Sashe 42
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ake fada a cikin gari? Wanda baki da yawa ke fadin irin hatsarinsa? Wani irin rike mutunci neza.a iya yi a wajen da ba mai hanawa ko mai sakawa? Mai karfi shi ke mulki, ga Uwata yarinya? Wace kake nufi a tsare mutuncin? Abdul ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yanda datijon ke jefo masa tambayoyi, a ransa ya ce" ku ji fa, shi da ya dace ya yi ta murna, aman da yake ya shafi Mamansa du ya rikice abinsa, dan Haka Abdul ya ce" ai ina ga a yi murna kawai tunda ta fito a raye, Jikin malan kam ya yi kalau da shi, a haka har Mama ta zo da kulolin abincin da aka dafa dan kuwa sun tarbi Abdul yanda ya kamata ya fado ranar aikinta ne, ita da kanta ta yi girkin ta hada komai ta shigo da zumbulelen hijabinta wanda ya rufe mata kafafuwanta ba.a ganninsu ko kadan sai fuskarta da hannunta Gaisawa suka yi da Abdul cikin mutunci kafin ta juya ta tafi bayan ta ajiye komai da komai bata tsaya zubawa ba dan kuwa malan da kansa yake zubawa baya so matansa su tsaya wajen da ya yi baki , sam baya son matansa su kasance a wajen da maza ke wajen, hankalinsa baya kwonciya da hakan.................................................................................... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 3 *KU YI HAKURI DA PAGE DIN YAU DAN ALLAH, KU MIN UZURI, INA CIKIN SHIRIN TAFIA NE, KU MIN UZURI , zan fanshi kaina in sha Allah ta hanyar sambado maku pages biyu zuwa gaba* A lokacin da ya fito, ya fita a gidan a matsayin kuku mai dafa abinci, Ta gaban hasanar kuwa ya bi ya fice, bata yi tunanin tun da ta zo bata ga wani mai dafa abinci ba, bata tsaya ta kula da kyau dan gannin ko waye ba, bata ga shigarsa dakinsa ba , aman ta zura ido ya fice ta gabanta da plat din abincin da ya dafawa kansa ya fice a falon Hanyar baya ya sanda, wace ya kwashi minti talatin yana gadinsu har sai da sallah ta tayar da su ya fice a gidan A lokacin da ya zo bakin gari tuni kusan karfe shida na yama ne, ba wani haske sosai sai na Allah, wato wata dan kuwa idan ka yanki cikin gari duhu ne sai fitilun da aka kukuna a gidajen mutane Mashin din ya karewa kallo, sannan ya duba yar karamar wayarsa wace BS ke kiransa , ya samu numbersa ya privet ce a jiya da suka nemi Hafsat, Tsaki ya ja, ya rasa ko ya gane baya nan ne ko me? Yana ta kiran wayar dai dan haka sai ya kasheta ya saka aljihunsa ya haye mashin din Tuki yake na garari, wani irin gudu yake yana duba JPS din dake hannunsa sannan yana duba agogo ya mika hannunsa ya laluba yar karamar bindigarsa da ya sakawa abin hana a ji karan harbi ya mayar da hannun ya ci gaba da gudu tamkar zai tashi sama Kai da ba dan muguwar wutar dake cin zuciyarsa ba da ya juya da wannan tafiar mai mahaukacin wahala dan kuwa wani rami da ya afka sai da mashin din ya yi cili da shi, Allah ya taimake shi kwakwaljewa ne kawai ya yi, haka ya mike ya tayar da mashin din ya kuma daukan hanya A lokacin da GPS din ke nuna masa cewar ya zo wajen, a lokacin ya kashe babur din ya nemi waje ya ajiye shi da adu.ar Allah ya sa ya tardo shi, dan kuwa jejin nan ba za.a rasa barayi ba A hankali yake tafe yana sandar wajen bakinsa dauke da adu.a, hannunsa kuwa dauke da yar karamar fitila ta haskawa mai duhun haske, Wajen shiru, shiru ne gaba daya wajen a haka yake kara shiga cikin jejin yana mai baza kunne yana sauraron du wani motsi Motsin da ya ji a bayansa ne ya saka shi dukewa cikin ciyayin dake wajen ya tsurawa wajen da ya ji motsin bayan ya dane hasken fitilar A hankali mitsin ke kara matsowa kusansa, har ya kasance an matso sosai kusan shi Ido ne ya zaro a lokacin da ya ga mai motsin, Kai, me? Mikewa ya yi da sauri ya fito ya karaso wajenta, wada itama motsin da ta ji ya sakata aniyar labewa Hannunta ya damko ya juyo da ita da karfi , hakan ya sakata zazaro ido tare da jan a.uziya ta kurawa wanda ya damki hannunta ido da taimakon hasken watan da ya raba tsakiya ya haske wajen tar, mutun mai sanye da wani gajetan wando da riga marar hannun kirki da hular kuku, sai dai kuma fuskar Abdul ne, Gabanta ne ya fadi a lokacin da ya ce" ke, baki da hankali ne? Me ya kuma fitar da ke a wannan tsohon daren? Bayana kika biyo dama? Ke bakya gudun wannan jejin? Wai wa ya saka ki a sha.anin rayuwata ne da kike daukan irin wannan garajen? Ajiyar zuciya ta sauke, dan kuwa ta yarda ba aljani nane ya yi kama da shi, shi din dai ne, kennan da ya fito nan ya yo? Au , kennan ya dilmiyar da ita ne? Haba gaske a lokacin da ta so bara masa dakin ya yi gagawar dawo da ita? Ikon Allah zuwa ya yi kennan ya kashe mutumen ko me? Wani haushinsa ne ta ji lokaci guda, shi kennan baya jin bari? Ba zai daina wannan banzan kudurin ba? Hannunta ta yarfe wanda ya rike mata ta ce" ni ba kai na biyo ba malan, tafiata daban, kuma kar ka kuma rike min hannu, a kan aikina nake Wani takaicinta ne shima ya ji ya rufe shi, wai aikinta, to ubanwa ya dauketa aiki irin wannan? Haba sai yanzu ya gane kiran da BS ke masa, wato dan ya fada masa ne ta kara fita ko? Lale yanzu ya yarda da irin taurin kanta, yanzu ya yarda lamarinta sai ita, idan ba kasada ba , mace, ita daya kwal da ranta, ta tashi ta wani dadame da wani shegen wando ta daure gaban goshinta da wani dan siririn gyale ta dunkule gashinta ta shigl jejo yamkar zaTa yi farauta? Tsaki ya ja a fili ya ce" to sai ki kama hanya ki koma inda kika fito Hafsat ta dube shi da kyau ta ce" mu juya dai Ke ni sa.an ki ne wai? Ya ina baki umarni kina kokarin takewa who are u? Umarni na baki ki juya ki koma gida Hafsat ma ta yi tsaye gabansa, ya kasance suna facing din juna ta ce" idan muka yi fita ta ni da kai, na zama a karkashin, ina matsayin malakar ikonka, a yanzu ka bar uwar malan a daki tana baci! Takaici ne ya saka shi dafe goshinsa ya nufi Hafsat da niyar nuna mata ya fita iya tsayaya, sai dai wata murya ce ta ce da shi" *kul Abdallah* dukan mace kuma ka koma? Wani irin tsayawa ya yi, lokaci guda gabansa ya fadi, Da wani irin sauri ya juyo dan gannin wanda ya yi maganar, Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Tsaye mutumen yake, ya ja rawanin da ya yiwa kansa ya sauka hakan ya bada damar gannin fuskarsa dake dauke da gemu da saje mai tsayi tamkar tun da ya fara fitar da gemu bai taba askewa ko ya gyara fuska ba Du irin karancin hasken wajen ba zai taba bace masa ba, du irin yanda ya fito a gabansa ba zai bace masa ba, Gaba daya jikinsa ne ya kwashi rawa, da sauri ya saka hannunsa jikin wandonsa ya janyo bindigarsa da niyar karasawa wajen mutumen dake tsaye kikam ya ki motsawa ko ya gudu kamar yanda ya yi wamcen karron Da wani irin gudu ta sha gabansa, ta yi tsaye a gabansa sannan ta nuna masa bindigar dake hannunta gaban goshinsa, cikin karaji ta ce" *walahil azim kafin ka yi harbi zan harbeka Abdul Jabar!* Sai da ya fan dakata yana kallonta sannan ya yi wani murmushin gefen kunci ya ce" *a kan wannan kudurina kashe ki ba wani abu bane, idan har kin yarda kar ki kauce ki ban hanya!* Gadan gadan Abdul ya nufo Hafsat dake tsaye tsakaninsa da wannan mutumen dake tsaye shima ya harde hannayensa Yana zuwa ya danna alburushin bindigarsa ya........ *Ya Allah, shin wa Abdul ya gani haka? Kar kuyi gagawar yanke hukunci fa? Kar ku manta Abdul na tsakiyar makiya kala daban daban,* *Ya Allah Shin Abdul harbe Hafsat din ya yi?* Ina muka dosa ne? *KUTKALE.....KUTKALE...KUTKALE* *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 3 Wani