← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 94

Sashe 93

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana bukatar taimakonta ko dan kunosa da maman malan da ta yi *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 7 Nd Nd Nd Nd Nd Nd *Alhamdilah* Ba karamar jajircewa Abdul ya yi dan gannin iyalansa sun hada kansu, yakan hada su ya sake a cikinsu ya yi ta jan su da hira da wasa da dariya Idan sun kadaice daga su sai shi yakan yi nasiha da nuna irin yanda yake son su hade kan nan nasu Sam baya nuna wata ta fi wata tsakanin su, Yana bakin kokarinsa dan kamanta adalci tsakanin su, baya baiwa wata fuskar kawo maganar wata idan ba alkhairi zata fada ba, shi baya daukan sirrin wata ya fadawa wata, baya yaba wata gaban yar uwarta dan ya bata mata rai Ba laifi ya samu abinda yake so , domin a cikin watani hudu da suka karu ya yi tafia sau uku kan harkar shagunan da zai bude a maradi, kowace tafia yakan saka ido sosai dan gannin shin daya zata nemi daya? Abin farin ciki shine ba.a wuni dare ya yi daya bata leka yar uwarta sun gaisa ba, duda ba wani hira can can ba ko wani sakin jiki irin wannan , aman haduwa a yi zumunci suna yi, idan kuma daya ba lafia dayar na tsayawa kamar yana nan ba wani abinda zai ragu Sukan dan zagaya a tsakar gidan tun da docter ya bada umarnin zagayawar Sosai Hafsar ke samun kulawa bangaren mijinta, iyayenta, mahaifin mijinta da abokiyar zamanta A haka har watan haihuwarta ya tsaya inda Abdul ya murje ido kan ba inda zai motsa, sam ba zai je ko.ina ba yana tare da ita , harma ya baiwa saudiya amsar zai je bincike aman da sharadin idan matarsa ta haihu zasu je tare Wani yamacin juma.a, Hafsat na gidan malan ta je gaishe su du kuwa da irin nauyin da ta yi, Abdul ne ya kaita da kansa ya ce bayan salar magariba zai zo ya dauketa dan ta shiga yan uwanta ko zata warware dan kuwa kwanakin nan haka kurum ta cika fushi, abin fushi da ba na fushin ba tanzu zata fashe da kuka ta samu da kyar ta mike ta barawa mutun waje, an ce da shi idan cikin mace ya tsufa takan fitar da sirfa kala kala Zaune take zugum tun da ya ajiyeta wajen karfe goma na safe Ciwo take ji na fitar hankali bayanta cinyoyinta kai harta da idannuwanta bata so ta daga su da karfi dan ji take har su ciwon suke Mahaifiyarta na lure da rashin walwalarta, sai ta ringa kokarin gannin ta sakata walwalar domin cen dama maman Hafsat ba mai basu damar yawon kawo korafin gidansu bane bale har ta saurare su ta basu kofar shirme Ita dai Hafsat daga zaune ta kasa yiwa abin dariyar mamanta dariya, a haka har aka kawo abincin rana A lokacin da ta muzguta dan wanke hannunta ne ta ji wani irin bulbul ruwa mai yawan gaske ya zubo daga pant dinta daga zaunen da take Di kira ta yi ta sanar da ubangiji kafin ta kai dubanta wajen kafafuwanta inda ruwan gayannan har ya fara gudu Gabanta ne ya fadi, irin gargadin mamansu na tsafta ne ya fado mata inda take fadin ba ruwanta da iskancin matan zamani wai dan kina da ciki shikennan ke an tara kazamta a tare da ke, ki zubar da wannan ki ci ki bari ba ruwanki da wanki wanka ko wanke waje, ke ga mai ciki kina wari kina karni fuska ba kwali a yi magana a ce ciki to ba a kanki aka fara ba bare a gama a kanki, yau ta shiga uku fitsari ne ta yi zaune a dakin mama? Mama da tsantseni ba mai hanata cewa a gidanta ma haka take,gashi duka duka yanzu karfe uku ta yi bale ta sa ran Bawan Allah zai zo ya dauketa su yi tafiarsu, yau ta san mai rabata da mama sai Allah dan haka a hankali ta dago suka hada ido da mama da ta yi sokoko tana kallonta da yannayin mamaki da tsoro a fuskarta Da Sauri Hafsat ta daga dan yatsarta manuniya sama ta ce" mama, na rantse da girman Allah ban taba yin fitsari a jikina ba , komin dare sai na sauka na saka takalmina zan je bayi na yi na dawo, kuma ki tambaye shi, itama auntyn ki tambayeta, sannan shi wannan fitsarin ban ji ina jinsa ba ban san zai fito ba sai fitowarsa da na gani mama, wly shi kadai ke zuba Da sauri mama ta koma ta rufe dakinta ta karasa kusan Hafsat ta duka ta ce" maman malan kina jin ciwo wani waje ne? Tun yaushe kika fara jin ciwon? A asibiti sati nawa suka baki? Hafsat na kallonta ta ce" mama tun da watan nan ya kama nake fama da ciwon baya da cinyoyi sai na ji marata ta kara nauyi sannan ta sauki dumi, ban fadi ba dan kin hana ni yawan korafi Mama ta gyada kanta kafin ta kamata ta ce" mu je saman bed, cire zanin nan ya jike Hafsat ta cire tana mamakin mama batai mata fada ba, sai dai tana kokarin mikewa gaba dayanta ta ji wani irin ras ras ras wanda bashi da misali Da sauri ta so durkushewa mama ta riketa gam ta taimaka mata ta dorata saman bed dinta Nan da nan mama ta saka safar likitoci ta hannu ta gyara Hafsat da kamar jira ake ta motsa a gagabo mata ciwo ta dubata Tabas Hafsat nakuda take har nakudar ta kankama domin a 3 take hakan ya saka mama saurin kallon agogo ta dauki wayarta ta shiga neman layin Malan Malan dake tare da jama.a yau juma.a sam bai ji wayarsa na kuwa ba, a wajen kuwa Harda Abdul suna ta hira da jama.a wanda shi kuwa ya baro tashi wayar a cikin mota Gannin ta yi ta doka wayoyinsu ba.a dagawa sai ta nemi ta babar yarta wato Aunty ta doka kira Aunty dake kicin tana gyara abincin mijinta da bakinsa sam bata ji kira ba hakan ya saka natama har ya yi ya tsinke shiru a lokacin kuma har karfe gudu ta zarce sosai Da sauri mama ta ahiga safa da marwa tana kallon Hafsat wace idan ciwon ya lafa sai ta dafe goshinta saman hannunta tana sauke ajiyar zuciya Bata taba fita ba da izinin mijinta ba koda halin rashin lafia ne, bata san yaya zata yi ita dai likitar mata ce mai karbar haihiwa aman ba zata so Hafsat ta haihu a gida ba hakan ya sa ta dauki hijab dinta ta fita tsakar gidan tana bin dakunan samarin gidan ko zata samu wanda zai taimaka ya kira mata malan Da kyar ta samu ta aiki salihu bayan ta fada masa a gagauce ne Tsaye ta tana yarde zufa, ta kasa komawa dan tsoro, haka kuma ta kasa fita ta tarbo malan din da kanta Ya kai minti arba.in tana safa da marwa sai ga malan da Abdul sun shigo a tare domin gannin irin misscal din da mama ta yi sai hankalinsu ya tashi Da sauri ta tarbe shi, bayan ta yi masa sannu a gagauce ta ce" UMMA ce ke kan gwuiwa Da sauri malan ya ce" Me? Kuma kuke gida baku je asibiti ba ? Abdallah da ya kwararo ido ai bai san lokacin da ya shige kai tsaye ya nufi dakin mama ba Yana zuwa ya tura kansa ya shiga Muryarta ya jiyo a hankali tana fadin" ALLAHUMA LA SAHLA, ILAMA JA.ALTAHU SAHLA, WA ANTA TAJ.ANUL HAZNA IZA SHI.ITA SAHLA Da sauri ya karasa ya tsuguna inda take kwonce kanta na kallon sama Hannayenta ya kama cikin nasa hakan ya sakata rintse ido ta damki hannun nasa da wani irin karfi kafin ta saki wani mugun nishin da ya saka mama afkowa da gudun tsiya ta karasa shiga cikin dakin Gaba daya jikinsa da nata rawa suke, wani irin hawaye ke taruwa a idannuwansa yana gogewa yana kallon yanda take jijiga sannan adu.a a bakinta ta kasa dainawa A haka maman malan ta haifo danta, dan jaririnta wanda yana saukowa a hannun kakarsa ya calara kukan da ya saka malan kaiwa kasa a nan kofar dakin yana tazbihi ga ubangiji Abdallah kuwa muryarsa sama sama yake fadin" Alhamdulilah Mama na gyara yaron ta dora mata shi kan cikinta bayan ta janye farar rigar dake jikinta mai girman gaske sannan ta zagine ta cire kunya ta shiga kiciniyar gyarata haihuwa mai gayar dati gashi yau an mata ita a kan gadonta Gannin ya ki fita ya saka mama ce masa" yawa ka je daga waje na kimtsata Kallon mama ya yi, kai da ba dan ita bace gaskiya da ba inda zashi, haka ya dauki yaron yana ta kallo ya nade a zannin mama mai kyau sabo fill abinsa ya fice waje Yana fitowa malan ya mike a zabure yana kallon yaron, sai kawai ya ji hawaye ya zubo masa, a fili ya ce" ya Allah, ka baiwa mamana ladan nakuda da haihuwa, ya Allah ka baiwa mamana lafiar shayarwa da ladan shayarwa, Allah kar ba baiwa wannan yaro damar saka mamana hawaye, ka shiryar mata zuriyarta , ya Allah kar ka jarabi mamana da yaya masu rashin ji, domin ni na yafe mata duniya da kiyama hakama mamanta, Allah ka ja da kwanakin mamana su zauna lafia da
Chapter 93 · 0% Book details