Sashe 74
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hafsat na farkawa daga baci ta yi ra.ayin buda facebook, tana budawa ta dora hotonta a dp dinta ba tare da dar ba, sannan ta saka sunnanta tsaf Hafsat maman malan, ta koma Whatsupp ta buda Sai da ta budar ne ta shiga neman numbobin yan uwanta du ta saka ai kuwa ta shiga takura su sun ki lekota sun kawota har sun kare da ita kennan? Su kam suna bata amsa suna rarashinta su a tunaninsu ta kwontar da hankalinta har mijinta ya bata damar hawa whatsup da facebook Saukowarsa kennan daga masalaci Ya nemi waje ya zauna, balarabiyar dake masa girki ta kawo masa tea da dan abinci kadan wanda salak nema kawai aka gyara da kayan lambu da mayonaise ta juya Cikin nutsuwa ya sha tea din, yana gamawa ya mike ya dauki wayarsa ya shige can kuryar dakinsa ya dauki wayarsa katuwa kirar iphone 11 pro ya zauna bakin kujera baba ya danna kiran number Na.ima Na.ima dake kwonce saman bed doguwar kujerar falonta ta daga kiran Tana dagawa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shiga shasheka tamkar wace zata fashe da kuka Idannuwansa ya lumshe, a hankali ya ce" menene? Sai da ta sauke ajiyar zuciya jin muryar muradin ranta sannan ta ce" ka dawo gida Abdul da idannuwansa ke lumshe ya ce" kin daina fushin? Na.ima ta yi shiru, sai kuma ta saki wani dan marayan kuka irin na shagwababun yara, tana yi tana jan majina sosai hawaye na bin kumatunta A hankali ya ce" zan kashe fa Da sauri ta ce" ka yi hakuri, Abdul dan me mani kishiya? Me na gaza Abdul? Abdul haka zaka ci gaba da aure aure ko fada min ba zakana yi ba bale har na yi tunanin zan samu rarashi? Idannuwansa ya bude sosai , a hankali ya kuma fadin" Na.ima, tun yaushe kike so na? Wani irin so kike min? Na.ima ta gyara kwonciyarta ta ce " ina son ka da dukan karfin jikina, ina jin kaunarka har bargona Abdul ya lumshe ido yana mai jin tausayinta har cikin ransa, a hankali ya kuma cewa" dan me zaki yi fushi dan na sako mace cikin gidana dan na kara raya sunnar ma.aiki da ita? Na.ima, a tunanina ko kura na kawo maki zaki kulata ki ciyar da ita Zaune na.ima ta mike, a hankali ta ce" Abdul, ko zaki ka kawo min, zan bashi nama, aman idan macen da zata rabarmin ni.imatacen kuma tsadadan jikinka ne, ina kishinta, Abdul.kishiya ka min ba yar uwa ba, ban iya boye abu ba bale na yi munafurcin zan so ta, ban taba ganninta ba, bana so na hadu da ita, Abdul bana son ta! Abdul dake sauraronta da mamaki ya kali wayar, murmushi kawai ya sakar mata a wayar ya datse kiran Mikewa ya yi ya bale agogo hannunsa ya ajiye, kansa ya daga ya kali agogon dakin, karfe biyar ne na yama, ya yi daidai da karfe goma sha daya a Niger, Doguwar fara kar din jalabiyar jikinsa ya cire ya kwonta saman bed, A hankali ya lumshe idannuwansa, Murmushi ya saki, a fili ya ce" kina ina? Kina me? Ke da wa? Shin kin saki ranki a bakon waje? Har yanzu kin tsane ni? Na san ba zaki taba so na ba, Hafsat kin raina ni sanadiyar sannin na kayar da zina abin yi a da, da wahala ki ga girmana bayan na sha yin izgili kala kala a gabanki, kin dauke ni mai wulakanta mata dan kin ga rayuwar taka tsantsan da na yi da matata kin dauki hakan a matsayin ni mai kudi ne, mai halayar wasu masu kudin Murmushi ya yi yana dauko wayarsa ya kunna ya shiga whatsupp dan kiran kampaninsa, a fili ya ce" ba dole ba ki raina ni, ke da kike zuwa ki kakabe min kurar dakin mata kafin na raya sunna? Ke da kike gannin ke ke bani tsaro? Yana shiga ya yi kiran su, aka hasko masa kayan da ya yi oder, Yana kashewa haka kawai ya shiga bin sunnayen wayar yana ware wa.inda zai goge daga wayar Sunnan Kauriyata ya kurawa ido, Hotonta ne daga ita sai hulaa a kanta ba ko dan karamin hijab bale baba a saman dp Da sauri ya shiga cikin sunnan yana kallon yaushe rabonta da hawa ko tsohon whatsup ne bai taba sannin tana da shi ba?? Ga mamakinsa a lokacin ma tana online Lokaci daya ya ji gabansa ya yanke ya fadi, a hankali ya fara share zufa yana kallon wayar, Ya rubuta message ya fi a kirga yana gogewa, Ina bata isa na mata message ba, bata isa ba! Shi ne abinda ya fada Mikewa ya yi ya dauki wayar tafi da gidanka ya yi kira fada Ana dagawa ya yi maganar yana bukatar su hadu da wuri yana son juyawa gida A wannan ranar sai da ya fasa wayarsa sannan ya daina kokarin yi mata magana ta whatsup din Mamaki kawai yake, whatup? A washe gari yana fitowa daga meeting din da suka yi, ya zauna a wata yar cafetaria Ya fara shan cafe din kennan ya dauki sabuwar wayar da ya saka layinsa kirar samsung ya yi gagawar shiga facebook Tunani ya fada, sunnayenta sun fi million a duniyar nan, idanfa ta shiga da wani sunna daban? Wata zuciyar ta ce da shi" kai yanzu gani kake rashin jin maganarta har zai sakata ta shiga Facebook? Ba zata aikata haka ba mana Abdul Wata kuma ta ce da shi" kai rubuta maman malan! Ai kuwa har hannunsa rawa yake ya shiga dora maman malan Maman da suka hayo ba kadan bane, a hankali ya shiga bi yana jin zuciyarsa na dokawa Sai da idannuwansa sukai masa arba da Hafsat maman malan, ya duba da kyau yar ina ce da komai ya tabatar masa Kauriya ce ya ajiye wayar hannunsa Bakinsa ya hade waje daya ya cije lebensa, lale kauriya ta gama raina masa wayo a gidan duniya, yanzu shi shi shi? Shi zata wulakanta? Talar kanta take ko me? Ko wani rikeken dan iskan take so ya ankara da tsarin kayatuwar halitarta na fulawer da Allah ya kagota irin Mamuda take so? Ni ko? Ya fada a fili wanda hakan ya saka daidaikun laravawan dake wajen dan kallonsa Mikewa ya yi ya saka bakin gilashinsa ya fice a wajen Yana zuwa gida ya dauki passport dinsa dake ajiye gaban sif din dakinsa na baci ya shiga dubawa, yana gamawa ya danna kira dan tambayar shin zai samu jirgi ne???????? A ranar bai samu tafia ba ba jirgi, sai an saka shi a tafiar gaba Bayan kwana uku ta kama lahadi da safe Hafsat na zaune da aunty Mariam da ta zo kawo mata sauran turarukanta wace bata so zama ba aman Hafsat fir ta boye waren takalminta sai zaunawa ta yi du a takure tana kallon Hafsat da mamaki gannin ta sha wando da riga abinta tana shagalinta ga tamfatsetsiyar tvn gidan na hasko indiyawa suna rawa Jus din da ta mayar ruwanta shi ta kawowa aunty ta bata Aunty na sha ta kaleta , jus din ya hadu kauri kitib da shi haka kuma ua sha kananfari, a ranta ta ayanna wa ya koyawa maman malan wannan hadi? Ta san anfaninsa ne? Gidan ta bi da kallo, ba dati ko daya gidan tsaf tsaf tsaf da shi, ga kanshin turare dake tashi Da kyar auntu ta samu ta gudu bayan ta kara yi mata nasiha Ita dai murmushi kawai take har ta tafi ta barta Dawowa ta yi ta sake wani wanka ta saka doguwar riga marar nauyi fara kal wace sosai ta hade da jikinta dan rigar bata da wani girma bakinta gwuiwarta ta kwonta saman kafet tana kallon fim har baci ya yi gaba da ita Da kansa ya tuko kansa har cikin gidan nasa Daga cikin motar ya gyara zama yana hangen bangarorin biyu Masu yi kasu aiki na ta shawagi, mata ne mazan kwaya hudu ne wa.inda ke tsaron kofa kawai, aman daidai da masu baiwa fulawowi ruwa mata ne, kowace kuma a ma.aikatarta ya daukota, gidan du yan gayu ne ma.aikatan, girki kansa mata uku ke yi, idan wannan ta yi break fast, wancen ta yi na rana, wancen ta yi na dare , sai dai du yin nan da ake basu taba shiga bangarenta ba, hasalima bakinsu bautar bangaren Na.ima domin ko shara basu taba shiga sukai mata ba, yo mai gidan baya nan bai bada umarnin hakan ba, matarsa kuwa bata saka su ba. Sai da ya jima sannan ya bude ya fito a motar, daga katon kwadon dake kofar Na.ima ya gane bata nan, a hankali ya shiga takawa yana gannin sai a lokacin suka gane shi ne a motar dan sai zubar da abubuwan aikin suke suna risinawa sunai masa sannu da zuwa Amsa su kawai yake da hannu har ya fice ciki ya karasa dakinsa Wanka ya yi na kirki da ruwan dumi, sannan ya canza kaya zuwa kananun kaya Saukowa ya yi ya nufi bangarenta yana ayana irin abinda zai mata na hukuncin buda Facebood da whatsupp ba da izininsa ba ya tura kofar ya shiga ta coridor din dake sada ka da dakinsa domin kowani dagi da hanyar da zata kai shi dakin matan ba sai ya fito ta fili an ga ya shiga dakin matansa ba Hafsat dake dukunkune saman cafet tana baci bata san da an buda kofarta ba bale har ta yi wani abu, A hankali ya ringa takawa ya shiga, kamshin turaran wutar dakin ne ke ratsa kofofin hancinsa Tsayuwa ya yi ya kama tsatsonsa ya buda baki ya ce" *Kauriya* da karfi karfinsa Wata irin zabura ta yi daga kwoncen da take ta mike tsaye cirrr tana kallon inda ta ji amon murya gaba dayanta a zabure hakan ya saka hannun rigarta ya fado kasa bayin Allahn da ba.a saka masu bra ba suka dan bayana sosai daga sama sannan gaba daya gashin kanta ribom din ya fadi kasa haka kuma rigarta a sama daga kasan har pant din ya dan leko daga baya domin mikewar dama rigar ba mai tsayi bace ta dage mata sosai sai kawai ta yi sama ta haye mazaunanta masu tudu da su Galala