← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 94

Sashe 13

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

din suke jira, dan haka tana zuwa ta zauna , duda jikinta du a tsatsamce saboda bata saba fitowa daga ita sai tawul ba, Kayanta aka mika mata da bras, Kallonta ta yi ta ce " bana anfani da bras, Matar ta ce" zaki fara anfani da ita daga yanzu, domin gudu za.a fara daga yanzu, idan kina gudu ba bras nononki zai zube ne, mu kuwa du wani abinda zai kawo mana cikas bama so, Ita dai da ido take binta, nan aka busar da gashinta aka daura mata ribom baki dan siriri sannan aka daure gashin da kyau yanda ba zai hanata komai ba, Wasu mayuka biyu suka bata, dayan suka ce da ita na fatar jikinta ne, dan gyaran fatar jikinta, dayan kuwa ta ringa shafa shi a tafin hannayenta, gwuiwar hannayenta da na kafafuwanta, da kuma tafin kafafuwanta dalin tausi da suka yi, kafafuwan harda dan ysatsagewa suka yi wato faso, Karba ta yi tana dubawa Kallonta ta yo ta ce" ba wannan zaki yi ba, tashi ki saka kayanki maza ki bi inda kika ga yan matan nan na bi, Mikewa ta yi ta saka kayan harda audugarta yar karama wace kamarma baka saka ba dan baka jinta a jikinka, ta saka kayan ta nufi inda ta ga yan matan na bi suna fita bayan ta daura takalmi kafa ciki na gudu kamfanin Gucci Sai da gabanta ya fadi da ta ga wanda ke tsaye ya hade girar sama da ta kasa, Wannan datijon ne, da wani a gefensa shima bakin ne kamarsa shima ya hade fuska tamkar an zage shi, Kanta take sadawa wai kar ya ganeta inda ta je ta ja layi wajen da suka tsatsaya su wajen goma yan mata cikinsu ba ta yardawa, kowace yar dagwas da ita , gashi basuda wani jiki mai girma, sai dai wata ta fi wata tsayi sosai Fuska tamke yaron ya shigo gabansu ya fara magana kamar haka inda kolon kansa ba gashi ko dis , murya hade ya ce"..... *Domin samun Kutkale naira dari biyu ne, yan niger kuwa 500franc ta Orang Money* *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 1 Shiru ta dan yi tana kallon yanda ya tsurawa bakinta ido, Ta ci gaba da fadin" babu kalar abincin da baka ci, du irin arzikinka kana iya cin du abinda ka samu, Baka da dar da kwonciya a duk inda ya kama , irin gado, katifa, tabarma, dandar kasa, Baka da damuwar irin suturar da zaka saka a duk halin sakawar ya kama, Idannuwanta ta lumshe, jin irin yanda sukai mata nauyi, ta bude ta dube shi ta hada babar yatsarta da ta tsakiya ta ri tap tap biyi da su ta ce" kadan, Kadan ya rage min na baka labarin rayuwarka Sire! Abdul Jabar ya lumshe idannuwansa ya dan ja baya ya jinginar da bayansa jikin kujerar da yake kai still idannuwansa a lumshe, Yana matukar girmama kwazon yarinyar, Tana auna abubuwa, tana da zurfafa bincike kan abinda ke gabanta, A haka suka karaso tafkeken ma.aikatar da suka fito dominta, Fita ya yi a lokacin da ya hangi mutumen na tsaye, wato shi yake jira, Su BS fitowa suka yi suna ta aikin duba wajen, inda ya yi gaba Hafsat ta bi bayansa, Maimakun su shiga cikin ma.aikatar sai suka ja suka tsaya gaban mutumen, Kalon kallo sukaiwa juna shi da Abdul, Kafin mutumen ya bude hannayensa yana dariya irinta ka ga abin farin ciki kafin ya ce" yarona, zo gare ni, Abdul sai da ya dane zuciyarsa ya nufe shi ya shige jikinsa duda katon tumbinsa bai bari sun yi gaisuwar yanda ya dace ba, nan sukai gaisuwar larabawa kafi su saki juna, Mutumen ya ce" ai tunda kace da ni gaka nan tafe na kasa zama sai da na fito tarbanka yarona, Mu je office din mana Abdul ya gyada kai yana murmushin yake kafin ya ce" aa, ba sai mun shiga ba ai elhaj, nan ma ya isa, Dubansa ya yi, eh tabas du yawanci da Elhaj ake kiransa, kai harma matansa, sai dai kuma a yau Shi Abdul da ya fadi kalmar sai ya ga kamar da nufin wulakanci ya fada ko da niyar zagi, domin dai *bako* shi ake kira da Elhaj a saudiya, a dan yana kiransa dad, ne ko yace da shi Uba, ko dan tsakaninsa da mahaifinsa, aman a yau ya kire shi *Elhaj*, Murmushin yake ya saki ya ce" aman ya kana mai guri, ka zo kuma ka tsaya a kofa? Abdulma ya sakar masa murmushin ya ce" ka san, bawa na iya malakar guri, sai dai ya zamo masa fage....wato fili, Yaya maganar kayan nan, an saka su du inda ya dace? Elhaj ya gyada kai tare da bashi gamsashiyar amsa, Abdul ya mika masa hannu da niyar yi masa salama, Har sun juya sun fara tafiya ya juyo ya ce" *ni ina mutuniyar, Baby kennan sarkin son dadi, koda yake, dadin ce* Wata dariyar Elhajin ya saki yana sosai keyarsa har Abdul ya shige motar suka zo suka tashi motar Elhaj na tsaye suka bar wajen, Hankici ya ciro ya goge zufar dake goshinsa, kafin ya danna kira a wayar dake hannunsa, Ana dagawa ya ce" bafa zan iya wannan lamari da yaron nan ba, kamarma ya san me ya shiga tsakanina da baby ka ji maganar da ya fada min? Shiru dai ba amsa kamarma an kashe kiran, Sauraronsa da yake ya saka shi yin tsitt, sai dai maganar da Hafsat ta fada ya saka shi saurin kallonta, A nitse ta ce" in dai munafukan ne, ba zasu yarda su ja maganar a waya ba Sire, Da sauri ya dube ta, abin kunnenta ta nuna masa, Kan uba, yaushe ta lika masa abin sauraro, wato shi ya yarda ya shige jikinsa ya laka masa abin sauraro ta haka, ita kuwa ta saka masa a lokacin da ya cika shi ymta matso tana yin kamar tana kakabe masa jikinsa, Murmushi ya sakar mata, jin wani irin birge shi da ta yi, yana son ya ga mutumen da ya san ciwon kansa walahi, hakan na masa dadi sosai a rai, Wani irin attention dinsa yarinyar nan ke kara ja du haduwarsa da ita daga jiya zuwa yau, Yana kallonta tana kallonsa har aka kai shi wajen da zai sha caputulo, Fita ta yi ta saka aka ajiye masa saman table bayan ta yarda da hakan ta kimtsa wajen shan ta fada BS ya fada masa suka fito suka shiga wajen, Zama ya yi ya dauki jarida ya shiga karantawa, hakan ya bata damar karasawa kusa da BS suna dan dube duben yannayin wajen da mutanen dake dan shawagi a wajen, A hankali ya ce" kar ki mance karkashinsa kike, kar ki manta uban gidanki ne a yanzu, yana da damar yi maki tsawa, wulakanta ki, ya taka ki, du abinda yake so, ke kuwa dole ki yi hakuri, Bana son abinda zai jaza maki matsala a wannan mission din, bana son dalilin haka a taba lafiarki ko kudin da za.a biya ki, fatan kin fahimta, Sai da ta dan waiwaya ta hango shi, ya kare fuskarsa dai da jaridar hannunsa yanda suka bar shi haka yake ta juyo wajen BS ta ce" damuwarka kennan? Ni damuwana na yi na gama na samu liberty din fita kamar kowa, Idan har kika bata mission din nan kin san da baya za.a maida ke, jiya me ya hada ki da shi ya fito nemanki haka? Kar ki yarda kuma ya yaudare ki, domin kin san aiki ya hada ku, daga shi babu wani, koda ya yaudare ki toh ya kare da ke ne, Tsai ta yi tana dubansa, shifa du wani waje ya nufa, shi fa tarin kishi ke dawainiya da shi,, dan haka ta girgiza kai ta kuma duban cikin cafetaria din dan gannin ko ya fara shan caputulon? Sai dai abinda ya bata mamaki, irin zaman nan dai da yannayin rike jaridar da ya yi tun na farko bai gyara ba, bai canza ba, A hankali ta matso ta kurawa hannayen ido, ba damar gannin kafafuwan domin table din rufafe ne kuma mai girma, Hannun ta kara kurawa ido kafin gabanta ya fadi, Da gudu ta nufi cikin ta shiga da sauri ta karasa ta warce jaridar dake hannun wanda ke zaune a wajen da ya dace ace Sire Abdul ne ke wajen, Gabanta ne ya fadi wannin wani dan kyakyawan saurayin da ba shi ba zuru sai zarar ido yake, Irin juyowar da ta yi ta dubi BS ne ya saka shi zaro ido domin ya fahimci me hakan ke nufi, Da sauri ya bude yar karamar computer ya danna abin localization dan samun inda yake dan kuwa jikin rigarsa suka laka masa abin, Sai dai abin haushin yana karasowa inda ta dora kafa daya tana bin saurayin da kallon takaici ta dago ta dube shi ta ce" mutumen da ya iya guduwa a irin tsare shin nan da muke, idan har ya yi gigin bari mu gane inda yake ta hanyar barin abin localization a jikinsa ai da ya zama lusari, Rigar ya yiwa wannan saurayin kyautarta da sharadin ya zauna ya kame da jaridar nan na wasu yan lokuta, Shi kuwa da yake banza ne ya zaunan kuwa! Ta karashe tana mai dukan table din da karfi yannayinta na nuna tsantsar bacin rai na rainin hankalin da Abdul ya yi masu, BS
Chapter 13 · 0% Book details