Sashe 24
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Abdul ya kaleta, inda Muhammad ya ce" aa, yau harda yar rakiyar taka kake tafe har cikin dakin nawa? Abdul ya tsurawa hafsat ido, ita kuwa ta sada kanta kasa ta raba shi ta fice a dakin hakan ya baiwa Abdul damar shigewa ciki yana mai jin ransa na suya, Me ta zo yi dakin nan? Me ya kawota? Ba dai abinda ya hanata ne take kokarin daura aniyar yi ba? Haka ya je suka tatauna da amininsa, dan uwansa kafin ya mike ya zarce dakin Furaira Gaba daya hirar da ya yi da matar bai fahimci komai ba sai tsabar bariki dake dawainiya da ita, Karara ya fahimci cewa abin duniya ya rufe mata ido, kuma shi ke janye da ragamar rayuwarta Dan haka ya biyewa sallon kidanta suka doka gangar iya iyawarta ya bari bangarenta bayan ya nuna mata kudi akoysu, wanfa hakan ya sakata kara share waje ta baza tabarmarta Kwonci tashi, har an kara sati biyu cikin wannan hali, A cikin gidan Abdul, an ci gaba da fuskantar hatsaririka kala kala, Du wani wanda ke gidan ya koyi sannin mahinmancin lumfashinsa, irin hare haren da aka ringa kawowa ya saka kowa ya gane cewa rai ba karamin abu mai daraja bane da Allah ya arawa bawa wanda yake iya karbarsa a kowani lokaci, hakan ya saka musulman ciki suka kara mayar da kansa wa Allah, christocinma suka kara rike adinnin su, Har yanzu Furaira na gidan, wanda take son fitarsa ido rufe aman cikin ikon allah Allah hakan ya gagara ta rasa dalilin da ya sa du irin iya barikinta da wayonta ta kasa samo kalaman da zasu saka shi barinta tafiarta dan kuwa tana son fita a gidan Hafsat na nan har ta fada ina nufin ta rame tsabar irin yanda ta sakawa kanta damuwar wani a ranta, dan kuwa ta zama tamkar fatalwa wajen iya leken asiri da daukan rahiranni tana hadawa a cikin kundin bincikenta dan samun amsa gamsashiya wa hasashen da take wanda ke nukurkusarta ita kanta yana bata tsoro, dan kuwa amsar da take hangowa bata tunanin idan ta fito fili za.a wanye lafia A tsakiyar daren talata, a wannan rana ce Hafsat ta saurari wayar da ta firgitata, A wannan rana ne ta fito da niyar zuwa dakin Abdul a talatainin dare, A wannan rana ne aka wayi gari ba Hafsat ba labarinta, A lokacin da BS ya shiga dakinta gannin har karfe tara da rabi ta fice bata fito ba bayan hakan ba sabonta bane yana shiga ya tarar ba computenta, ba wayarta, ba du wani abin aikinta an kwashe babu ita babu alamunta, Hakan ya saka kansa sarawa ya fito da gudu yana harhada du wani ma.aikacinsa suka rarabu suka shiga nemanta ilahirin gidan A haka ya je dakin Abdul da ya gama ganawa da Ni.ima ya shiga a firgice yana mai tambayar a yau ko ya ga Hafsat? Abdul dake zaune saman salaua ya dago a hankali tare da rintse ido dan irin yanda gabansa ya yanke ta fadi ya kali BS ba tare da ya yi masa tambaya ba, yana jiran karin bayani BS ya ce" mun nemeta bata nan, wannan batan ba irin wanda ta saba ficewa bane domin ba kayanta a dakinta Wata irin mikewa Abdul ya yi tsaye, lokaci guda kuma ya dafe kujerar dake kusa da shi domin wani irin jiri ne ya ji ya zo ya rufe idannuwansa, Da wani irin ihu ya ce" ina take? Ina ta shiga? A hankali kuma ya shiga rage muryarsa yana magana tamkar wanda ya zauce cewa" sai da na hana ki, sai da na hana ki, kin gano ne? Kin gono ko waye? Kin gano an ganki kafin ki fada ne? Ina kike? Kina ina? Ki zo gare ni?????