Sashe 40
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zan so ka gyara idan har mahaifinka na raye ka gane ba kai ya dace ka hukunta shi ba, laifinsa da ya yiwa ubangijinsa ba ruwanka, fatana , baban fatana shi ne ace ba hannunsa a kisan kanwarka da kuma mahaifiyarka Hafsat hafsat farka fa Sisters, comment comment, comment plz *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 3 *DUNIYA, ABAR TSORO CE, KANA TAFE KANA YIWA KANKA MAKIYA A LOKACIN DA KAI KANKA BAKA SANI BA, FATAN RABIH YA SA MU GAMA DA DUNIYA LAFIA A wannan rana Sun wuni tare da Malan da Abdul, dan kuwa sallah kawai ke fitar da su, sun tatauna sosai, hankali malan ya kwonta ya kuma fada kan adu.ar Allah ya kubutar da ita, A haka suka yi masa salama da yama suka kama hanyar garin Minna Tun da ta ji motsin an shigo dakin ta yi tsai tana sauraro kamar yanda aka saba aka so aka bude wajen da zata ci abinci aka saka mata mesa aka dudura mata abincin da sam babu dadin dandano sannan aka barta aka rufe mata bakin aka fita Idannuwanta dake rufe cikin bakin kyale ta lunshe wasu irin hawaye suka bi tsuman suka jika, nan ta shiga buga hanci dan kuwa muguwar mura ke damunta na irin azabar da ake gana mata Mamake take, irin yanda ba.a fita da ita a mota ba an fai ja ta an yi tafia mai nisa da ita a lokacin da aka rufe mata idannuwanta da bakinta aka kuma daureta aka durfafi wajen da ba zata ce ko ina ne ba aka kawota aka daureta saman kujera ake gana mata azaba kala daban daban dan kuwa namiji daya ne ke azabatar da ita sai ta fadi inda ta saka wayar da ta hada da computernta take sharing du wasu informations dan kuwa wannan dalikin kawai ya hana a kawar da ita aman mirsisi ta ki fadi, du ta fice a hayacinta ta zama wata iri sai karbar azaba take ko abinci sau daya ake bata wani irin damun da bata san ko meye ba a bata ba wani da yawa ba shikennan sai kuma gobe, ta yi ta yi ta kwonce daurin da sukai mata aman ta kasa san ba komai a jikinta wanda zai saka ta iya kwoncewar, so take a mayar da ita azabar tsoma kanta a cikin ruwan da aka yi ko zata samu ta damki wani abin da zai bata damar kubuta Tarin tashin hankalinta shi ne Bayan masu son ran Abdul ma tare da shi, tayi imanin kuma *A CIKIN GIDANSA NE AKA DAURETA* dan kuwa ta ina za.a bi a fita da ita a irin mugun tsaron da gidan ke samu? Idan sun jirge camera ai ba zasu jirge sojoji da su BS ba, ba zai yiwu duda dare ne a fita da ita a kafa a yi nisa da ita ba, in dai an fitan da ita to fah ana kusa! Kai, irin girma da lungu lungu sako sakon gidan nan, ta fara tunanin ko dakin horon Abdul ne? Motsin da ta ji an buda dakin da wani irin karfi ya saka gabanta yankewa ya fadi Muryar da ta ji sama sama ana fadin magana kamar haka" *banzan sonta yake! Sonta yake, kuma ya iya fita da bada sau! Ka san irin yanda yake da mugun naci a kan abu, ina jin wannan yarinyar idan muka kasheta mun idasa tunzura shi! Damuwarta ya hana shi bin matan da wadincan sakarkarun suka hada shi da shi fa? Dan haka ka bude mani idonta idan har bata fada min a inda ta saka wayar nan na harbe banza a kai masa dakinsa a ajiye masa ya dawo daga inda ya je din ya tarar da gawarta mu ga abinda zai yi* ! Das das das das das shi ne abinda gaban Hafsat ke yi, Wani irin mugun tausayin Abdul, da tata rayuwar ne suka kamata, Shikenan, Shi ne abinda ta iya fadawa zuciyarta A hankali ta shiga neman taimakon Allah har ta ji an kama abin bakinta an vire shi da mugunta hakan ua sakata jin wani irin zafi Bata gama jin zafin ba aka cire abin da ya rufe idannuwanta Tar hasken wajen ya sakata saurin rufe idannuwanta dan wani irin dukanta abin ya yi a idannuwanta A hankali ta ringa buda idannuwanta tana gannin dishi dishi da kumburariyar fuskarta har ta idasa buda idannuwanta saman fuskarsa Ido cikin ido suke kallon junna, a hankali ta buda baki ta ce" *WHY? WHY? Kai ne wanda ya fi kowa kusanci da shi, kai ne wanda ya fi kowa sannin sirrin sa, kai ne wanda ke yi masa fada kan ya bar desir na vengeance ku juya gida, kai ne wanda a duk lokacin da aka kawo masa hari ka fi kowa rikicewa da shiga tashin hankali, aman ka san kai ne ka shaka masa abu da kanka a wajen auren yar gidan aminin mahaifinsa? Bashi da baban abokin shawara sama da kai, ka kasance mai yi masa fada a kan banzan burin daukan fansa da nacin zama a wajen da ake son gannin bayansa! ME YA AIKATA DA GIRMA DA KUMA ZAFI HAKA DA HAR KA ZABI ZAMA MAKUSANCINSA MAFI KUSANCI SANNAN MAKIYINSA MAFI GIRMA A DORON KASA? KA MIN ALFARMAR SANAR DA NI WANNAN DALILI NAKA KAFIN KA KASHE NI Gashin kansa ya shafa cike da dumbin mamakin yanda aka yi a kankanin lokaci, kwanakin da basu fi wata uku ba yarinyar karama ta shigo ta gane abubuwan da sauran mutanen basu gane ba, wato cewar banda bin bayan Abdul na son kashe shi da yake shi ne ya kashe mahaifiyarsa da hannunsa, ya kuma saka aka kashe kanwarsa? Kai wannan yarinyar dole a yau a yanzu ya kasheta dan kuwa yana gannin take takensa da dukan jama.ar dake tare da shi, a kowani lokaci suna iya gane wanda ke saka su a rudun rayuwa su kashe shi kafin shi ya kashe shi! Kafarsa ya dora daya saman abin kujerar yana kallonta ya ce" dalilinsa hukuncin sare kai ya hau budurwata wace tun da aka haifeta nake son ta tamkar raina, ina ji ina gani ta afka soyayarsa a lokacin da muka tasa dan ya fito a matsayin zakaran da ya zarce kowa ya ci aikin baban bodyguard na kasar *SAUDIYA* Mun kasance mun fi karfin a kiraye mu aminai , sai dai yan uwa Ni ke zuwa gidansu hutu a lokacin da ya je aikin da take takamar shi rikeken dan bincike da kuma gane mai laifi ne, Tabas na san dukan abubuwan dake faruwa tsakanin mahaifinsa da yar da ya haifa, na kuma san du wani shirye shiryen uban , Mahaifinsa ya dauke ni kamar yanda ya dauke shi, dan kuwa har shi kansa bai san ainahin waye ni ba , bai kuma san na yi alkawarin karar da danginsa ba! *Hasina* ta kasance mai son bakin namiji jarumi dan kuwa muguwar harija ce a tana kananun shekarunta ma na san da haka dan wani lokacin sai na taimaka mata nake samun lafiarta, Tun da ta yada ido ta ga Abdul, ta shiga tarda shi ni tana kewaye ni, Abin ya zama jaraba ta tsane ni tamkar ranta, shi kuwa ya tsane ta tamkar mutuwarsa! Takan tarda shi du inda ta san zai je, ya wulakanta ta ko a gaban waye ya taketa ya yi tafiarsa, Gana da kanai ciki akoy wace sak irin halayanta ne da ita dan kuwa itama nunawa ta yi tana son sa, A lokacin shi harkar mata bata gabansa, ni kuwa ina bibiyar kanwarsa jira kawai nake ya yarda ya so Hasina ni kuwa na bi kanwarsa dan kuwa cikin ma.aikatan gidan na samu mai bin mani du wani motsinta Ke bara na takaice maki, dan ya kori Hasina sai ya fara kula kanwarta a lokacin ya dawo ya zama cikeken sojan boye, yana shirye shiryen zuwa gida wajen iyayensa wani lokaci aka wayi gari Hasina ta Kashe kanwarta da hannunta , binciken da ya yi ya gano ita ce ya fakasata aka kawot tsakiyar gari aka gile kan Hasina ina tsaye ina kuka ina magiya ina kallo ya gurgura gangar jikinta ta fadi gefe Daga wannan ranar na zama makiyin Abdallah, ke ko raina zai shiga sai na ga Abdallah na kukan jini yana magiyar a yi hakuri a kashe shi dalilin bakin cikin rayuwar da yake gani kala daban daban kafin na kashe shi da hanuna Hafsat kyam shi take kallo, kafin ta ce" *tabas, mutuwarsa zata fi zuwan masa da sauki da jin mumunan labarin cewa kai MUHAMMAD kai ne bakin kumurcin dake bibiyar rayuwarsa cikin innuwa yana kasara shi, na baka albishir din a lokacin da zai san da hak, abinda zai hana zuciyarsa bugawa to fa lale baban abu ne mai girman sauran kwanakinsa a duniya, kuma tabas na yarda da maganar cewA......makashinka yana tare da kai, ko ba komai na gane cewa duniya sai Allah* Irin yanda take hawaye yake kallo kafin ya yi wata yar karamar dariya yana kallonta ya ce" na kasa gane shin son ki ne ya saka shi a wannan halin ko shakuwar ce da yake fada? Dan kuwa a yanzu ina cikin tsakiyar abu biyu, ban taba gannin ya yi rikicewar da ya yi sai da na dauke ki! Shi kashe ki zai idasa haukata shi ko kuwa cire maki kayan jikinki nake, na mayar da ke matata na