← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 94

Sashe 92

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka karasa gidansu Yanzunma fitowa ya yi ya bude mata sannan ya kamo hannunta ta sauka daga motar Rufewa ya yi yana rike da hannunta ya nufi bangaren Na.ima da ita Ja ta yi da sauri ta tsaya tana kallonsa Juyowa ya yi shima yana mai jin dar dar dan bai san yanda zai iya tankwasa kansa gaban maman malan ba! Kallonta ya yi cikin ido ya ce" ya dai?? Hafsat ta kale shi da kyau sannan ta kalli inda zai kaita, a hankali ta ce" nan ba bangarena bane ba fa Abdul ya lumahe idannuwansa shima cikin nutsuwar ya ce" eh na sani, zamu je ne mu yi zumunci sannan kin ga bata san fitarmu ba Hafsat ta kara kallonsa da kyau kafin ta ce" aman ai sai ka fada mata ko? Sannan ai zamu hadu bangarenka ba sai mu yi zumuncin ba?? Tana maganar tana kokarin hadiye sauran ne sakamakon wani irin yanda fuskarsa ta fara hadewa tana hade kanta tamkar kashin safe Takead ya yiwa fuskarsa irin bai taba dariyar nan ba, Bai bata amsar maganarta ba ya kara jan hannunta suka je kofar fallon Na.ima Ja ya yi ya tsaya ya danna abinda zai shaida mata da bako bangarenta Na.ima dake zaune tana jiran lokacin zuwa bangarensa ya yi ta sha kwaliyarta daidai misali ta mike cike da mamakin waye ya zo gidanta a irin wannan lokacin? Yan aiki dai ba shiga wajensu suke a irin wannan lokacin ba, mijinta kuwa bai taba zuwa bangarenta ba bale ta kawo shi a tunanin ko shi ne A wannan yannayin mamakin ta je ta buda kofar Sai dai mamakin ganninsa tsaye ne ya kasheta Murmushin da bata shirya yi bane ya kubuce mata saman fuskarta ganninsa tsaye Sai dai gannin hannunsa rike da na mace a hankali murmushin nata ya ringa ragewa har ya bace fuskarta ta kasance babu yabo babu falasa a lokacin da ta ga wace ke tare da shi din Gannin ta yi bake bake a bakin kofar ya saka shi cikin yannayin laushi ya ce" hajia mun zo ziyara ne ko mu juya wannan tsare hanya haka? Na.ima ta kale shi da kyau, ta kuma kallon Hafsat Ja ta yi gefe wanda ba haka ya dace ta yi ba a matsayin wace aka zo gidanta Sai da suka shiga sannan ta bi bayansu jikinta du a mace tana jinsa yana waya da mai kula da harkar girkin gidan Zama suka yi su duka, ba wace ta gaishe da yar uwarta, shi kuma bai damu ba ya dai shiga jan kowace da hira cikin hikima yake sako daya cikin hirar daya a haka har aka gabatar masu da abinci suka ci a nan bangaren nata Sai da dare ya kara tsalawa Hafsat ta mike, Dan murmushin iya lebe ta sakar masu kafin ta ce" Allah ya tashe mu lafia Na.ima ta kalleta itama murmushin ta sakar mata ta amsa da " asuba ta gari Abdul ya mike ya kashewa na.ima ido ya ce" Ina zuwa Fita ya yi ya bi bayan Hafsat ya rakata har kofar dakinta Gannin zata shige bata ko kale shi ba ya saka shi riko hannunta da yannayin shagwaba irin ta maza ya ce" ko dan muah babu Madame?? Hafsat ta juyo da idannuwanta da sula cika da kwallah ta jin haushinsa ta sauke su a kan fuskarsa Haka kawai sai ta fashe da kuka ta janye hannunta ta shige bangarenta, Ita fa kawai ya wulakantata ta, dan me zai fara kaita bayan ita bata taba takowa inda take ba? Me take takama da shi da ita bata da shi? Kallon raini da wulakanci? Dan me zai wani kwasheta ya kaita bangaren macen da bata damu da ita ba? Abdul dake tsaye ya daburce sai dora hannunsa yake yana shafa kansa, Tamkar ya fada dakin ya duka ya bata hakuri, sai dai ina, hadewar kansu ya fi masa komai, ya fi masa fushin su su duka Juyawa ya yi ransa a jagule ya koma bangarensa Yana zuwa ya tarar da Na.ima ta zo, Tana ganninsa ta tabe baki a fili ta ce" an bi matar so kennan Na.ima, bata san dawan garin ba da bata yarda ta yi furucinta ba, bata san a kan tsani yake ba, bata san kiris yake jira ya fashe ba, bata san ta tabo tsuliyal dodo ba sai da ya budi baki bayan ya ja ya toge ya dafe tsatsonsa da hannunsa na hagu ya nunota da manuniyar hannunsa na dama ya kankance idannuwansa ya ce" *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 7 Wato ga sakarai wawa marar hankali Ga dan iskan nan ya dawo Ga danki da kika tsana bara ki sauke masa kwondon rashin kutunci Wato ga shegen nan ya dawo To Na.ima sai ki mike ki ciro wayar jikin bangon dakinki ki ki lakada min dukan jaki kin ji? Au, girmama kin da na yi na dauke ta na kaita bangarenki dan ku yi zumunci ne laifina ko me? Shin ku dukanku marainin ku nine? To bara ku ji baki dayanku, bilahilazi karya kuke! Ni ba sakaran namiji bane au ku hade kanku au na dauko rigar rashin mutunci na yafa na yarfa maku kalar nawa takun sai a auna a ma.auni idan naku ya fi rinjaye zan sadako! Kan muradina ba abinda ba zan iya yi ba, muradina a wajenku kuwa shi ne ku hade kanku ku yi zumunci! Abdaul jabar nake haihuwar Mina girman maka ni da ku shege ka fasa! Yana gama fada ya ja tsaki ya juya dan komawa bangaren Hafsar domin ya ga alamun idan har ya yi sanya zasu mayar da shi wani sauna ne zancen ya tafi a shashance Yana zuwa turawa ya yi ya shige uwar dakanta ba tare da ya nemi izini ko wani lako lako ba A lokacin Hafsat na tsaye gaban gadonta zintir haihuwar mamanta tana shafe jikinta da man zafi ko zata ji damar ciwon da yake mata domin ita cikinta bai zo mata da wani ciwace ciwace ba sai dai taunar jiki da abubuwan da ba za.a rasa ba Turus ya yi yana kallon bayanta da ta baiwa kofa, Dukawar da ta yi dan lakato Victago din ta kuma bin jikinta da shi ne ya kusan dauke numfashinsa Da sauri ya rintse idannuwansa sai dai yana rintsewar ya ji idannuwan sun kuma budewa suna kara waruwa kan abincin su Shi da ya shigo da niyar yi mata wankin banban bargo sai kawai ya ji ta shiga bulale shi da taimingiyar dukan rakumi! A hankali ya taka ya karasa bayanta Rungumeta ya yi a jikinsa tare da lumshe idannuwansa Ta so tsorata dan bata ji shigowarsa ba ta raja.a a abinda ke gabanta sai dai jin kamshin jikinsa ya sakata sauke ajiyar zuciya ta lumshe nata idannuwan itama tana jin yanda yake bin jikinta da shafa cikin nutsuwa yana jan numfashi A hankali ya dora hannunsa a kugunta pamkameme da shi kafin ya shafa kasan mararta Murya can kasa tamkar ba muryar da ya gama kirta fada da ita ba ya ce" cikin ki a shafe yake sosai, a haka akoy ajiyata na wata hudu? Ki ringa cin abinci Kauriyata kar ki haifa min yaro da tamowa Hafsat ta saki murmushi tana jin wai yaro da tamowa, ita kanta mamakin cikinta take a haka wai da mutun a ciki? A hankali ya kuma shafota ya ce" na kai ki bangaren Na.ima a farko.ne dan tana matata ta farko kafin ke, ita ce uwar gidana ke kuwa amaryata, ina so ki girmamata itama ta girmama ki, ban fi son wata fiye da wata a cikin ku ba, dukanku zabina ne Hafsat ba na kowa ba, dan Allah, ku taimake ni ku hada kanku ku yi zumunci tsakaninku hakan zai haifar min da kwonciyar hankali harma na samu karfin gwuiwar fita nema cikin nutsuwa Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juyo jikinta na dan rawa rawa ta kama lebensa na kasa ta shiga tsotsa idannuwanta a lumshe Ya fita haukacewa , jin zai zarme ya sakata dakatar da shi a hankali ta rada masa a kunnensa cewa yau ranar auntyna ne, Sakinta ya yi shima yana janyo numfashinsa ya sauke mata manyan idannuwansa da suka canza kalla yana kallonta Murmushi ta yi ta mana masa kiss a kuncinsa a hankali ta furta" i love u Hannunsa ya kara mikowa dan ya damkota ta saki karamar dariya ta zile da sauri sauri gudu gudu da gaya ta afka bayin dakinta tana juya jikinta wanda hakan ya saka shi yin sakalau da baki ya bita fa kallo Sai da ta bacewa ganninsa sannan ya saki murmushi ya ce" Yar malan, bakya jin magana walahi. Juyawa ya yi ya fice a dakin tun kafin ta karasa shi dan ya lura hanyarta ta hukunta shi kennan Sai da ya fita ya tsaya ya dafe bishiyar wajen cike da mamakin abinda ya faru, aa, ya zo ne da niyar itama ya sauke mata abinda ya saukewa yar uwarta, aman yaya aka yi ya bige da yar murya? Yaya aka yi bai balbaleta da balaki ba? Wato da ake cewa akoy matan da suke da kwarjini shi ne wannan? Matar Abdallah maman malan ta fi karfin ya kirta mara rashin mutunci? Murmushi ya yi ya girgiza kansa ya daga kafarsa ya nufi bangarensa yana ayanna bara ya koma itama ya rarasheta ko dan kwatanta adalci a tsakaninsu, bale a yau
Chapter 92 · 0% Book details