← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 94

Sashe 35

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya yi toh zai shiga wani hali ne na takura da rashin lafia, shi kuwa yaki ya yi aure, shi ke gudun matan, dan kuwa matansa biyu bai san inda suke ba, iyayensu kansu sun tabatar masa da suna son saki aman kuma basu fadi dalili da kuma inda suke ba, zamani na daurewa yaya, zamani na soyayar yaya, bai ga laifinsu ba, ya yi masu uzuri ne, rayuwace.... Sai da ya gama abinda zai yi ya mike ya dauki hula ya dorawa kansa ya fito ya nufi motarsa, Direba ke jansa ya dauki hanya, Doguwar tafia ce sosai suka yi kafin su karaso inda take, Suna zuwa ya sauka ya shiga ya samu waje ya zauna yana sauraronta bayan ya gaisheta, Cikin sanyin murya ya ce" aa, bana so, na yi me da Bodyguard bayan wa.inda ke bibiye da ni a nan gasu nan har mutun biyar dake karkashina dan kare lafiata? Me yasa kike tsoro har haka ne Ummi? Ki daina , ki cire tunanin wani na jikina ke kashe min mata, lokacinsu ne ya yi, Kanta ta dafe, gardama ce yake mata aman cikib sanyin murya tamkar mai fadin maganar dadi, sai da ya yi shiru ta ce" ban yarda da su ba, mutanen da ka dauka a haka shanshakai? Mutanen da kake biyansu dan kudin da ba zai yiwu su sadaukar da yaruwarsu dan taka ba? Mutanen da ana iya siyansu ta hanyar basu kudin da ya fi yawa su ilata ka? Wai kai baka gannin hankali ya fara juyowa kanka dalilin kudadan dake bankina da sunnanka? Ba niger ba, ba nigeria ba, har saudiya kudinka dake cikin banki sai da ya saka prince Muhamad ya nemeka kuka gaisa? Bakinsa ya tabe ya ce" Ummih, Kudi, Kudi, Kudi, Ummi ba kowa kuddi ya rufewa ido ba, eh ana kisa dalilin kudi, ana abubuwa dalilin kudi, aman ummi dukanama nawa nake? Ban tafasa bama bale na kone, ba zai yiwu da kananun shekaruna 31 na zauna du inda na saka kafata wani gardi ko wata gardiya na tsaye kaina wai kareni, adu.o.in da nake basu isa su kareni ba? Ummih, ina da sirri, inada rayuwa tawa, ina yawo kasashe, ni ba zan zauna da gardi yana tsarona ba sai kace wani soko, haka kuma ba zan wani zauna sarkacecen kato da ni mace ta yi gadina ba sai kace dan daudu, Tsura masa ido kawai ta yi, ta san an rina, muryarta ta sanyayar ta ce" aman ka san doguwar tafiar da na yi dan samo wannan solution din? Ka san yanda nake gagara rintsa ido du lokacin da ka fita da sunnan wai kai ka tafi nema? Ka nemo me? Ka samo me? Du wanda ka tara ko jikokin jikokinka ne zasu yi wadaka daidai da zamaninsu, aman sai kace wani kogima na son kari, kuma du abinda dibansa ake kawai ba.a kara masa watarana zai zama babu, Shiru ta yi kafin ta kara tausasa murya tamkar itace yar (kun san mutanenmu na yanzu da shegen son yaya bale yan gayu) ta ci gaba da fadin" kai daya na malaka gidan duniya, yayarka ta mutu, mahaifinka an kashe min, ya hankalina zai kwonta idan na ga kana rayuwar garari? ABDUL a cikin mota zaku je diner, ka fita amsa waya ka dawo ka tarar da gawar mace tamkar tana barci, Tafia ta biyu washe garin aurenka ta tashi da ciwon ciki, itama ta tafi, Ta uku a cikin gidana, na tarar da gawar yarinyar da an daura aurenku muna saka ran zuwanka cikin satin , ni na mata wanka, da idona na ga shaidar jan jan abu wajen wuyanta na kamar an shaketa da wani abu mai kauri ne, Mata biyu sun gudu ba tare sa kun yi zaman auren ba domin sun tsinci labarin komai! Abdul, duka matan nan ba wace ka yi ainahin rayuwar aure da ita, kowace hakan baya tabatuwa ake katse lamarin, har yanzu shekara 31 baka san aure ba, ka yi aure har biyar, why ba zan damu ba? Danme ba zan kawo abubuwa a raina ba? Da idonka muka kalli vidon da jirgin da mahaifinka ya watse ciki, yana zaune kamar an lika shi ne a saman kujerar, da ido yake magana sannan yanda ya zaro ido kamar yana kallon wani ne ya tsare shi, kamar an sakawa mahaifinfa glue ne an dafke shi, har vidion ya dauke, Abdul, ka yarda ka ji? Ka amsani Fuskarsa ya shagwabe, daga inda yake zaune ya tashi ya karasa kusa da ita ya zauna ya kara yin takwaf takwaf da fuska ya ce" Ummih, ki yi hakuri, ba zan iya yawo da kowa ba, ni rayuwar yanci nake so, bana son rayuwar shiga hanci da kudundune, ki bar magnar nan kin ji? Da kallo ta bishi a kasan zuciyarta tana fadin" zaka sauko ne, sai ka yarda in sha Allah, zan yi ta lalabaka (toh fa wollah da oo ne, cewa kawai za.a yo kai maza an daukar maka bodyguard, zai amsa da to mama, ba maganar ehyane Gidan horo Sannu a hankali ta gama fahimtar eh lale wannan aiki da aka kawota aka hadata da mutane aiki ne mai mahinmanci, mai girma, mai hatsari, wanda cikin su su goma sha biyar dan an karo wasu, duka duka mutun hudu ake so, idan har bata ci wannan Jarabawa ba, to fa zata koma rayuwar KuTkale ne , rayuwar da abinda ya fi damunta a cikinta irin yanda ko adinninta yake da rauni, sannan ake harin mutuncinta! Hakan ya sa ta tatara hankalinta, ta maida baki daya hankalinta kan wannan aiki, Bata ji , kuma bata gani, Abu mai mutunci a wajenta a wurin nan shi ne! Suna yin excercise kala kala kamar : Gudu, gymnastic, karin koyon espanol, larabci, inglish, hausa, wanda shi ke ajiye su class, iya tafia, iya magana cikin sanyi da kyakyawan yannayi, iya saka kaya, kare rayuwar abokin aiki fiye da taka, iya girki, kai du wani abu na rayuwa ana koya masu cikin kwarewa da hikima, A haka suka dauki wata uku, wanda zuwa lokacin su bakwai kawai suka rage, Sai ya zama wata irin rayuwa ta ba mutunci, ba tausayawa dan uwa, uwa uba harin rai, somin kuwa a bakwai din nan ba wace ke so a cireta, gogagu ne, fitatu ne, a haka aka fara sama masu mission dan kara tabatar da hazakarsu, mission din da idan sun fita ana biye da dukan wani motsinsu, A haka wata mata ba za.a kirata datijuwa ba, ba kuma za.a kirata da yarinya ba, ta dauki Hafsat a matsayin wace zata bata kariya na tsayin wata biyar sakamakon wata shari.a da ta dauka, domin lauya ce mai zaman kanta, kuma gagarumar yar kasuwa ce, hakama gidansu an tara, tana aikin lauyanci ne dan ya kasance passion dinta, Matar bata da aure, aman kuma yayanta biyu wa.inda ta yi adopted, Tana zaune da su a gida guda inda su kansu sun girma sun zama baban saurayi da budurwa sosai, sannan suna karatu ne a kasar, A lokacin da aka gama bata labarin irin aikin fa zata yi, aka bata damar yin tambaya, ta jima tana rubuta dalilin aikin nata sannan ta dago da kanta ta ce" wace irin shari.a ce ta zata gabatar? Da wa da wa shari.ar ta hada? Sai an fada maki sirin shari.ar ko me? Da kike son sannin sirrin shari.at bisa wani dalili? Hannayenta ta hade waje guda , dogon wando sakake ne jikinta sai riga mai hannaye daidai gwuiwar hannu, sai hula irin ta mazan nan wace ta yar kofar bayanta ta fitar da gashinta dake daure da dan karamin ribom, ba wani abin kwaliya a fuskarta ko dis, aman wani sirririn sirin kyau ne a tatare da ita, ita kanta idan ta mike din zaka yi mamakin wannan yar abar har zara iya kare lafiar wani? Aman kuma mu je zuwa dai, Cikin nutsuwa ta fitar da harshenta ta lashi lebenta na kasa, sannan ta fitar da hakoranta na sama ta dantse leben nata, Sai da ta yi wal wal da idannuwanta sannan ta ce" wannan bai shafeka ba! Da mamaki yake dubanta, shi ne bai shafa ba? Shi zata rainawa wayo? Karamar yarinya dan tana ganninsa a bagas? Dan tana tunanin zama Bodyguard din fake kila wa kala shine har zata fara maida masa magana haka gatsal? A me ta dauki kanta? Bayan ga mutanen da suka fitar da ita suna jiranta su daga? Muryarsa ya daga ya ce" ni zaki maidawa magana a haka tamkar wani sa.anki ko wani class dinki? Ko yau kika fara aiki baki isa ki kamo ni a dukiya ba sai kin yi aikin shekara ashirin na rayuwarki! Shi ne zaki kalleni ki ce da ni ina ruwana? Kin manta ni ke hora ki? Datijon da ya daukota daga kutkale, wanda shi ne mai gidansu baki daya ne hankalinsa ya kawo wajen hayaniyar da SB yake yi, dan haka ya mike ya nufo wajen ba tare da ya yi ma masu jiran nasa magana ba, Nan matar ta mike itama da dan sauri ta bi bayansa, dan kuwa ba mai hana shiga a kofar, Cikin nutsuwa daga zaunen da take ta ce" aman ai na ga nan ba filin horo bane bare in bi du abinfa ka ce ko? Me ke faruwa? Ya jefo tambayar a dake, sannan fuskarsa ba alamar sasauci Gaba dayansu suka mike suka sara masa, Nan ya shiga kora masu bayannin abinda ya faru, Dubanta ya yi ya ce" baki dauki lesson din ladabi da biyaya bane na maida ke baya ko me? Kanta ta girgiza tana dubansa ta ce" GN, an yi mana lessin din ladabi da biyaya, kuma an yi mana ta mahinmancin lokaci da maida amsa wajen da aka yi tambaya da kuma kiyaye yin tambayoyin da basu da ma.ana! Ido suka zari su duka, sun gama sarewar shikenan ba za.a dauketa ba, tana zubawa wanda ya horata irin wannan fitsarar wa zai dauketa? Bayan wannan ai sai ta bata image din wajen, dan kuwa an sansu da bin na gaba da su ido rufe, Bai so haka ba, sam bai so haka ba, irin abubuwan da ya take ya kutsa ya tarba dan gannin ya cirota daga cikin gidan yari,
Chapter 35 · 0% Book details