Sashe 31
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bai ga ko irin rigar mararsa lafia ba bale ya dauka ya saia Dubansa ya kai kan BS dake tsaye ya ce" ina rigar asibiti ne?? Docter ya dube shi da kyau kafin ya yi murmushi ya ce" ai oga bamu da shi a nan mu, wannan dakinma mun tanadeshi dan irinku, ba kowa ake sakawa a ciki ba, Da mamaki ya dube shi, ya ce" ku su wa? Wace asibiti ce? BS ya dan zaro ido , kafin ya tari numfashin Doctern ya ce" am, am sire mu je kawai, ga rigata da wandona bara na je cire sai na je na tsayar da taxi, Abdul kara zaro ido ya yi, taxi? Taxi fa yace? Me ya hada shi da taxi? Shi ko a saudiya bai shiga taxi ba, yana kallo BS ke kokarin cire kayansa, bai hana shi ba, dan walahi ba zai yarda ya ratsa gari ba kaya ba, idan fa ya hadu da wanda ya sani? (Abdul, a taxin? A dazu da ka ratso ko dan kana duniyar summa ne? Bawan Allah BS haka ya cire kayansa, Allah ya taimake shi, shi wandon na ciki ya kai har gwuwarsa sannan sakake ne, dan haka da mamaki ya bi Abdul da kallo har ya saka kayansa inda sukai masa wani kabe kabe rigar ta wani irin tamke shi dan sun masa kadan, wandon kansa ya tsalake masa sosai tamkar dan izala aman kuma da damamiyar riga, Ido ido sukai da doctern sannan ya fice ya nemi taxi ya tsayar Nan fa Abdul ya shiga taxin gidan baya ya hakimce inda BS ya shiga gaba ya fadawa mai taxi cewar sun yi shata har inda za.a kai su Shi dai Abdul yana kallon gari, da irin yanda motar ke sama da kasa da shi, da irin yanda suke kutsawa sunna wani rin gudu, a haka suka zo suka wuce danjar da ta bayar da jar wuta a guje inda Abdul sai da ya dora hannunsa samman kansa ya leka da kyau ya dubi mai taxi din ya ga ba yaro bane datijo ne sosai aman yake wannan tukin Sai,da suka zo danja wace polisai ke tsaye ya ja ya tsaya kafin ya lailayo wata ashar ya dura ya ce" mutanen banza ido yay masu kuri, ka fice ka janyowa kanka balaki, to ba dai aljihuna ba! Abdul kam komawa ya yi ya zauna yana mamakin ashe bai ga komai ba? Shi bai taba shiga taxi ba, yana hawan tsofafin mashin ya shiga wurare masu hatsarin gaske, aman yau gashi a taxi zata kashe shi! Tafiar da idan a motocinsa nene bai fi su yi minti ashirin ba, sai gasu a minti kusan arba.in Ko tsayuwar da direban motar zai yi sai da ya wani irin ja ya yi wani kuuuu motar ta fitar fa hayaki sannan ya tsaya ya fitar da kansa ya ce" ikon Allah, jama.a ku ga ginnin gida tamkar ba za.a mutu ba? Yanzu mai gidan nan haka zai mutu yana ji yana ganni a nutsa shi a kabari? Han gaskiyar mabaraci da yace a baku a nan mu a can mu samu BS tamkar ya mangare mutumen haka yake ji, gashi tsaf sai da Abdul ya gama sauraronsa ya bude ya fita daga motar yana duban yanda BS ke hararn mutumen, aman cikin ikon Allah sai mutumen ya ce" kai yanzu bawan Allah shaye shaye ka yi ka tunkaro gidan nan mai zagaye da arnawan sojoji ko rigar kirki baka da ita , ka dauko wannan shi kuwa da wata riga a dame a jiki tamkar bazawarin kwarto da wani wando ko sauka kasa bai yi ba yana lumshe ido uwa ya hadiyi jinjirar tinkiya? Tsayuwa ya yi ya dafe tsatsonsa sai da mutumen ya gama ya shiga kokarin tayar da mota yana mika hannu BS ya bashi kudinsa motar sai tayar da hayaki take abinta Abdul ya dubi BS da du ya daburce ya kankance ido ya ce" ni, ni din ne dai bazawarin kwarto? Bama saurayi ba ko *Bashi*? Ni dai ne mai tsangalalen wando ko? Na gode! Yana gama fda ya kara gaba abinsa yana tafia da sauri da sauri dan da tazara sosai dan kuwa ta kofar bayan ya saka a ajiye su , to shi wannan direban da ta gaban kofar ya je yaya kennan? Wai bama wannan ba, a ina sire ya san sunnansa Bashir? Ita mana! Ya huci ita zata fada masa du sunnayenmu na gaskiya? Wata zuciyar ta bashi amsa inda nan da nan ya ji haushi ya turnike shi, nan kuwa datijon nan ya ce" kai yaro ya haka? Cinye min kudin zaka yi ne ko me? Ka bani kudina ko na fito mu yi wace zamu yi da kai a wajen nan dan bari gannina tsoho, na fi ka iya shegantaka BS ya ciro jika goma ya dankawa tsohon yana dubansa ya shiga neman canji, nan ya duko ya ce" bab, ai duka na baka, ka dan ban adireshinka mana na kawo maka hira? Tsohon ya dube shi da kyau ya kalli kudin hannunsa, sai kuma ya yi shiru, can ya ce" yanzu yaro, tsakani da Allah dan ka bani wannan zaka biyo ni ka yi kudin kaina? Kudin kaina mana yaro, da ganninka ai ba.a ga yannayin mutumen kirki ba ko? BS kam gannin wannan mutumen komai ma yana iya fada kai tsaye idan ya so kowace wace ya saka shi saurin dage kafarsa ya bi bayan motar da kallo ya dauki number motar dan walahi sai ya tarda shi ya ci masa abinda ba za.a fadi ba, gashi kiri kiri zai hada masa masifa da wannan mutumen Ya jima yana shawagi dan ba zai shiga kai tsaye su hade da Abdul ba, dan kuwa ya ga alamar ya gode din nan yana iya yi masa komai Abdul kam na shiga, bai zame ko.ina ba sai dakinsa, Ya jima cikin ruwa masu dumi, ya lumshe idannuwansa ya afka duniyar tunani, Waye ta ganni? Yaya sifarsa take? Yaya aka yi ya san da wannan abin da zai same shi? Sihiri ne, wannan magannin makarin sihiri ne ba na poison ba, ko likita bai ga guba a cikin bakin jinnin da ya fitar, Waye kuma ya neme shi da sihiri? Wanda ya fadi makarin a gabansa aka yi ko yaya aka yi ya sani har ya bada makari? Sai da ya kusan kwashe minti ashirin yana gasa jikinsa, sannan ya wanke jikinsa sosai da sosai ya fito ya zauna bakin gadonsa, Dakin ya bi da kallo, daga nan aka fitar da shi ko daga ina? A halin summa, yanzu da ya zama marigayi kennan? Murmushi ya yi kafin ya daga kansa sama yana shafar gemun fuskarsa, Ni.ima, Ni.ima toh wace irin mace ce? Tana ina? Idan tana zayanno irin son da take masa har mamakinta yake, aman shi baya gannin kulawa irin ta son? Bata taba nuna yi masa girki ba, bata taba idan sun gama abinda suke ta gyara shinfidarsu ba, ita dai barta da yarinta, Shi yasa yake zaune da niyar aure aure idan komai ya lafa, Sai ya auri hudu, ya jera su daki daki, tsala tsala, su ringa yi masa juyi suna kashe masa ido, ya wuni a daki abinsa (yanzu marar lafiar ne? Haka ya yi ta zancen zuci, har aka yi kiran magarib nan ya ajiye komai ya mike ya nemi sallah Bayan sallar magariba, sai a lokacin BS ya nufi ainahin bangaren nasu, A lokacin da ya karaso Abdul har ya shige daka wanda ya gama zance da Muhammad da mahaifin Muhammad din a waya A lokacin da ya hangota tsaye sai da gabansa ya fadi, ita da Hasana ne tsaye a kofar dakin Abdul sai bodyguard din Ni.ima rigar sojan da ya amsa ya kara ja ya gyara a jikinsa kafin ya karasa inda suke tsatsaye, Dubansa ya kai wajen Hasana cikin daurewar fuska ya ce" ki yi abinda na saka ki yanzu, tsalan kwado kai ka irga mata Fuska hade ya juya ya nemi dakinsu shi da abokin aikinsa ya watsa ruwa , har zai fito ya tsaya ya dauro alwallah sannan ya saka wasu kayan ya dauki salayar abokin aikinsa ya shinfida ya hau ya yi tsaye yana mai kallon alkibla, rabonsa da sallah har ya manta ranar (wa.iyazubillah) , haka ya gabatar da sallar magariba ya yi nafila sannan ya mike ya fice yana tunanin karbar adu.o.im shiriya Abdul bai nemi sakewa da kowa ba har sai da ya kara kwana biyu ya warware sosai ya kara samun lafia A yamacin yau ya fito da wandonsa wanda tsayinsa ba zai fi gwuiwarsa ba sai riga mai hannu kananu fuskarsa dauke da gilashi A lokacin da ya fito du suka shiga hada hadar shirin fita, inda Hafsat da Hasana suka take masa baya, Sai da ya fito tsakar gidan ya tsaya ya shaki iskar yamar dake kadawa, sannan ya juya cikin nutsuwa abinsa ya nufi bangaren ruwan dake gidan inda ruu suka kuma biyo shi su hudu harda BS A lokacin da ya zo wajen ruwan ya yi tsaye, can ya hango runfarsa ta shanawa, wace a nan yake holewa da yan matansa, Kansa ya girgiza yana murmushi ya kai dubansa wajen Hafsat dake kallon yanda ruwan ke garairai da shi sai daukan hankalinta yake, ya ce" shiga mana, Ta san da ita yake, ta share shi ta kawar da dubanta daga wajen ruwan Hakan ya saka shi juyawa ya koma wajen kujera ya zauna, su kuwa suka tsaya a bayansa wato Hafsat da Hasana Kaffafiwansa ya daga ya fora saman kujerar sannan ya dago fuskarsa ya tsura mata ido ta cikin gilashi wanda hakan da ya yi ya saka ta kawar da fuskarta inda hasana kuwa ta kale shi ta kauda kanta dan kar ya ga ta kura masa ido, Rigar jikin nasa fara ce mai digo digo blue sannan mai boturai, boturan saman du sun bude har uku hakan ya saka gashin kirjinsa bayana kadan, harda pecto dinsa na gefen hagu ana iya hanga idan aka kure shi da kallo Harshen larabci ya dauko, da sak irin larabcin larabawa wanda idan ba kwarewa ka yi sosai din nan ba ba zaka gane komai ba ya ce" na yi marmarin gannin gashin kanki kauriyata,