← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 94

Sashe 82

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mu kanmu bamu san yau kwanan wancen ko na wannan bane da wace ka yi ra.ayi kake gayata! Kana zaune da mu muna tafiar da rayuwa tamkar rainon yahudu ko dan ka tsara ba zaka haihu ba bale ka gyara gidanka ko dan tarbiyar yayanka?? A hankali ya kai bakinsa kan nata, Rufe bakin nata ya yi ta hanyar shiga kissing dinta a hankali a hankali Sai da ya yi iya yi sannan ya dan saki bakin nata, muryarsa can kasa ya ce" ba zan kuma ba nace, ina son haihuwar yanzu, a min hakuri na daina, zan ta yi maku ciki kuna haife min du shekara...walahi ko hutu ba zan baku ba, Hafsat ina son yaya sosai fa, tsananin jin son yayan da ban haifa ba tukunnan ya saka ni tsoron kar a cutar min da su Tunaninka sai ta yaya Allah zai kama ka idan har baka tuba ba? Mu ba matayenka bane? Ohk kana tunanin ka kilace mu ka rufe mu a gida baka barinmu fita , baka barin maza zuwa inda muke ka tsiratar da mu kennan ko? Idan Allahn ya jarabeka da mu fa?? Idannuwansa ya kura mata ido, ji yake tamkar ya make bakinta kai lahaula wala kuwata illah billah Falyakul khairan auliyasmut! Ya fada muryarsa na kausasa.... Mikewa ya yi a hankali ya kamata ya tayar da ita tsaye, Hijab din auntynta ya saka mata ya kama hannunta Du irin yanda ta so ya saketa a gaban aunty kiyawa ya yi sai auntyn ce ke kakauda fuskarta irin tana jin kunya , haka sukai mata salama suka fice ita dai sai fa suka fita sannan ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana girmama eh lale tauri da tauri ne Suna fita Abduk ya tsayar da adaidaita sahu, Dan adaidaitan na tsayawa ya karewa motar adaidaitan kallo, kallon Hafsat ya yi yana murmushi ya ce" ita wannan ai kungurguma ce Hafsat dake wani shasha masa kamshi bata san lokacin da ta saki murmushi ba, sai kuma ta hade fuskar tana kallon dan adaidaitan dake jiran su shiga ya kaisu inda zai kai su Abdul ya dube shi ya ce"""" *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 6 Abdul ya dube shi ya ce" malan zaka dan saki wannan abin dan ya rufe mana iskar gari?? Mai adaidaitan ya juyo ya kali Abdul da kyau, bai ce da shi komai ba ya saki labulen adaidaitan sannan suka shiga suka zauna Ko a cikin adaidaitan yana ja ne hannun Abdul na rike da na Hafsat, suna tafe ne a hankali domin ya hana mai adaidaitan yin gudu da su A hankali yake murza yan yatsun nata, yana yi yana sauke ajiyar zuciya, Bai taba tunanin idan wai mace tace zata barshi na dukan rayuwa zai ji ciwon kai bama bale wai har ya firgice, sai gashi wuni daya tak da ta dan nuna tana fushi harma ta yi gaba abinta du ya fice a hayacinsa Hafs at kuwa dake jin irin yanda yake murza mata yan yatsunta bata iya hana shi ba, hasalima shiru ta yi tana sauraronsa, sai kuma a hankali ta ringa jin hankalinta na tashi, ba komai ke tada mata hankalin ba sai irin yanda Abdul ya biyota ya rungumeta a jikinsa, ta ji mugun dadin dadadan kalamansa, sai dai kaf cikin bayaninsa babu inda ke nuni da ya kamu da soyayarta, ita tama fi fahimtar yana girmama wajen hutunsa ne Daidai adaidaita sahun ya tsaya kofar tamkamemen gidansu Abdul ya fito daga ciki sannan ya fitar da Hafsat a hankali Masu tsaron kofar da suka zaburo da korar mai adaidaita daga kofar gidan ogansu ne suka yi azamar zuwa dan salamar mai adaidaitan a lokacin da suka fahimci ai ogan nasu ne a adaidaita Shi dai murtuke fuska ya yi ya kama jan hannun Hafsat suka shige cikin gidan Tafia mai tsayin gaske suka yi dan sosai akoy tsayi tsakanin kofar shigowa da kuma bangaren Hafsat din, sannan a tsakannin tafiar sun hadu da ma.aikaran gidan jefi jefi, su kuwa gannin Abdul din ne da kansa suke tsayawa su mika gaisuwarsu cike da girmamawa, sannan su bi su da kallo har sai sun fice a gabansu Suna shiga bangaren Hafsat Abdul ya saki hannunta ya karasa tsakiyar fallon ya zauna ya dafe kansa da hannayensa bibiyu Tsayuwa Hafsat ta yi daga dan nesa da shi tana kallonsa, a ranta kuwa tambayar kanta take meye kuma?? A hankali ya dago da dubansa ya sauke saman fuskarta , idannuwansa ya lumshe sakamakon jin yanda zuciyarsa ta buga, Hijab na yiwa Hafsat kyau fiye da tunanin mai karatu. Hannunsa na dama ya dago ya mika mata, yana nufin ta zo gareshi Sai da ra kalli hannun da kyau, sannan ta shiga takawa a hankali har ta karasa kusa da shi din A hankali ya zaunar da ita sosai daf da shi, sannan ya juya yana kallonta Bakinta ta tabe tana dan yamutsa fuskarta jin har yanzu ba wai daina ciwon cikin nata ya yi ba, yana yi yana lafawa ne A hankali Abdul ya ce" na shiga tashin hankali Hafsat, da kika ce kin tsane ni, Shiru ya yi na dan lokaci sannan ya kamo hannayenta yana murzawa a hankali yana massaging yana kallonta Hannun ta kalla, sannan ta kali fuskarsa da manyan idannuwansa suka kara girma suka yi mata wani irin nauyi a cikin nata idannuwan, A hankali ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa ya sanyayar da muryarsa ya ce" *tell me, da gaske kin tsane ni?* Zuciyarta ce ta ji ta buga mata lokaci daya, a haka kuma ta ji jikinta ya fara daukan dumi harma cikin tafukan hannayenta ta fara jin sunna fitar da zufa mai zafi Cire idannuwanta ta yi daga cikin nasa, a hankali take son ya sake mata hannu dan gaba daya ji ta ringa yi wani irin abu na shiga jikinta daga jikinsa Abdul ya ki ya saki hannun, saima kara kusanta kansa da ita da ya yi, Muryarsa ta nuna mugun raunin da yake ciki ya ce" dan Allah, idan na kasance mai laifi ki yi min nasiha ba ko guje ni ba Hafsat, baki san me na ji ba, baki san irin halin da na tainci kaina a ciki ba..... Hannun nata ya kai daidai kahon zuciyarsa ya kara tausasa muryarsa A hankali ya ce" kin ji , har yanzu dokawa take... Gabanta ne ya kara faduwa, wasu irin kwallah suka cika mata ido lokaci daya Hannun nasa ta kaiwa kallo da hannunta, tabas zuciyarsa ta canza salon bugu, tana bugawa da mugun sauri ba kamar da ba A hankali ta lumshe idannuwanta hawayen nan suka samu damar zubowa, Tana kallon fuskarsa irin yanda du ya matse mata waje sai kawai ta ringa jin ta kasa kwakwaran lumfashi idan ba da nasa na taimaka mata ba A hankali ta buda bakinta tamkar ba zata yi magana ba, sai kuma ta ce" bugun zuciyar yayi min kama da idan kana da bukatar mace Abdallah Idannuwanta ta lumshe tana kokarin dane mugun kukan dake tukota wanda bata san ko na meye ba ta yi ta kuma ce" wacece ni? Wa na fi ko halitata aka daukaka fiye da ta sauran? Abdul, dan Allah ka taimaka ka fada min dala dalan abinda ya faru aurena ya juya a wannan ranar Kallonta kawai yake, hankalinsa gaba daya ya dugunzuma ya tashi, kennan tana nufin bugawar zuciyarsa na nufin dan yana da bukatar mace ne ko? Sai kace wani bunsuru? Sannan bata bar maganar BS ba kennan? Kusancinsu da ya matse sosai ya dan sasauta ta hanyar dan ja baya kadan Hannunta ya sasautama rikon da ya yi mata, a hankali ya ce" Malan ya tura ni binciko masa waye shi kamar yanda adini ya tanada Na binciko, sai dai na boye masa hasalin waye shi din, ke din kanki ba zan iya fada maki ba dan ban kasance mai tona asirin bawa ba, sannan kowa na da tabo a rayuwarsa sai dai na wani ya girmi na wani Dan shiru ya yi, sannan ya ce" maganar auren ki, eh ya daina ne dan an bashi zabi, kuma ya zaba Wani shirun ya yi kafin ya fuskanceta da kyau ya ce" sai malan ya daura da ni Kallonsa kawai take, Bata iya cewa komai ba, Abdul ya karsa sakin hannayen nata ya kara sasauta muryarsa ya ce" na ga mata da yawa, na gan su a matsayin da suka diro duniya..... *sai dai na shigi biyu kacal* Eh ina da jarabar mace, sai dai ina da kyankyami! Idan min ga na raba shinfida da mace Hafsat ki tabata dan na fita hakinta na igiyar aurena dake kanta ne ko dan ina rayi... *wato ina son abinda ke cikin bujenta!* Yana gama fada ya mike ya juya ya shige can cikin dakinta ya barta nan zaune, cike da dana sannin tsokano zancen nan haka gashi ya yi tafiarsa bayan ya fada mata magana mai tsayea a rai da saka tunanin dole! Ita yake zuwarma dan fita hakinta na aure? Kennan ita ke gannin ita har mace ce ko? Yana zuwa ne dan ya fita hakinta na aure Gaba daya ji ta yi tamkar an lakada mata duka, sosai take ji zuciyarta na kuna na wani irin zafi! Dan me zai wulakanta ta ta hanyar kwatanta mata karara yana zuwar mata ne dan ya fita hakinta? Shi mai wata matar ko? Ciwon abin ya sakata
Chapter 82 · 0% Book details