Sashe 61
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fa ita nan har tana gannin ramuwar da zata yi ta huce? Ramuwa ta fi ta barwa Allah ya saka mata? Sai da ya lakaci hancinta yana kallonta ya ce" shekarun ki arba.in da bakwai da wata hudu da kuma kwana ashirin da biyar yau maman Uwata, aman har yanzu akoy rigima......... Ki kwontar da hankalin ki, adu.ar nan dai da muke yi in sha Allah ba zata kuma ba, ai yanzunma Allah ya dawo mana da ita lafia ba karfinmu ko dabararmu ba ko? Kanta ta gyara a hankali sai kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya A kadan dai sai da Malan ya jima dakin mama yana ta yi mata nasiha sai da hankalinta ya idasa kwontawa sosai sannan ya mike ya kalli agogon hannunsa ya ce" yau ban ga ana shirin zuwa turakata ba Murmushi ta yi tana rufe idannuwanta irin ta ji kunyar nan, hakan ya saka malan kara sakar mata murmushi ya juya ya fice a dakin, har tsakiyar ransa yana so ya je ya ga kar a je fadan da mamanta ta yi mata tana can tana kuka, kai a duniya da ake cewa ko cikin yaya Allah na saka maka kaunar wani ta fi ta wani, haka yake jin kaunar mai sunnan mamansa har baya iya boyewa, dalilin wannan ne ya saka shi daukan damarar boyewa ko a gaban mahaifiyarta ne bale a cikin yan uwanta da sauran matansa ko za.a shafa mata lafia Bayan kwana hudu..... Hafsat a kilace take cikin gidansu, an yi gumurzun an kare an yi rigimar da tashin hankalin an kare, an yi yawan maganar da tsegumin du an lafa, masu jiran su ga ta tsiro da dabanci kala daban daban sun ga shiru, Abdul aziz ya yi sau ya fi a kirga bai ga ko kalar mai kama da ita ba bale ya ganta, kai hasalima ta zama kawar mamanta da kuma yayarta A yanzu du zama da tashinta tana lure da kyawawan dabi.un mahaifiyarta, idan aikin mamanta ne takan shiga ta zabga masu girki na ji na gani mai dadin dandano a zuba kowa ya ci da sabon taste wa.inda ta koya a wajen Formation na zama bodyguard Bata da waya, bata damu da rikewa ba , ita ta kanta take sai a yamacin yau mahaifiyarta ta mika mata wayarta ta da wace masoyinta na da wanda sanadiyarsa ta afka tashin hankalin rayuwa Ta jima tana juya wayar kafin ta kai ta saka a caji ta ci gaba da sha.aninta A rana ta shida mai dinki wato hajia Farida ta kawo dinkunnan da mama ta bata , Ai kuwa dinkuna ne masu shegen kyau rufafu tsararu sannan na gayu masu tsadar gaske, Ba karamin farin cikin kayan nan ta yi ba, haka ta hau sama wajen mahaifinta dan yin godiya, tana zuwa ya kara mata abayoyi kala biyar masu shegen kyau na yayi dukansu masu botira da mayafansu bakake masu tsari Kanta kawai ta sada ta rasa bakin magana, a hankali ta dago da idannuwanta sai ta ga mahaifin nata na kallonta yanai mata murmushi, ba komai yake jin dadinsa ba sai yannayinta na yanzu, wai mamansa ce ke nuna farin ciki dan an saya mata sutura, yarinyar da a da hayowa zata yi, ba ruwanta da neman izini sai dai ta afka idan a gaban wa sai dai ta fadi muradinta na kudi ta karashe da fadin" kuma a bani ko na je saurayina ya bani! Sai gashi yanzu a gidan duniya Allah ya nuna masa ita tana godiya harma ta rasa bakin godiyar Hannunsa ya daga mata dan ya tabata tana iya yi masa kuka a gurin , shi kuwa baya so , dan haka ta mike har ta kusa fita ta tsinkayo muryarsa ya ce" su ABDALLAH zasu dawo gari da zama karshen satin nan, kwana biyu ina tsaye kan saukar alkur.ani a gidan da zai zauna , kulun muna zuwa a sauke a yi sadaka dan gudun fitinar zamani Sai da gabanta ya fadi, a ranta ta ayanna me kuma zai dawo da shi kasar Niger? Kafadunta ta daga a lokacin da ta tuna asalin dan niger din ne shima fa, haifafan garin ne, haka kuma dangin da suka rage masa yan nan ne wato matarsa da kanwar mamansa Bata baiwa Malan amsa ba sai karasawa da ta yi da murnarta suka dadaga kayan da mahaifiyarta kafin su shiga yi masu turaran wuta da adu.ar Allah ya sa a mora lafia Bayan kwana goma Kwonce take tsakar dakinta wajen karfe biyar na yama, juyi kawai take tana tunanin wai yau zata yi zance, zancen ma da BS, zuwansa biyu sai yau Malan ya bashi damar ya zi su gana Mikewa ta yi zaune tana kallon madubin dakinta mai tsayi, kanta ta girgiza ta koma ta kwonta gashi har karfe bakwai din ta kusa, Tana nan kwoncen har karfe shida ta buga, buda kofar da aka yi ne ya sakata mikewa zaune tana kallon yayarta da ta shigo da yaronta da ya fara rarafe yana yawonsa ko.ina Bayan sun gaisa ne yayar tata ta bita da kallo, Can ta ce" Maman malan, ni ba bako aka ce zaki yi yau ba? Hafsat ta dubeta ta ce " eh Yayarta ta ce" to ya haka baki shirya ba Hafsat ta kaleta da mamaki ta ce" shiryawar me kuma auntu ? BS ne fa?? Sai da ta rike habarta sannan ta yi dariya ta girgiza kai ta ce" dan BS ne shine ba zaki kimtsa jikinki ba? Oya tashi tashi malama Mikewa Hafsat ta yi tana kallonta kafin ta shige ciki ta dauko abaya daya daga cikin abayoyin Aba ta saka abinta a nan sannan ta shiga saka turarukan wutar da ta miko mata Tana kokarin yana mayafin dan kwalin ta tsayar da ita ta zauna ta dan gyara mata fuska da kwalinta sannan ta yana mata dan kwalin a kanta Tsaf hafsat ta fito tamkar ba ita ba, wani irin kyau ne ya bayanna a tare da ita wanda ita kanta sai da ta shafa gefen fuskarta sannan ta yi murmushi Ana fitowa sallar magariba aka suka zauna tsakar gida inda malan ya basu minti talatin su gana A zancen nan Hafsat banda tambayoyi a kan aiki ba abinda ta tsare BS da shi, shi kansa sai ya kasa wani yi mata zancen soyaya sai da ya tashi tafia ne ya ce da ita" Hafsat, ina son na turo a yi komai da wuri a gama, dan kin ga malan baya son dogon zance Sai da ta ji gabanta ya fadi, ta dan tsura masa ido aman sai ta kasa ce da shi komai, Murmushi ta sakar masa sannan ta shige ciki da dan gudu gudu hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya juya ya tafi ya shiga galeliyar motarsa yana tunanin sai dai a waya ya mata maganar aikinta da kuma dukiyarta Can wajen karfe biyun dare, dare ya tsala Hafsat na zaune tsakiyar gadonta daga ita sai dan gajeran wandonta da yar rigarta na barci ta yi zuru da wayarta a hannunta tana dannawa tana game Message ne ya shigo mata kamar haka " *KAURIYATA, NA KASA BACI* kurawa harufan ido ta yi tana kallo, bugun zuciyarta ne ya canza lokaci daya hannunta ya fara rawa, Du duniya ba wanda ke haye mata irinsa, shi ne, walahi shi ne Wayar ta ajiye tana kallon rubutun tamkar wanda ya yi da hannunsa idan hasken wayar zai dauke sai ta danna ta kara kallo A hankali ta rubuta " *ME YA HANA KA BACI?* mikewa ya yi zaune daga kwoncen da yake yana mai hararar wayar, kafin ya rubuto " *ke, gida kika je kika tara samari haka? Bakya dan jan aji daga yi maki magana har ki bani amsa ko kin sanma da wa kike magana ne?* A lokacin da ta karanta sai da ta saki murmushi, sannan ta rubuto" *na san ko kasuwa na yi a tsakiyar dare irin na barawo? Dole bazawara ta ringa damka da karfi karfinta mana* Wani uban tsaki ya ja a lokacin da ya karanta message din, Zama ya gyara ya shiga dandankara magana son ransa, har ya so saki sai kuma ya koma da baya ya zauna ya jinginar da kansa jikin bed din, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon waje daya sai kuma ya rubuta message kamar haka" *Na yi missing din ki amaryar BS* Numfashinta ne ta fara ji yanai mata sama sama, lokaci daya kuma ta koma ta mike kafafuwanta saman bed din , sai da ta yi mika nitsatsiya sannan ta rubuta message kamar haka......... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 Suna nan tsaye kusan minti ashirin har ta fara kitan layin Malan dan ta fada a zo a dauketa sai ga wata mahaukaciyar hamer baka wulik ta tsaya a gabansu sai maskin sabuntaka take tana dana ashar din rashin mutunci ita kadai sai lillon iskanci take tsabar an murxata an yi gudu da ita, bakaken gilas ne a jikinta gaba da baya hakan ya sa koda wasa ba.a gannin na ciki komai kwakwarka dan sabuwa ce , komanta sabo ne Daga cikin motar ya kare masu kallo lafin ya sauke gilashin yana jinjina rainin hankalin Hafsat, ta sab sarai ko waye a motar aman ta wani kawar da kanta tana kallon wannan jajir fin uwa gwonda, Dariya ya yi a lokacin da yake sauke gilashin ya rage sautin cikin motar ya