Sashe 90
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 6 Aman a fili sai ta ce" kar ka bani hakuri, baka yi min laifin komai ba Shiru ya yi yana sauke ajiyar zuciya cike da mamakin irin jan ajinta, ya tabata da wata ce da tuni ya samu amsar zata so shi ko aa, aman ita ta bar shi a duhu ya kasa gane gabas din maganarta tamkar tandun kwali. Basu su tashi a wajen ba sai da kiraye kirauen sallah ya fargar da su, Nan ya taimaka mata suka mike suka nufi dakinsa A keana biyun nan sun kasance cikin aminci, shakuwa, kulawa, madaukakiyar soyaya Hafsat cancara kwaliyarta take kafin ta koma bangarensa idan ya fita, Eh lale bai ji da bakinta ta furta masa kalmar so ba, aman yannayinta , ayyukanta a gare shi, irin yanda a yanzu take bashi hafin kai a bed, harma ta neme shi dan kanta wanda shi kansa yana mamakin dama harijar mace ce ita? Irin yanda idan yanai mata hira take bashi hankalinta baki daya harma ta dara na darawar, na jimami fuskarta ta nuna, komai na zaman lafia sai dai ya godewa Allah A haka har lokacin fitarta a aiki ya yi sukai wata irin rabuwa tamkar zata bar gari, tamkar ba zasu kuma haduwa ba dan kawai zasu raba kwana na kwana biyu kacal, hakan ya sakata hawaye da ta koma bangarenta sannan ta tashi da azumi domin a gaskiya ita ta san wannan lamari na bukatar mijinta dake damunta ya fice misali, sarai take cikin damuwar rashin mijinta, sai dai ta kwana da sanin ba na ita kadai bane dan haka sai ta gayato hakuri ta yafawa kanta ta tura masa sakon tana azumi danma kar su yi tsamaninta wajen kari da kuma cin abincin dare Sarai tausayinta da tausayin kansa ya kama shi, a hankali ya mike bayan ya salami Na.ima daga cin abincin safe ya nufi bangarenta kafin ya fita aiki Dakatawa ya yi daga bakin kofa tun da ya shigo yana kallonta, Tana yannayin mutun mai sanyi, tana yannayin damuwa A hankali ya karasa inda take kwonce Hannunsa ya dora saman mararta ba da nufin wani abu ba sai dai taurin da ya ji wajen ya yi ne ya saka shi sauke idannuwansa a kan fuskarta da sauri Itama jin ya tabata da kuma jin zafin dana mararta da ya yi ya sakata saurin zabura tana kallonsa Da yannayin damuwa yake kallonta, a hankali ya saka hannayensa ya janyota jikinsa, cikin nutsuwa ya ce" bab, me ke damun ki?? Murmushi ta kakalo tana kallonsa a hankali ta ce" ba komai, ina azumi ne Idannuwansa ya lumshe yana kallonta ya ce" me ya sa mararki take da tauri haka? Kallonsa take, ita kam bara san mararta na da tauri ba dan bata taba ganewa ba, takan ji dau marar tata ta yi mata nauyi sosai, sai dai sam bata taba jin taurinta ba Kallonta ta kawar daga fuskarsa a hankali ta ce" ban san tana da tauri ba Mikewa ya yi ya ce" kwonta na ga? Irin kwoncin da ya tarar da ita ta yi ta kuma yi tana kallonsa Tamkar wani likita ya kara yaye rigarta ya shiga dana cikin nata a hankali yana kallon yannayinta Rike hannun nasa ta yi tana yatsina fuskarta dan walahi ita zafi take ji sosai Daina danawar ya yi ya shiga shafawa a hankali yana kallonta ya ce" yaushe rabonki da al.ada? Hafsat ta amsa shi a cikin sanyin murya cewa" wannan watan ma na yi To me ke damun ki? Hafsat ta daga kafadarta Abdul kam ji ya yi hankalinsa ya kasa kwonciya, gashi tana jini da sai ya ce cikin ne bai fita ba, mai ke damunta? Agogo ya kalla ya ga takwas har ta yi dan haka sai kawai ya mikar da ita ya bata hijab dinta ya ce" saka mu.je asibiti Kallonsa take bayan ta saka din ta ce" aman ni ai lafiata kalau, bana jin wani ciwo fa Abdul ya gyada kansa ba tare da ya bata wata amsar ba ya kama hannunta ya jata a hankali suka fice Suna fita motarsa suka zarce Kys ya yiwa motar kafin su kama hanya Ita dai kawai kallon hanya take, bata san na me zai kaita asibiti haka ba ita lafiarta kalau Gabanta ne ya fadi na tunanin ko dai shima yana tsantsamin bata da lafiya ne sakamakon wannan yanayi Harhade fuskarta ta yi tana jin kamar ta dadage ta zunduma ihu ko zai mayar da ita gida tun kafin ya kaita a fadi wani abinda zata ji kunya A haka suka karasa cikin clinik din Wannan karon kin ya riko mata hannun ta yi ta dai bi bayansa har suka shige wajen gannin likitan matan Sun taki sa.a mace biyu ce kawai zaune dan haka suka zauna suma yana mai binta da kallo sai ta ga ya sakar mata murmushi aman kuma bai yi mata magana ba A haka har zuwansu ya zo suka mike suka shiga tare Tun da ya shiga ya ga wani jikeken namiji mai kalar fatarsa zaune yana aikin duba matan mutane gabansa ya fadi, ransa ya yi masa bakikirin , Bai aune ba sai gani ya yi har ta zauna a farar kujerar duba mararsa lafia ta bada hankalinta wajen likitan Sai da ya gama rububuce rubucensa ya dago ya zuba masu kallo, Fuska Abdallah ya yatsina yana kallonsa, a zuciyarsa kuwa fadi yake mumuna ne kai, sam baka da kyau Daga kafa ya yi da sauri ya karasa shima ya samu waje ya zauna sai muzurai yake Likitan da ya gama kallonsa ya ga bai bashi hannu a matsayin wanda ya tarar suka yi musabaha ba kuma dai a yannayinsa bai ga yannayin mai duhun kai ba sai shima ya ki bashi Sai da ya buda katon litafinsa sannan ya dube su ya yi masu tambayar waye ba lafiar? Yaya sunnansa? Shekarun haihuwarsa? Tana shirin yin magana ta ji Abdul ya ce" Hafsat , Madame Abdul Jabar, shekarunta ashirin da uku Kallonsa ta yi, inda shima likitan ya kaleta yana tunanin to ko kurma ce ita din?? Rubutawa ya yi sannan ya basu hankalinsa kacokam ya ce" menene damuwarta? Wace irin rashin lafia ke damunta? Abdul ya hadiye abin haushin da ya tsaya masa a makogwaro sannan cikin isa shima ya ce" mararta ke da tauri, tana daukan zafi, bayan as nrmal marar mutun bata haka Kansa ya gyada ya kara yi masu tambayoyin da ya dace kafin ya mike ya nuna mata bed din da zata kwonta kusa da wani allon haskawa wato wata yar karamar tv Irin kwonciyar da ta yi kanta sai da cikinsa ya juya, wannan a haka din idan ba shi zai haye ruwan cikinta ba gaskiya wani garjeje ba zai kale masa yannayi mace ba ehe! Bai gama fahimta ba sai da ya ga ya kai hannu zai yaye hijab din jikinta ya kai wajen mararta, waje mai daraja da daukaka a idannuwansa, waje mai tarin sirrinsa Hannunsa ya kai da sauri ya tare nasa hannun, Dago da idannuwansa dake cikin gilas ya yi sukai ido hudu, Abdul ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa yana kallonsa bai ce da shi komai ba Doctern ya saki murmushi kafin ya janye hannunsa a hankali ya juya ya fice a office din Hade fuska ya yi tamkar bai san meye daria ko fara.a ba inda Hafsat mamaki tamkar ya kasheta Kanta ta girgiza tana kokarin mikewa da niyar sai su tafi ai tunda likitan ya bara masu office din baki daya! Bata kai ga tashi ba sai ga likitan ya dawo tare da wata likitar mata Zuwa ta yi cikin fara.a suka gaisa ta gabatar da kanta ita din ma doctern mata ce Waje Abdallah ya matsa ya bata ya tsaya gefe kusa da kan Hafsat dake binsa da kallon ga irinta Shi dai ko a ransa saima maida hankalinsa a wani ruwa ruwan da likitar ta matso ta shafa a marar Hafsat din Dora abin ta yi ta shiga yawo da shi a hankali tana kallon allon wannan karamar tv din A hankali ta ce" haka ne doctern, gayanan dan jaririn foetus Da sauri Hafsat ta rintse idannuwanta tare da jin gabanta ya fadi, Foetus? Aman ai tana al.ada, kennan cikinta bai fice ba? Cikinta yana nan? Gabanta ne ya fadi cike da tsoron me mijin nata zai yi shi da baya wannan ra.ayi a yanzu? Sai dai yannayin da ya shiga a lokacin da likitar ta tsayar masa wajen da dan karamin halitar da ba.a gama ba aman ana iya gannin abin tamkar wani kadangare sai ya ji gaba daya jikinsa ya dauka Tsurawa abin ido ya yi, ba.a gama halitarsa ba, bai san kalar da zai bada ba, aman ya ji gaba daya jikinsa ya dauka da kaunar abin, Ji yayi dama kar ta daina haska masa, ji ya yi dama a janyo wata biyar din da suka rage ya taka duniya ya ganshi, Kaunar abin, wani irin yamyam ya ringa ji inda ya duka yana shafa wajen Cikin nata ya dan tada , sai dai ba zaka yi tunanin dan mutun bane a ciki sai dai ma ka yi tunanin nrmal haka cikinta yake Wata kwala ce ya ji ta tarar masa a cikin idannuwan nasa, a hankali ya karasa kusa da fuskarta ya duka sosai ya kama lebenta Idannuwansa ya lumshe ya tsotsi na kasan cikin wani irin sanyi sannaj ya saki yana kallonta A hankali ya ce" ina son ki Hafsat, plz ki so ni? Ki so ni tun kafin yarinyar mu ko yaron mu ya taka kasa? Hafsat zaki bani