Sashe 87
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da son kansa da yawa? Take tambayar kanta da kanta, Tafia? Bai tashi tafiar ba sai da ranar girkina ta zagayo bayan ya kwana biyu cirrr yana min fushin da ban san laifin da na aikata ba? Abdul, ni ko? Ni? Tamkar wata sabon kamu ta girgiza kanta ta ce" a kanka malan ya taba daga hannunsa a kaina, kai kake min laifin dan ka tsane ni kuma ka fi ni zuciya? Da wace kake so din ce ai da baka yi mata laifi ba! Kukanta ta ci na arziki kafin ta shiga shashaka a hankali tana rage karfin kukan Sai kuma ta kankame jikinta a hankali ta ce" me ya ji maka ciwo Abdellah? Hannunka da ciwo wa ya taba min kai????? i.m back *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 6 Wasa wasa haka ta yi ta juyi, sai barci barawo ne ya yi awon gaba da ita a irin wannan halin, A washe gari Abdul na daukan wayarsa ya duba call din da ya yi missing Bai bi ta kai ba dan da wuya su samu abinda suke so, domin aiki ne ake nemansa ya gabatar a kasar maroco, binciken sirri na wani ahli da daga an haifi jariri a gidan sai a wayi gari a nemesa sama ko kasa, gasu da samari sai aute suke suna hayayafa mace daga wata ta barsuma wata zama take ko dan dukiyarsu, Shi ne baban dan gidan ya nemi da a bashi kwararen malamin sirri, dan sam bai yarda da cikin gidansu ba, hakan ya saka kasar da ta hore shi nemansa dan ta tura shi gidan a matsayin dan aikin giran har ya gabatar da bincikensa Laptop dinsa ya kuma kunnawa, Message din amail dake nuno masa ya danna Ba wani hayaniya akai masa ba sai amsa da aka bashi kamar haka *da zata dawo min, ko cikin ramin ginnin rijiya take sai na je na zauna da ita* Ajiyar zuciya kawai ya sauke dan ya fahimci wada mahaifinsa ke nufi, wato matarsa mahaifiyarsa Rufe komai ya yi ya fice ya tafi cikin gari dan karasa abubuwan da suka kawo shi garin Sosai ya wuni yana zirga zirga da kansa, sai da ya tabata ya ga wajen da ya dace da shi sannan ya karbi number mai wajen ya fice hotel din A lokacin tuni wani daren ya kara zagayowa dan haka sai kawai ya nemi waje ya yi ibadarsa sannan ya nemi kwonciya Ko yau hakan take a bangarensa, domin ya kasance mai tunani a kanta, daren ya yi masa tsayi ga gajiya, ya matukar wahala wanda tun karfe shida bayan ya gama sallar asuba da adu.o.insa ya dauki hanyar garin shugaban kasa , a cen take, ya yarda koda yanai mata fushi to fa yiwa kansa adalci shine zama a inda take, idan har ya yarda ya yi nesa da ita to fa ya tabata wannan shafa ruwa ne a alwallar dake gabansa dan haka ya baiwa kansa baki ya shiga murza sitiyarin motarsa ya dauku tafiar mai tsayi Zaune take da yarinyar da auntynta ta turo mata dan ta yi mata kunshin zamani, wanda da iya ja kawai ake zana shi ana na kafar dama an gama na hagu Katuwar wayar dake hannunta take dan jujuyawa, Idan bata mance ba yau kwanansa uku kennan da tafia, tun da ya tafi bai kirayeta ba bai nemeta ba, a ganninta ai ita ya yiwa laifi ko? Whatsupl dinta fa ya buda ta shiga , kan sunnansa ta shiga ta kirawa ido Nan ta ga rabonsa da whatsup din jiya wajen karfe goman dare Fita ta yi ta ajiye ta mikawa yarinyar hannunta na hagu ta shiga zana mata kunshin kadan ba mai yawa ba a hannun A lokacin da aka gama mata ta salami yarinyar sannan ta mike ta shige daki dan yin wanka Sosai ta gasa jikinta dan a yanzu hakan kawai take kafin ta samu ta ji dadin jikin nata Fitowarta daga wanka ta ji tsayuwar mota Da sauri ta mike ta je wajen windows din dakin jata ta dan leka Daga motar ya fito, yana fitowa ya yi tsaye ya daga hannayensa ya wara kafafiwansa ya yi wata irin mika daga inda yake yana salati a hankali Ido ta tsura masa tana kallonsa, wani irin farin ciki ne ta ji na ziyartarta lokaci daya, a hankali ta lumshe idannuwanta ta kuma budewa a kansa, Juyawa ya yi ya dauko jakar laptop dinsa ya maida kofar ya rufe sannan ya kuma juyowa a hankali ya shiga takawa Kamar daga sama ta ga Na.ima ta fito da gudu ta fada jikinsa Gabanta ne ya kwonci kwonci ya fadi , Rungumeta ya yi a jikinsa kafin ya dan dagata ya shiga juyi da ita a hankali Da sauri ta saki labulen ta yi gagawar fadawa saman bed dinta Zuciyarta ne ta ringa ji tamkar ta faso kirjinta ta fito, kamar da wasa sai ji ta yi hawaye na neman zubo mata Abdul kuwa na dan juyawa da Na.ima idannuwansa na kan kofar Hafsat Ya san ba zata taba fitowa a irin wannan lokacin ba, sai dai ya kasa kwadaituwa da son ganninta Duda magariba ta kawo kai gashi basa haduwa cin abincin dare, baya son kara rintsawa bai ganta ba Haka suka juya suka shige bangarensa da Na.ima wace ta maida hankali sosai ta kula da mijinta cikin nutsuwa, abinda da jarababe daman ya kunso lamarinsa suna shigewa daka shiru kake ji bai kuma fitowa ba sai da lokacin sallar asubahi ta yi Hafsat kam kuka ta kwana yi wanda ya matukar hadasa mata ciwon kai, gani take cin fuska ne, wulakanci ne , nuna mata ne zai yi ita ba kowa bace! Wajen karfe shiga ya dan buga kofar dakinta ita kuwa a lokacin ta shiga wanka bayan ta gama sallah Jin shiru ya saka shi zuwa bangarensa da kudurin daukan wayarsa ya yi kiranta haka kuma lokaci daya ya ringa jin gabansa na wani irin dokawa tamkar zuciyarsa zata fito ta balo ta bar jikinsa Da sauri ya shige ya zarce kuryar dakinsa, Na.ima dake zaune tana busar da gashin kanta ta yi gagawar juyowa tana kallonsa gannin kamar hankalinsa a tashe Da sauri ya zauna saman bed dinsa hannunsa har rawa rawa yake ya shiga danna kiran numberta Da sauri itama ta mike ta je kusa da shi ta zauna tana kallonsa, muryarta har rawa take ta ce" lallalafia? Me ke faruwa??? Abdallah dake kara danna kiran numberta aman ana ce masa wai a rufe ya kaleta da sauri ya ce" a a rufe numberta, bana samun numberta, kar dai a je ta kuma yi min fushi? Tun da na zo ban ji motsinta ba, Na.ima ina yar uwarki ta je?? Gabanta ne ya fadi, lokaci daya kuma ta hi zuciyarta ta yi mata bakinkirin Ba zata manta ba a jiya a lokacin da yake kokarin shigarta a hankali ya furta sunnan kishiyarta kafin ko ankara ne ya yi ko me sai kuma ya yi shiru Ita kennan du yanda zata nuna masa soyaya a banza ne? Kennan ba zata taba yin daraja a wajensa ba dan ta kasance wace ta fara nuna masa tana son sa? Ji yanda hankalinsa ya tashi bayan ta ji dawowarsa aman bata fito ta gaishe shi a maysayinsa na mijinta ba, sai shine zai fito a yanzu a haka?? A hankali ta shiga sauke kafafuwanta kafin ta mike ta kama hanyar fita Mikewa Abdul ya yo yana kallonta da mamaki, Me aka yi? Kukan me take? Dan ya tambayeta yar uwarta ne zata yi fushi ta wani fice? Shi kam wai dama haka auren mata biyun yake da saka ciwon kai? Daga wace ke yin halin ko in kula da shi sai wace ke son fitar da sabon halaya? Komawa ya yi ya zauna ransa na kuna Bai gama tunanin ba ya ga ta dawo dakin Yana kallonta ta zo har inda yake ta tsugunna gwuiwoyinta a kasa Fashewa ta yi da kuka bayan ta kamo hannayensa Tana kukan ta ce" dan Allah ka so ni, ka so ni Abdellah koda kwayar zara ne, dan Allah ka so ni, ka ga ni ba kudinka nake so ba, ba burina zama wata ba, Abdellah ni yar uwarka ce ta jini ko dan wannan na samu soyayarka ka ji?? Ta karashe tana kara fashewa da kuka tana dora kanta saman cinyarsa Wani irin tausayinta ne ya ji ya tsarga masa Fuskarta ya tsurawa ido yana kallonta, menene makusarta? Ita dai zuciya sakarai ce wace bata san ciwon kanta ba ko kadan, ita wace kake yiwa haukan ta nemeka ne? A hankali ya dakar mata murmushi yana kallonta ya ce" wa ya ce maki bana son ki Na.ima? Shin za.a iya hada shinfida ba.a son mutun? Kin kasance mai hakuri da ni da kuma daukan nauyina Tabas ina son ki Na.ima, ki daina saka damuwa a ranki haka kin ji? Wata irin ajiyar zuciya take saukewa a kai a kai, tana kuma kallon fuskarsa kafin ta mike da sauri tana dariya ta tsere Ajiyar zuciya shima ya sauke, a ransa kuwa ya yiwa kansa fadan cewa daga yau komai halin da zai shiga a kanta zai kiyaye nunawa a gaban yar uwarta Can wajen karfe biyu na rana suna zaune suna niyar fara cin abinci inda hankalinsa kacokam na kam kofar falonsa, tunaninsa da dukan abinda ya shafi zuciyarsa na hangen kofa, Yakan sauke