nawa ban miki komai ba? Kullum kina wajan Ummi tana hanaki samun lada" idanunta na lumshewa tace "Ayyah Zauj ka barni kaji" yana zame mata towel 蓷in yace "ka蓷an zan" "uhm" tace kawai yau duk wani iri take jinta dauriya kawai take, tana jure abinda yake mata yana gamawa kuwa tace "Zauj" yana shafa kanta yace "Hubb" zamewa tayi a jikinsa tana ri茩e cikinsa tace "Zauj cikina" ta fa蓷a tana sakin kuka da sauri ya kunna hasken 蓷akin ganin jini Male male a 茩asanta yasa ya ru蓷e da sauri ya 蓷auke ta bayan ya zura mata jallabiya jikinsa duk rawa yake, yana fitowa Ummi tace "lafiya?" A gigice yace "Ummi jini take zubarwa" ya fa蓷i hakan yana waje da ita da sauri Adnan yabi bayansa, Didi kuwa kuka tasa, suna zuwa asibiti Akeem da kansa ya fara dubata kuka ya sanyawa Ummi yana fa蓷awa jikinta lokacin daya tabbatar cikin dake jikin Akeela ya fita yasan kuma Shine yaja, da 茩yar yay shiru akai mata wankin ciki 12 na dare suka dawo gida Ummi taci gaba da kula da ita Akeem kuma wani kukan ya 茩ara yana Rungome Amani dake wajansa yana son cikin Akeela sosai a haka bacci ya 蓷auke sa a kuma washe gari za'ai Sallah 茩arama...
Chapter 106 · 0% Book details