Sashe 83
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dage kafafuwanta a hankali ta dora saman doguwar kujerar sannan ta jinginar da kanta ta limshe idannuwanta tana jin yanda ranta ke kara daukaka abin Adu.a ta shiga yi tana kara lumshe idannuwan nata tana neman sauki wajen Allah. Ba shi ya fito ba sai bayan salar magarib, daga nesa ya tsaya yana kallonta, Sam baya gajiya da kallonta dan birge shi take a koda yaushe, sannan jikinta sai kara daukan haske da ma.ana yake A hankali ya taka ya buda dakin ya fice, buda dakin ya shaida mata da an fita Kofar ta tsurawa ido dan ko ya wuni a daki ba zata rasa kanshinsa ba A hankali ta mike ta nufi dakinta tana jin kanta tamkar wata marainiya, sam bata da sukuni bata da wani kwonciyar hankali sosai magangannunsa ke tsaye a ranta, sannan sharetan da yayima haka, fushi yake da ita ne? Ko menene? Wanka ta fara yi na kirki domin ta wuni ba wankan tun safe rabonta da ruwa, Tana fitowa ta shiga tsane gashin kanta , sannan ta saka turaran wuta ta rufa ya kama jikinta sosai Pad ta saka domin kadan kadan take zubar da jinni, wanda ke murda mata cikinta , ba karamin daurewa ne take yi ba Tana gamawa ta ciro doguwar rigarta na atamfa cikin kayanta ta saka , atamfar ja ce mai adon manyan shuka farare da baki baki Dan kwali ta daura saman kayan sannan ta balo ubiprophene ta hadiya dan ciwon marar A hankali ta taka ta fita ta shiga kicin dinta, madara ta kada da siga ta sha dan har jiri take ji na yinwar da ta hana kanta ci Tana nan zaune har ta ji kiran wayarta na ta zo cin abinci, dama shi take jira ko zata samu ta kwonta A hankali ta mike ta saka hijab dinta har kasa ta shiga ta kara feshe jikinta da turare sannan ta fito ta nufi bangarensa A hankali ta tura ta shiga, dariyar Na.ima ta fara jiyowa kasa kasa sannan ta ji muryarta tana magana cike da nishadi Ita dai bata yi kasa da gwuiwa ba ta yi salama sannan ta nufe su cikin nutsuwa Tana tafe ne tana jin zuciyarta zata tsinke, Kallon da ya saba taryota da shi bai wani kulata ba, ko daya bai kaleta ba kamar yanda ya saba tsura mata lumsasun shanyayun idannuwansa masu tafe da wani irin baiwa wa.inda ke sakata jin yanai mata susa a jiki tsabar yanda suke da tasiri a tare da ita , Tana kallonsa ko kiftawa babu har ta karasa wajen table din ta zauna Gaishe shi ta yi a hankali, ya amsa mata kamar wata bakuwarsa sannan ya ci gaba da kokarin zuba abincinsa Dago da dubanta ta yi ta kale shi, sai dai baima kaleta ba bale har ya gane yarenta A haka Na.ima da Abdul ke cin abincinsu cikin nutsuwa, inda Hafsat ke dan jujuya spoon din tana jin zuciyarta na tashi Basu jima suna yi ba suka gama, nan ya mike ya yi masu duba daya ya ce" ina son magana da ku Su duka da kallo suka bi shi har ya nufi fallonsa, hakan ya sa Na.ima mikewa ta bi bayansa Hafsatma mikewar ta yi jiki sanyaye ta bi su, suna zuwa suka zazauna saman kujera sannan kowace ta bada hankalinta kan mijinta mai aji! Abdul dake daura agogon hannunsa kampanin Gucci na farin azurfa ya yi gyaran murya kafin ya fara magana Magana ce yake cikin daurewa da cikakiken iko wanda gaba dayansu lokaci daya suka ji darr dar dinsa Hafsat kallon lebensa da fuskarsa take tamkar bakonta, bata taba ganninsa a yannayi na serius irin yau ba, hakan ya saka ta hangi girman darajarsa harma take tunanin irin su Abdul ne sanninsuma riba ne A hankali ta saci kallon Na.ima, gani ta yi ta bada hankalinta gaba daya da nutsuwarta tana sauraronsa, sai a lokacin ta ga eh tabas idanma Na.ima ta yi kishin mijinta ba laifi bane dan ya isa ya kai a yin, Ajiyar zuciya ta sauke tana jin tsare tsaren da ya canzawa gidansa, Ya raba masu kwana, sannan ya tsara tsarin zumunci, ya yi kwakwaran kashedi a gaba, haka kuma ya yi jan ido a fada, ya masu nuni da zaman aure suka zo ba wata wada zata fi yar uwarta a wajensa , idan kwanan mace ne ya soke mai zuwa gyra masa bangarensa da kula da cinsa da shan sa idan ba ita ba har ta fita aikinta, kys din bangarensa ya mikawa Na.ima kafin ya yi nuni da zata fara aiki a ranar, Daga karshe ya rufe maganar cikin sansanyar murya sannan ya mike ya fara bara masu wajen ya fita Wani tsadaden murmushi Na.ima ta saki sannan ta mike a hankali cikin shigar nan tata mai razana zuciya ta shige uwar dakan Abdul....danma ba abubuwan jujuyawa da sai ta jujuyasu son ranta, ita yau bata san me ke damun Abdul ba, ga0ba dayansa ya bata lokacinsa , wai Abdul ne harda bata labarin abin dariyarsu a saudiya? Ita dai tana son mijinta kuma batun kishiya kishiya ce idan har kishin take so su yi! A hankali Hafsat dake ji zuciyarta na tsintsinkewa na irin halin ko in kulan da Abdul ya nuna mata ta mike ta fita ta nufi bangarenta tana ji tamkar zata kife dan wahala Da kallo ya bi ta daga inda yake tsaye har ta shige bangarenta, Ajiyar zuciya ya sauke yana mai jin radadin irin yanda sam bata damu da damuwarsa ba, yana cikin yannayi na rokon kulawarta da kasanceewa tare da ita ta yi masa tambaya kan tsohon saurayinta, karshema ta yi masa nuni da idan dai mace ne kowace ya bi, bugun zuciyarsa da ya canza wanda har yanzu idan ya tina maganarta cewa ta tsane shi sai ya ji zuciyarsa ta buga , ta dora hakan kan jarabarsa ce ta motso...... Tabas yana girmama lamarinta a rayuwarsa, ta kasance mai dukan tunaninsa , tana dukan lamuransa , tana hana masa sukuni, tana saka shi jin muradinta a saman kirjinsa, tana motsa masa jinin jikinsa dama zuciyarsa har ya ji muguwar zufa ta wanke masa jikinsa.....sai dai hakan ba zai hana ya hukuntata ba, ! Juyawa ya yi ya shiga motarsa ya tayar ya fice a gidan, Tuki yake na iskanci a saman titin har ya iso kofar gidansa.... ina, ba zai iya rintsawa ba idan bai jijiga shi ya ci ubansa ba! Yau sai ya gane me ya fi shi ne? Yau sai ya bambance girman iskancinsa bilahi! *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 6 Sauka ya yi faga cikin motarsa ya je wajen mai gadi Salama ya yi masa a mutunce harma sukai musabaha kafin ya tambayr shi ko mai gifan na nan? Wato BS Gannin irin motar da ya fito, irin yannayinsa, da kuma zuwan mutuncin da ya yi masa bai tsaya wani tsaye tsaye ko tambaye tambaye ba ya budewa Abdul gida bayan ya tabatar masa da BS na gida yanama bayan gidansa wajen hutawarsa Sai da ya karewa yannayin gidan kallo kafin ya tabe bakinsa ya shiga nema hankali kwonce Da kyar ya gane yannayin gidan dan tamkar gidan barawo sai lunguna lunguna Hango shi ya yi zaune saman tapi mai fadi, gefensa budurwar nan ce da suka bashi tsaro tare , cikin shiga mafi muni sannan sun mayar da hankali kan begen juna a irin wannan yannayi Kansa ya gyada kafin ya yi murmushi ya karasa inda suke Bai yi masu salama ba, haka ya ya karasa infa suke, sosai ya matse masu waje ya yi masu kerere a ka a tsaye Da wani irin sauri suka zabura du suka mike suna kallonsa, Kallo daya ta yi masa ta gane shi, du kuwa da irin yanda ya gyaru ba uwar kasumbar nan, ba hadewar fuskar nan, du yannayinsa da sauki sosai, Murmushi ta yi ta daga hannunta ta sara masa tana kallonsa, bata damu da wanda take tare da shi ba ta kashe murya ta ce" sire ne da kanshi? Abdul ya zuba mata ido yana karantarta na dan kankannin lokaci, Murmushi ya yi kafin ya kada kai, Hannunsa na dama ya daga ya shafi gaban goshinsa, a fili ya ce" kai, bariki, bariki ba sana.a ba, idan kana son ka zama sakarai wanda bai san ciwon kansa ba sannan baya kishin kansa...to fa biyewa bariki, Kallon BS da ya hade rai ya yi kafin ya kara kallonta ya ce" ke yanzu tsakaninki da Allah da aikin ki, iyayenki da rai, kina musulma, ba laifi da dan kyanki sannan yannayin jikin ki wanni zai iya kwasa a haka dan shi abin ra.ayi ne, ki rasa abinda zaki yi a rayuwa sai bariki? Ke kuwa hau din bai miki adalci ba ki duba ki ga yanda kika make wata garjejiyar muryarki kina gaishe ni bayan da na shigo hannun wannan shegen a cikin rigarki yana laguda wannan shanyayun abubuwan tamkar slifas tsofi kuma nima kike kashe min wadinan tsofafin idannuwan naki so kike mu hadu mu uku ko me? BS dake kallonsa da mamaki, ga dumbin haushinsa na auren Hafsat da ya yi dan kawai ya ce ya zabi aikinsa a kanta baima tsaya ya ga daga baya idan bai auretan ba kamar can dama son ta yake, kamar mai jira ya aureta a ranar ya kale shi da kyau ya ce" *ABDULLLLL......* bai bar shi ya kai karshen maganarsa ba