Sashe 9
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ce idan an kawotama harbeta ne za.a yi, a niger babu Loi din harbe mutun koda ya yi kisa hakan ya saka suka sakata kaso daurin rai da rai, Tunda ta zo kason sai da ta san yanda ta yi ta zama shugaba, kowa tsoronta yake tamkar rai, basa haye mata, dan ta fada ta kara kashe wani ba damuwarta bane dama ta shigo ne da niyar a fitar da gawarta bata da matsala da hakan! Haka aka fitar da ita, aka nufi inda ake son gannin nata, nan ta bar su kowa jikinsa mace dan sun san yau ba su ba barci, za.a sha masifa ta bugu da kari! Turata ya yi dan dakin sannan ya ja ya tsaya yana muzurai, Daman ta san shi ne, bata san tambayoyin me yake mata ba, bata san me yake nufi da ita ba, Tana shiga ta kara kallon yannayinsa, a ranta ta ayana ban taba gannin fuska marar annuri irin taka ba, Shima dake zaune fuska hade ya mike ya dauki abin auna tsayin mutun ya auna tsayinta, Hannunsa ya daga a lokacin da take tsaye ya zabga mata wani wawan mari wanda ya sa ta daku da jikin bangon wajen, Da sauri ta taro kanta sannan ta mike tsaye tana dubansa ido cikin ido, Dakin take bi da kallo, ba komai ciki sai bindiga daya kwal dake ajiye saman table din da ya tashi daga sama, Da gudu ta nufi wajen bindigar ta dauka ta saita shi ta firfito da idannuwanta ta daga muryarta da kyau ta ce" kai mahaukaci! Me na maka? Me na maka? Uban me kake zuwa nema wajena? Ko jira kake kaima na daga maka jiki? Kan haka zan iya harbeka dan Walahi malan ba zai yi kukan na rasa mutuncina a waje ba! Koda kuwa gawata zama fitar daga wannan bakin gidan! Da sauri guard din dake waje ya shigo ya nufeta dan karbe bindigar, ai kuwa ta dana ta kara dana kunamar bindigar, sai dai ba alburushi a ciki, A haka ya karbe yana mai jin zuciyarsa na bugawa dan kuwa shima bai san ba alburushi a ciki ba, ya dauka ya gama mutuwa kennan, Datijo ne mutumen da ya gannin nata dan haka ya zagaya ya koma wajen zamansa, Wayarsa ya ciro ya canza harshe zuwa yaren french ya ce" na yarda da taurin zuciyarta, girman mutun, yannayin fuskarsa, ko karfin mulkinsa ba zai sakata yin dar ba idan ta hado su, tsayinta ya kai daidai a dauketa , bata da kakauran jikin da zai hanata daukan formation, zan saka rana a sakata cikin wa.inda aka dauka, Shiru ya yi yana gannin yanda take waiwayensa bayan an fitar da ita sannan ya ci gaba da fadin" tabas idan ta samu mugun horo, zata kara tsayuwa saman kafafuwanta, zamu dauketa mu bata horo na wata biyar, zata fito a matsayin *BODYGUARD SECRET* zamu bata horo kala daban daban, zamu bata horo na tausasa murya, zamu bata horo na kalolin yaudara, zamu bata horo na jure azaba komai girmanta, sannan zamu horata da yin biyaya, Shiru ya kuma yi inda ake masa bayanin an gamsu da kyanta? An gamsu da girman gayunta? An gamsu da girman iliminta? An tabatar tana jin yare biyar *HAUSA, FRENCH, TURANCI, LARABCI, DA ZABARMANCI?* murmushi ya yi ya ce sunnanta na gaskiya shi ne *HAFSAT MUHAMAD SA.IT*, yare tara take ji, gaba daya kwaya biyu ne na iyayenta, sayran ta koye su ruwa ruwa je a makaranta zama da masu iya yaren, yarinyar kamar computer take, tana dauke abu nan da nan ba tare da ta sha wahala ba, tun da ta shiga makaranta itace ta fari har zuwa faruwar kadararta, gasa ta school da islamiya sai dai idan ra.ayi ya hanata shiga, in dai ta shiga sai ta lashe, Tana da kakarfar zuciyar da na yi na.am da ita, Shekara ashirin kennan ina horon sojoji, polisai, guard, Body guards, ban taba tsayuwa gaban mutun mace ko namiji muka kali juna ido cikin ido ba tare da ya sada kansa ba sai wannan yarinyar, zuwan da nake dan duba yannayin mutanen kason dan zaban wanda zan dauka har na isheta yau ta nuna min bindiga danma bana ajiye bindiga da alburushi da ta dana ta harbe Guard dina, Haka suka gama magana kafin ya fito ya nufi motarsa inda suka sara masa aka ja shi aka fice da shi ....... Wannan kennan . Ku biyo ni ku sha labari.... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida 6 *Free page* *SALAM, ZAKU GA WASU ABUBUWA CIKIN WANNAN RUBUTU NAWA, KAMAWA TA YI, WANI ABIN YA ZAMA DOLE NA SAKA SHI, DAN HAKA KU BIYO NI Cikin dakakiyar murya ya ce" kafin ku shigo gidan nan kun yi gudu na kilometa 4 a minti talatin, to yau zaku yi 6 a minti ashirin, ba tserere bane, domin so muke ku zo gaba dayanku a tare, kar wani ya rigayi wani zuwa, kar kuma a bar wani a baya, akoy mai tambaya ne? Shiru du suka yi domin kuwa kida sunada tambayar ba zasu iya yinta a wannan mutumen marar annurin ba, taf idannuwansa kansu wasu jajajir ne kamar an watsa masa barkono, kai ko da hakoran bakinsa ya cikeja ya tada ka tsaye domin dogaye ne, dan haka du suka yi shiru suna tunanin abin, Kara maimaita tambayar ba mai magana ya yi? Tsagal ta ce" wani irin mu zo a tare? A tare zamu yi aiki ne? Ko akoy aikin da za.a iya tura mu tare da sharadin sai mun dawo a tare daya ta kula da ran daya? Datijon nan ne ya saki murmushi yana dubanta kafin ya gyada kansa, Sai a lokacin ya matso inda saurayin ya dan matsa masa gefe, Datijon ya dube su ya ce" ya zaku tsaya gaban mutun ya zayano maku maganganu kuna sauraronsa kuma kuna kallonsa, cikin hankalinku, ba maye kuka yi ba, ba duka kuka sha ba, bayan kun san abinda kuka zo yi , horon aikin zama Bodyguard wanda a kaf cikinku za.a dauki mutun uku zuwa hudu, sauran sai dai a yi wani wajen da su, bayan kun zana jarabawa an tabatar maku da abubuwa na wannan aiki, aiki ne na individual (mutun daya), shi ne za.a ce da ku wajen gudu ku karaso tare tamkar tayar mota da aka daidaita wajen hakan sai kawai ku hafiye? Murmushi ya yi irin na mugunta kafin ya dubi saurayin nan ya daga murya a hade ya ce" Bg soldier (Bodyguard soldat ), ka fitar da wace ta yi tambayar ma.ana gefe, sauran ka horar min da su ta hanyar yin tsalen kwado dari kafin su yi gudu, Haka ta ja gefe tana kallon yanda yake tsaye kansu da zabgegiyar bulala suna tsalan kwado suna karawa du wance ta yi da sanya ba wata wata yake dada mata bulala ciki harda wata mai dan kakauran jiki baiwar Allah yar baba da rai ce, ta samu shiga wajen da mahaifinta wani ne, dan haka baki dayansu suka jigata sosai , sannan aka laya su aka sake su gudun kilometer hudu, wanda ta jigata ta ji kamar zuciyarya zata tsaya, domin rabonta da wani gudu mai dan tsayima tun wanda ya kawota gidan yari, hakan ya sa sai da suka rigayeta isawa kafin ta karaso, aman bata yarda ta zauna ko ta fadi ba, jurewa ta yi a du kuwa da irin yanda take jinta zata kife kas ta ki bari sai da ta karasa, Ai kuwa da gudu take neman ruwa, nan ya dakatar da ita ya hana mata ruwan kafin ya firfito mata da micik micik din idannuwansa ya zazaro mata ya ce" du lokacin da kika yi gudu kar ki yarda ki sha ruwa daga kin tsaya, hakan na tsayar da zuciya, ki bari sai kin jima sannan ki sha ruwa! Kai kawai take gyadawa inda baki daya jikinta ya jike da ruwan zufa Basu gama mayar da numfashinsu ba aka nuna masu wajen da zasu shiga dan jim, (dakin motsa jiki), A cikin dakin ba abinda babu, sai dai su aka yi masu iyaka da duk wani abinda zai saka jikinsu ya yi tauri ko hannayensu su mumurde, abinda ake so a nan shi ne, du mai wata yar guntuwar tebarsa, mai wani lumkilumki a bayansa, da wani mai mundil mundil din hannu du su sabe su zube, slim, su zubar da du wani teba, ko wace ya kasance bayanta ya fice girman musali akoy itama mashine din dake rage masu tudu ko fadi, dan haka cikin gagawa aka shiga horar da su, wanda wasunsu har hawaye suke na wahala, basu saba ba, ba.a saba masu da haka ba, Haka suka jure sukai ta motsa jiki, ba su su baro wajen nan ba sai kusan takwas, ya rage minti talatin takwas ta yi aka fito da su, Tsaye ya yi yana kallon yanda suke haki ya ce " daga yau, kulun, karfe shida ta maku a wajen da muka fita gudu yau, zan salameku bayan mun gama karfe bakwai da rabi, kunada minti goma na cin abinci, minti ashirin ku tabatar da kun shirya kowace da kayanta a dakinta ku fito daukan darasi, Amsawa suka yi a tare sannan kowace ta nufi dakinta cikin gagawa Tana zuwa ta tarar da abinci sannan da wasu fararan kaya wando da riga suma, sai dai su wandon ne kawai sake aman rigar daidai take da mutun cicif kuma fara tas, Ajiyewa ta yi da gagawa ta fita ta je