← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 94

Sashe 26

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 2 Fuskarsa ya hade sosai kafin ya ce" wa kike magana kanta? Hafsat ta sauke lumfashi, ta dube shi da kyau, ta san fa ya gane wanda take nufi aman zai wani tambayeta! Dan haka ta ce" mai aiki mana Abdul ya lumshe idannuwansa ya ce" ki ce dai budurwar ubana! Ido ta zaro tare da dora hannunta saman bakinta tana dubansa, bata san lokacin da ta ce" Abdul! Idannuwansa ya bude daga lumshen ya kalleta da su kafin ya mike gaba dayansa ya shiga kokarin bin hanyar cikin gidan Bayansa suke bi daidai da takun tafiarsa, Bata gajiya ba a lokacin da zai shiga dakinsa ta yi saurin fadin sunnansa ta hanyar kafe shi da ido Tsayawa ya yi yana dubanta , ido cikin ido suke kallon juna sai kuma ya yi kasa da idannuwansa ya mayar wajen lebenta da shi baima san nan ya kurawa ido ba a hankali ya ce " Hafsat, sunna zan raya, kin san bata jira dai ko? Da sauri ta rintse idannuwanta sanadiyar kunyar abinda ya fada, gashi ya fada ne da yaren da kowa zai iya ganewa ga Hasana itama a kusa da su take sosai dan kuwa ita zata shiga ta gyara dakinsa kamar yanda aka saba, Juyawa ta yi gaba dayanta ta koma gefe ta tsaya, ta kasa daga idannuwanta bale har ta yi ido hudu da daya a cikinsu, gaba dayansu kunyarsu ta ji ta mamayeta a haka har bata san lokacin da ya shige ba, sai takun takalman sarauniya ya shaida mata har ta karaso, A hankali ta dago da dubanta ta sauke saman Ni.ima,.ta sha wani danyen lesh mai ruwan madara, ta sha kwaliya fuskarta tamkar ka saceta ka gudu, Ni.ima ba ramama bace, sam bata da rama, sannan ba sakaken jiki ne da ita ba gashi ya hadu da kulawa dan akoyta kwaliya sosai, budurwa ce mai zamani wace dubai ke son malaka a wannan karni Yannayin takunta ke tafiar da isarta, Ni.ima ta jiki, jika irin ta naira, dan kuwa bata nema ta rasa ba, ga kuma daidai gwargwado iyayenta sun bata tarbiya, so ne kawai ya sakata sangarta da shiga sabgar Abdul Kanta ta sada dan kuwa du macen dake wajen a tsaye sai da Ni.ima ta kwasheta da kallo ta yarfata kasa da idannuwanta sannan ta tsayar da masu bin bayanta da hannunta ta juya ta buda dakin Abdul ta shige abinta ba tare da damuwar komai ba a fuskarta Tana shiga gabanta ya fadi, dan kuwa ta san abinda ya kawota dakin, wai ita, yaushe zai zauna ya yi hira da ita irin na soyaya? Yaushe xai dubeta da duba na darajanta dan adam a matsayinta na matarsa? Inda yake zaune ta je, tana zuwa ta haye saman cinyarsa ta zauna tana kallon yanda yake lunshe ido Abdul dake binta da kallo ta kasan idannuwansa ya saka hannayensa ya janyota a hankali jikinsa sosai sannan ya shiga kokarin sarafata dan samun nutsuwar damuwar dake damunsa Binsa kawai take, du yanda ya jirgata sai ta bi ba tare da ta nuna wani yannayi na shauki ko murafin hakan ba, Tun yana yi da nuni a yannayinsa na muradin gannin shaukinta har ya cire a ransa ya shiga kokarin zuwa duniyar ma.aurata Da sauri ta rike damtsen hannunsa wanda du girman hannunta sai ya kasance ko rabin damtsen bata cika ba bale har ta cike wajen da hannun nata, Muryarta na rawa ta ce" ka...ka bari na birgeka mana? Yakan ce da ita birge ni, a duk ranar da baya son zuwa waje mai kakant din , takan yi ta fama kafin ta samu ya samu kansa, har bata son yace da ita ta birge shi dan haushi take ji lamarin na wahalar da ita, sai gashi yanzu da kanta ta nemi ta birge shi? Tsai ya yi da niyar shigar nata ya tsurawa yannayinta ido, Tabas bata cikin ra.ayin hakan, sam babu muradin hakan a tatare da ita, Aman rabonsa da ita fa yau 2 days, shi ne batama daukinsa? A hankali ya janye hannayensa ya rage nauyinsa a jikinta sannan ya mike gaba dayansa, Maimakun ta ga ya juyo ya bata damar birge shin sai ta ga ya nufi bayi Da sauri ta mike zaune tana raraba ido, gabanta ne ke ta faduwa lokaci guda kuma ta ji wani haushin kanta wanda har ya hadasa mata zubar da hawaye, ya salam, ya yi fushi? Fushi ya yi ko me? Nan take zaune tana ta sharar hawaye har Abdul ya fito da tawul yana goge jikinsa Turus ya ja ya tsaya da mamaki yana kallonta tana kuka, Yana son ya budi baki ya tambayeta abinda ke damunta aman bai san me yasa yake da nauyin baki a kan lamarin mata ba, shi dai zai maki surutu ne idan ya yi niyar dizga ki, shi banda Kauriyama wace mace ce yake sakewa ya yi ta surutu da ita? Kallonta da yake ya sakata mikewa gaba dayanta ta nufo inda yake tsaye ta mika hannu zata taba shi ta ce" dan Allah ka yi hakuri kar ka yi fuahi da ni Abdul ya dan ja baya yana dubanta kafin ya fahimci inda ta nufa, Wajen ajiye tawul din ya nufa ya sarkafe shi ya juyo inda take tsaye ya ce" bana takurawa mace dan zuwa duniyarnan, ina son koda yaushe duniyar nan ta zama a kawace, ba fushi na yi ba, ki saka kayanki kinje ki tsaftace jikinki Yana gama fada ya bude wajen suturunsa ya kurawa wajen ido, Kaya ne kala daban daban, na manyan manyan kudade sannan masu kyan gaske, Du a cikinsu ya janyo wata riga fara ya zura ba tare da ya saka komai ba ya dawo saman bed din ya zauna, Har ta fice a dakin, da kuma kuka ta fita, Bakinsa ya tabe yana mai kallon wajen windows din da ba damar ya shaki iskan wajen an rufe ruf Karamar wayarsa ya mika hannu ya dauko ya kunnata, Kara wayar ya yi a kunnensa bayan ya danna kira a wata bakuwar number Bai jima yana wayar ba ya ajiye ya mike ya shiga shiryawa sannan ya saka akaiwa masu tsaron kofa maganar zai yi bako a bar shi ya shigo A lokacin da bakon ya zo , Abdul ya nemi Hafsat da ta shigo wajen da zai gana da bakonsa dan ta kula da lafiarsa, Bakon wani mutun ne da ba za.a kiraye shi yaro ba, magidanci ne ya kwana biyu sosai sai dai ba tsoho bane, Irin mutanen nan ne wayayu, masu shegen wayo da son da bakinsu su sayi du wani gara, Suna siyen kuwa dan idan ka yi wasa lokacin da zasu tafi da kai kai kanka sai ka laluba ka ga babu kai Tunda ya zauna suka gaisa Hafsat ke tsaye gefe tana aikinta ba tare da ta bada hankalinta kansu ba Tambayar da Abdul ya jefa masa ne ya sakata maido hankalinta inda suke zaune ta raja.a dukan wani nutsuwarta a kansu da rataunawar tasu, sannan sai a lokacin ta gane ya saka ta shigo ne dan wannan dalilin Mutumen ne ya dago hannunsa na dama ya shafi gaban goshinsa kafin ya maida hannuj bayan keyarsa ya dan sosa sau biyu ya ce" eh Elhaj, tabas marabina da su na ga dan nata , sosai saurayi ne kakarfa sai dai sam baya kama da kai, kuma shi fari ne, Abdul dake kallonsa ya ce" kuma yaya sunnansa ne? Yanzu a ina suke ne? Ko nace marabinka da su a ina? Dan zakutowa mutumen ya yi ya saka hannayensa ya ja rigarsa ta kara yin sama hakan ya baiwa dogon wandon rigar damar kara bayanuwa, Agogon hannunsa ya murza da babar yatsarsa, ya zagaye ya kuma zagayewa, sai da ya rintse ido na sakonni sannan ya budi baki ya shiga bada labarin marabinsa da matar da kakaninsa suka koreta da cikin mahaifinsa, wanda ya tabatar masa cewa namiji ta haifa harma ya ga mutumen da idannuwansa, ya tabatar masa cewa makudan kudadan da kakaninsa suka bata dan ta kula da rayuwar dan da zata haifa sun isheta rayuwa suna cikin wadata suna rayuwa cikin jin dadi, Abdul ya sauke kafa daya daga saman cinyarsa ya ce" ta musulunta ne? Sai da ya kurawa Abdul ido sannan ya ce" ae, eh eh mana Elhaj ta musulunta mana, Abdul ya gyada kansa, kafin ya maida dubansa wajen Hafsat ya ga kawai mutumen take kallo da sexy eys dinta, Komawa ya yi ya jingina da jikin kujerar ya ce" wane da wane kika yarda a cikin magangannun nan? Hafsat da ta yi firgigit ta maida dubanta wajen Abdul, ta kasa cewa komai, dan ita dai ba sannin mutumen ta yi ba, duda yannayinsa na nuni da rashin gaskiya da son dole dole sai ya yi cinvaincre din Abdul din, ba zata iya cewa komai a kan hakan ba, Abdul ya lumshe idannuwansa ya ce" wato idab mutun baya son gannin abu a zahiri ba zai gansa ba? Mutumen ne ya ce" Elhaj ban gane inda ka nufa ba Abdul ya bude idannuwansa aman bai basu damar budewa baki daya ba ya ce" karya kake min Murtala, gaba daya magangannun nan da ka fada ba daya dake gaskiya, Kai hasalima baka ga wannan matar ba, dan kuwa da ka ganta da ba zaka ce ta musulunta ba dan can dama musulmar ce Saukin mikewa tsaye ya yi yana zarar ido, hakan ya bashi damar tsayawa kerere gaban Abdul Ya buda baki zai yi magana sai jinsa ya yi an dangwarar da shi zaune saman kujerar da ya miken, Mamaki ne ya kama shi gannin yar budurwar an ce ta mayar da shi haka da
Chapter 26 · 0% Book details