← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 94

Sashe 57

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dake jiran gannin amsarsa na ya rama da fada fada ta ji shiru sai abin ya dameta, Tunani ta yi kan yanzu fa ba aiki take masa ba, mutun ya nuna damuwarsa a kanka bai dace ka yi masa abinda zai iya taba ransa A hankali ta rubuta message kamar haka" *Yaya jikin ka?* Mikewa ya yi zaune yana murmushi mai sauti, sannan ya bata amsa da" bani da lafia ne? Hafsat ta yi shiru da wayar a hannunta, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta rubuta" *malan meye wai? Zakana wani neman bani wahala ka manta da maman malan kake magana?* Wannan karron har sai da ya buda hakoransa wajen murmushi, a fili ya ce" come on, relache toi, i really miss yannayinki, Na.ima dake kallonsa ce ta yi motsi irin wanda zai saka shi gane ta farka A hankali ya kai dubansa kanta, bata sanye da riga sai gajeran wando baki mai santsi Yan berayan mamanta ya kalla haka kawai lokaci daya siffar Hafsat ta fado a ransa Wani irin mikewa ya yi tsaye ya rintse ido lokaci daya, a hankali ya yi baya baya ya jingijar da bayansa jikin garun wajen, Sai da ya jima a jaka kafij ya buda idannuwansa ya ga dai kuri shi take kallo Takowa ya yi inda take ya tsaya mata kerere yana kallonta ya ce" ki daina zamarmin ba riga dan Allah, idan nemanki na yi ina gamawa ki saka rigarki....hakan zai sama min kwonciyar hankali Yana gama fada ya juya ya nufi bayi , Da kallo ta raka shi tana mamaki halayarsa, Mikewa ta yi ta shiga saka rigar a kasan zuciyarta kuwa ayyanawa take cewa.... ban san yaushe zan fahimceka ba, tanzun kuma wane zan yi? Nan ka ce da ni na ringa zama ba kaya, nicema nake saka wandon nan dan ba zan iya zama haka ba, kuma yanzu kaine da cewa na ringa saka kaya hankalinka zai fi kwonciya? Tana gama sakawa wayarsa ta dauko ta ajiye masa gefen gado ta yi tsuru tana kallon wayar, da wa yake magana? Da wa yake nishadi har haka? Wacece ita? Wata dabara, wani irin kyau, ko wani irin iya girki ta iya wanda ya saka shi sakewa da ita har haka? Gabanta ne ta ji ya fadin mata lokaci daya, ta sani ba tun yau ba ko ba dade ko ba jima Abdul sai ya kara aure dan kuwa a da can ma ta san da ba mijin mace daya bane bare a yanzu da yake jajan wai dama haka take da son jiki? Tsoro ne ta ji ya rufe mata zuciya lokaci daya, in dai wannan da yake magana da ita budurwarsa ce kuma aurenta zai yi ai kuwa da zaune bata sameta ba, tabas da ta hadu da tsayuwa kennan, dan tana tunanin auren so kennan, ganninsa ma zai iya yi mata wahala Tana cikin tunanin ta ji ya janyota baya, wato saman bed din, gaba dayanta ta tafi jikinsa a hankali ya saka hannunsa cikin rigarta sannan ya ja hannunta ya kai wani sashe na jikinsa daban wanda ya sakata jin gabanta ya kwonci kwonci ya fadi, aman da yake yanzu ta gama daukarwa kanta niyar gwada juriyar sai ta rintse ido ta shiga bashi hadin kai du da irin tarin tsoron kasancewarsu abu daya, Hafsat dake jiran amsa shiru shiru haushi ne ya isheta, cike da jin haushi ta ajiye wayar kasa ba saman bed dinta ba dan kuwa an hanata ajiye waya kusa da kai dan babu kyau yana hadasa rashin lafia Kwonciya ta yi saman hannunta na dama bayan ta gama adu.ar baci ta yi shiru tana kallon waje daya Wani uban tsaki ta ja ta mike ta zauna saman gadon tana kallon waje daya A fili ta saki wata yar karamar dariya kafin ta tafa hannayenta, hannun nata ta dago ta zunguri kanta a fili ta ce" Hafsat baki da mutunci, ke da zaki yi baci kina mai yabon ma.aiki aa sai kawai ki je duniyar baci kina hangen rayuwarki ta Bodyguard? Rayuwar ta hatsari? Wace har harbi akai maki a can? Wajen da kika hadu da dan rainin hankalin nan wato Abdul? Kanta ta girgiza ta ce" to ki yiwa kanki fada, ki yi aurenki ki tafi abinki, ki je ki yiwa BS biyaya, ..... A daren nan ta jima tana kokowa kafin baci ya dauketa , hakan ya sa da asuba sai da mama ta shigo dakinta da kanta ta tasheta tana yi mata fadan cika dare dan kar ta fara makara a sallah kuma! Ranar Lahadi da yama wajen karfe biyar Hafsat ta gama shirinta tsaf cikin sabin suturunta sannan sabin shiga a wajenta wanda ta mayar shigarta na yanzu wato Abaya Ta yane kanta, fuskarta ta gyarata daidai misali ba abinda ta saka mai yawa ko mai daukan hankali sosai aman a banza dan kuwa irin yanda hankali ke kaiwa kanta abin ba.a cewa komai Ta jima duke dakin malan tana shafa fatiyar adu.ar tsarin da yake ta binta da ita, shi kam dan an fito masa da cewa haka zata yi ta zama a gida sannan aka daure shi cewa ai Allah ke tsarewa da shi aka bi, da ba zai taba yarda ta fita ba sai dai idan za.a kaita dakin mijinta Sai da ya gama sannan ya dauki kudi jika biyu ya bata tare da cewa ta shiga taxi idan ta gaji Mama dake tsaye murmushi kawai take zubawa, a ranta kuwa fadi take wai a nan malan gani yake yana mugun kokari na boye soyayar yar tasa, yanzu ba fita bane zata yi? Ta tabata ta siyarwa kanta jaje kennan, idan kuwa maman malan ta yarda ta kai magariba to fa tabas zata ga malan a bayanta ya je nemanta Sai da ta rakata har tsakar gida, kiri.kiri mai dakin tsakiya ta yi dariya a bayane sannan ta ce" wani lamarin sai a gidan mu, yaro ya je bariki ya dawo a ci gaba da ririta shi ana kara tura shi wani barikin Ikon Allah ko kallonta Hafsat bata yi ba bale ta nuna ta ji me ta ce ko ta tankata, wannan abin shi ke kara basu haushi dan irin ta tanka mutun din nan irin na da a yi ta masifa har yayansu su kai mata duka su ce ta yiwa masu rashin kunya basa samu, du inda ta je din nan ya kware su dan magana ba irin wada basa yaba mata aman sai ta zama tamkar dutse ta ki motsi ta ki nuna ta ji bare har a yi fitinar da zata fitar da malan ! A haka basa tunanin zasu ci galaba a burin sakawa uban ya tsaneta harma ya koreta, wau shi malan karfin imani da daukan kadara ko? Yarinya ta je yawon ta zubar ta dawo masa aman ba wanda ya ji inda ya yi mata fada da daga murya ma bale a yi tunanin duka da kora, aa sau nasiha da nuna soyaya! Tsaki ta ja masu mai karfi sannan ta ja gefe ta tsaya tana kallonsu tana son jin me za.a cewa Hafsat Mama ta kali Hafsar fuska a hade ta ce" *ANMIH,* ki tabata magariba ta yi maki a gida in sha Allah, Allah ya tsare ki da dukan sharin abin shari, Allah ya kare ki ya shirye ki A hankali Hafsat ta amsata da amen Mamana, sannan ta juya ta sa kai ta fice tana dariya cikin ranta, sarai ta gane nufin matar babanta so take ta tankata a dawo kada mata rashin mutuncin, bata san Kutkale da horon zama Bodyguard ya horeta zama kurma sannan makauniya gaban du wani abinda ta yi niya, sai ta yi niya zata tanka koma menene, idan ta ki ba zata tanka komai ba walahi! A hankali take tafia da pos fara kal a hannunta har ta isa bakin titi Tana tsayar da taxi ta fada masa Butik din da zai kaita sannan ta shiga gidan gaba ta daura belt ya ja suka kama hanya Kanta ta sada dan irin yanda fuska da yawa ke binta da kallo irin kugun kallon nan mai sakawa a fadi, Ta san kallonta suke dan su gane wai ita ce ko ba ita ba? A haka mai taxin ya tsaya ta cire kudinsa ta bashi ya bata canji a cikin kudin da Malan ya bata Sai da ta daga kanta ta karanta tankamemen rubutun dake jikin Boutik din kafin ta zagaya a hankali ta je hanyar shigar Matar dake tsaye da abin caje mutun ce ta cajeta sannan ta shiga Sai da ta yi tafia mai dan tsayi kafin ta tura madubin wajen ta shige Zuwa ta yi wajen accenseur ta shiga domin inda zara yi siyayar dole shi zai kaita ki ta yi ta hawan matatakala har sai ta hau hawa tara! Tana fitowa a nitse ta taka ta je wajen da ake siyar da liptom din, lipton din malan kennan, wanda yake anfani da shi Gidan Lipton din kansa abin kallo ne, kwaya daya ne ta siyo aka saka mata a jakar Butik din, sannan ta fita ta nufi ainafin aiken da akai mata wato siyen shada gizner ta babar sallar dake karasowa tata da kuma ta yayarta wace yayar tata ce da kanta ta kawo mata kudin kan ta je ta siyo masu ta kai masu wajen mai dinkinta Tana shiga wajen mai tsaron wajen wani bature ne jajajir da shi da gilas dinsa na karin ganni yana zaune da jaridarsa a hannunsa yana karantawa da ganninsa saurayi ne mai jinni a jika hutu ya kwonta masa Wajen shadojin ta je tana dubawa cikin nutsuwa ba tare fa ta yi kwaramniya ko ta tsaya a cito mata ba Tun fa ta shigo yake kallonta, dan da yawa wasun idan suka shigo sai su wani zarto wajensa su shiga tambayarsa inda zasu je su dauko abinda suka zo nema bayan ga komai a ajiye idan ka zo zaka kala ne a katon screnn din kana dudubawa har ka samu wace ta yi maka sai ka nuna a ciro maka ka biya kudin ka juya abinka aman sai an yi ta basu wahala Mai ruwan maroon mai manyan zane ta tafi da ita, dan haka sai kawai ta danna daidai ita
Chapter 57 · 0% Book details