← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 94

Sashe 4

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi ya yi mata maganar ba ya yi mata wani mahaukacin riko, da wani irin karfin da a yannayin maganarsa ba zaka taba sakowa ranka shi din nan Allah ya hore masa wannan karfin ba, duba da yannayin hutu dake sakashi magana a yangance da kuma sanyi, wai kuma yannayin rikon bai nuna alamar ya saka wani karfin a zo a gani bane Bras din dake jikinta ya bale sai dai me ciko ne ya fado, Ashe tudun nan na sama da ya saka saman cika ya batse gaba daya ciko ne ta yi daga kasan ta turo saman, A hankali ya sasauta mata rikon, harma ya saketa baki daya, Cikin salon karuwanci ta nemi komawa jikinsa tana wani laudi ita ga zata jashi koda ya ga sirrin cikonta, Riketa ya yi ya zaunar da ita suna kallon juna ya ce" ke musulma ce?? Tana kane ido daya tana turo yan berayan kirjinta ta girgiza masa kai , amsar eh ita musulma ce, Habarsa ya talabe da hannayensa ya ce" yanzu karuwancinma ba zaki yi da gaskiya ba? Ai musulmi an sanshi da gaskiya ko? Ya zaki cika taunman pant a nono ki ja ra.ayin maza? Haba cutar ai ta yi yawa, kina tunanin idan kasanki nake so zan zauna kina min rawa ne? Ni bana zina....aman ina son mata, Mata ababaden so ne, Kin san me idan na ga mace wace ta amsa sunnanta nan da nan wannan take mikewa, idan kuwa muna mata ne lafewa take kara yi ta yi kwonciyarta, Mata duka suna da kyau, sai dai wace ta iya gyara ta fi kowace kyau, Kin ga bariki ta shaida ki, ji yanda nononki ya dawo dan Allah in dai ba dan da kika haifa ba ya sha dan kar ya mutu ubanwa zai sha wannan yangom din? Shiru ya yi yana duban irin yanda ta saki baki tana dubansa, Murmushi ya yi cikin sanyinsa ya ci gaba da fadin..... (Ku fa gane, ya fito a wani irin mutun marar sirin baki, sam sam bakinsa bashi da birki, magana zai saketa ne son ransa *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 2 Hasana ta ce" hala, menene tsakanin ki da wannan Elhaj? Hafsat kuwa tamkar mai koyon gane yaren Hasanat ta tsurawa lebenta ido tana kallon yanda yake motsawa tana fitar da harufa, tamkar da gaske tana fahimtar abinda take fada, ashe ita bata ma san me take cewa ba, Zagayeta ta yi ta nufi ciki tamkar ta kifa, Tana zuwa ta tarar an rufe dakin, bodyguard din nan sabo ya tsare kofar ya caka fuska, Shi kansa uban gidansu ne, dan haka ba zai yiwu Hafsat ta kawo masa wargi ko wani gatsali ba, kusa da kofar ta je ta tsaya ta tsura masa ido tana kallon sa Shima ita din ya kala, mamaki ne ya kama shi irin yanda ta tsura masa ido, dan haka da girarsa ya yi mata alamun tambayar lafia? Kanta ta sada ta kasa bashi amsa, Suna wajen nan wasa wasa har docter ya zo, Cikin wani irin sauri bodyguard din nan ya caje shi sannan ya bashi hanya ya shige, Abin ya baiwa docter tsoro, domin wannan jinnin da yake fitarwa ta hancinsa dole ya fitar da shi a hayacinsa, kuma a iya binciken da ya yi da abubuwan da ya dauko da aka fada masa cewa habo ne bai ga wani dalili ba, kuma ya bayar da du abinda ya dace a yi an yi dan ya tsaya aman ina, haka suka talaba shi suka yi ta bubuga goshin , shima dai sai ya yi kamar ya tsaya aman daga sun kwontar da shi sai ya dawo, gashi dai tamkar gawa dan ya fice a hayacinsa tuni Doctern ne cikin wani yannayi ya ce " sai fa mun je asibiti da shi, idan ba haka ba kuwa za.a iya rasa shi a kowani lokaci Cikin tashin Hankali Muhammad ya dube shi kafin ya yo gaba ya fito a sukwane ya nufi dakinsa Cikin hanzari ta mike ta bi bayansa sai dai nan ma an hana ta shiga sanadiyar sojojin dake wajen Me ya yi? Oho sai fitowa ya sake yi tamk ar ya tashi sama , fuskarsa jaga jaga da hawaye nan Hafsat ta tare shi tana tambayarsa jikin Abdul din Sai da ya dan dubeta, sannan ya girgiza mata kai ya rabata ya shige Hannayenta duka biyu ta dora saman kanta a fili ta furta" shikennan, sun cin maka Abdul, Hannunta mai ciwo ne ta ji kamar wani abin ya kara sukarta, dan haka ta dan ajiye shi a ranta tana tunanin harbin ne ke hadasa mata haka, aman a hankali sai ta dan juyo hannun dan dubawa Sai da gabanta ya fadi irin abinda ta gani, rubutu ne, da larabci a bayan hannun nata, Da sauri ta juya ta fada dakinta ta kunna wutar dakin ta je gaban madubi ta ja ta tsaya tana kallon hannun, A hankali ta karanta abinda aka rubutan kafin ta fasarce da kalmar hausa cewa *maganin ruwan zamzam da dabino ta hanyar da jinnin ya yawaita* Ta karanta ta maimaita ya fi a kirga kafin kamar a mafarki abinda mutumen da ya damki hannunta a wajen taron nan ya dawo mata, Tabas wannan mutun shi ne ya damki hannunta daidai wajen nan wanda ta gani rike da bindiga har ta yi ihun mutun da bindiga, Da sauri ta ruko idannuwanta domin kuwa ba zata manta ba da ya fadi haka sai da ya kure mata waje kafin ya furta mata sunnan *ABDUL* Baya baya ta yi dabas ta zauna a kasa, Tsoro da rudu ne suka shigeta a lokaci daya, Ta shiga rudanni tsakanin amsoshi biyu ta fanni biyu, To waye shi? Me zai saka shi ceton Abdul? Idan fa ba cetonsa bane zai yi aa karasa shi ne zai yi ta wannan hanyar? Aman kuma ruwan zamzam waraka ne, tsaftacen ruwa ne, zai cutar da bawa ne? Eh to ana iya hada shi da wani abin ya cutar din mana, To aman da dabino ne aka hada shin fa, dabinoma ai warakar ne, Yannayin mutumen bai bata kalar mai tausayi ba, Yannayinsa bai yi mata nuni da zai iya ceto ba, idannuwansa sun tsoratar da ita, irin rikon da ya yi mata ya tsoratar da ita, Tana nan zaune tana sakawa tana warwarewa har ta ji alamar kukan ambulance Mikewa ta yi cike da mamakin ambulance kuma? Ina kwakwaluwar BS zai bari a kai shi asibiti a ambulance? Idan fa an yi haka ne dan a tarbi motar a karasa shi?? Baya tsoron daga ambulance din wani mugun abin ya same shi?? Da sauri ta nufi hanyar fita ta fice a dakin ta tunkari dakin Abdul din Tana zuwa yanzun tsaye ta yi gaban Bodyguard din ta bashi bayannin ita ke kula da ci shan Abdul, ya dace ace tana kusa idan za.a saka masa karin ruwa da du wani abu, idan ya hanata shiga Abdul ya tashi zata kai karansa wajensa dan kuwa ya hanna mata yin aikinta yanda ya kamata Sai da ya yi mata kallon baki da wayo, sannan ya yiw BS magana da abinda Hafsat ta fada, Jimm BS ya yi na dan lokaci kafin ya ce" barta ta shigo Hanya ya kauce mata ta shiga ya bi bayanta da kallo yana mamakin to idan ta fadawa Abdul din sai me? Shi ya san kan aikinsu ne? Kuma yayama aka yi take kama sunnansa kai tsaye tace *ABDUL?* Tana shiga wajen BS ta zarce tana kallon yanda Abdul ke kwonce shame shame an cire masa rigar jikinsa daga shi sai wandon rigar , likita da Muhammad na kusa da kusa da shi Haka kawai ta ji zuciyarta ta karye, ya salam, mutun, mutun ba komai bane, mutun ba komai bane, yanzu Abdul ne lokaci kankani ya dawo haka? Mutun shi ya dauki kansa wata tsiya! Sai da ta yi da gaske ta hana idannuwanta zubar da hawaye, a haka ta karasa gaban BS dake tsaye ta dago da idannuwanta ta lunshesu sosai ta bada kalar tausayi da son ya saurareta ta ce" BS, ya zaka yarda a tafi asibiti da shi? BS ya tabe baki yana kawar da idannuwansa daga yannayin fuskarta fanma kar zuciyarsa ta karye ya ce" kin san dai a haka ba za.a iya tafia da shi asibiti a motarsa ba ko? Dole sai an jona masa abin taimakon da dole sai an saka shi a ambulance domin a ciki ne za.a iya samu! Hafsat ta kara matsawa kusa da shi sosai , ta rage karfin muryarta ta ce" mutumen da ya rike hannuna, dubi abinda ya rubuta min a bayan hannu, idanfa an saka masa poison ne sai wannan ne makarinsa? Wani duba ya yi mata kafin ya ce" ta ina aka kai gareshi? Marabinku da shi shigarsu cikin motar dan minister, jikin ku jikinsa fa, a iska aka saka? Idan a iska ne yaya aka yi mu bamu shaka ba? A abin sha aka bashi? Sannin kanki ne ko abinci bai yarda da shi ba , shi ke girkawa ya ci da kansa ko *abincin ki* bai yarda da shi ba! Da sauri ta dube shi, wai ko abincinta, dan me za tana wareta da su? Kanta ta kawar tana dubansa ta ce" wannan likitan, baban likita ne da ake takama da shi a garin nan, tun da na shigo ni banda kame kame
Chapter 4 · 0% Book details