← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 94

Sashe 33

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

abin ba kuma, Tsaye ta tarar da shi wajen windows daga shi sai gajeran wandon dake cikin jalabiyarsa yana tsaye kikam ya lumshe idannuwansa iska, sansanyar iska, mai cike da ni.ima na hura shi, yana jin kansa sakayau, Wani irin ihu ta yi tana mai cewa" ka kwonta! Juyowa ya yi da sauri, da kuma mamakin me ya dawo da yarinyar nan a wannan lokacin da bai nemeta ba? Sai ganninta ya yi a kiftawa da bismillah ta masa wani irin afkowa gaba dayanta a jikinsa wanda hakan ya saka shi zubewa kasa, domin kuwa ba wani shiryawa ya yi ba, ba wani tunanin haka zai faru ya yi ba a ransa, Suna faduwa kuwa karan harbi mai boyayen kara ya fasa gilas din dakin ya tafi ya huda labulen ya shiga jikin garun domin kuwa bai samu wanda aka daidaita dominsa ba, Gannin hakan ya saka mai harbin gane cewar an gane zai yi harbin, dan haka da sauri ya tatare ya nemi hanyar tsira..... BS ba inda bai duba ba, haka abokin aikinsa ya kasa ya tsare a bakin titin yana gannin shige da fitar kowa, ya zubawa ko.ina ido , inda gaba daya sauran masu tsaron gidan aka shiga haya haya ana ta duduba masu shiga da fita, hakama cikin gidan du sun rikice bodyguards din sun fitar da du wani soja daga wajen da ya shafi Abdul da matarsa sai hayaniya ake, A lokacin da abdul ya gane abinda ya faru, Ya ganshi yashe kasa, yar yarinyar nan dare dare saman kirjinsa ta saka hannunta ta rufe bakinsa, Ya rintse idannuwansa yana sauraron yanda zuciyarta ke dokawa,..... Tabas jaruma ce, sai dai boyayiyar jaruma, Da sauri ya yinkura ya cireta a jikinsa da niyar mikewa sai dai ta kara damke hannunsa da yannayin tashin hankali ta ce " ka daina yannayin masu kudi ko sangartatu ka gane rayuwarka ke hatsari ka duka, kar ka mike, domin ba.a ga wanda ya yi harbin nan ba! Yannayin yanda ta yi magana murya a kausashe, da irin yanda ta bashi ordre ya saka shi yin dan tsai yana kallon fuskarta, kafin ya bi hannunta da kallo, Da sauri ta cika hannun nasa tana mai kara tamke fuskarta , tana kallo ya mika hannu ya dauki jalabiyarsa, ya dan tsurawa Ni.ima ido sannan ya juya ya fice, Kuka Ni.ima dake dukunkune waje daya ta fashe da shi tana mai bin hanyar da ya fice da kallo, Shikenan , ta shigo rayuwar hadari, ashe da gaske dai neman ransa da du wani wanda ke tare da shi ake? Yanzu da an same shi, da shikenan har an mayar da ita karamar bazawara? Da sauri Hafsat ta kawar da kallonta saga kan Ni.imar ta bi bayansa, Dakinsa ya je, kai tsaye ta ratsa ta shiga inda ya shiga, Tsayuwa ta ja ta yi dan ta gane wankama shi ya shiga, Tana nan tsaye ya fito da tawul daure a kugunsa hakan ya saka ta kawar da dubanta daga wajensa, Ikon Allah ita bata taba gannin bakin namiji mai cikar gashi a fatar jiki irin wannan ba, dama ba sai larabawa, buzaye , fulani, da dai sauransu keda irin wannan izgar gashin? Hankali kwonce ya cire tawul din, ba tare da damuwar tana dakin ba, ya saka wandonsa na ciki, sannan ya dora wani wandon baki, Rigarsa ya saka irin mai lafewa a jikin mutun din nan du tana kallon wajen da ba wajensa ba, Bata tashi juyowa da sauri ba sai da ta ji wani kara yannayi na gyaran bindiga, Da sauri ta juyo tana mai zaro ido tana kallon irin yanda ya saka kartushi a yar karamar bindiga ya ja ta ya gyarata da kyau sannan ya yi mata kyakyawan ajiya a kugunsa, irin ajiyar da idan ba karantun hakan aka koya maka ba , ba zaka taba iyawa ba, Bata gama mamaki ba sai da ta ga ya dauko computernsa ya kunna ya ajiye saman table din dake dauke da turaruka shi kuwa ya dora hannunsa na hagu dake jimke saman table din, na daman kuwa ya shiga dadana computern kamar wanda shi ya kirkiri abinsa, Bakinta da hancinta gaba daya a bude suke tana mai binsa da kallo, har ya gama nuno waje waje a jikin computern dake nuna ciki da wajen gidan, abin mamaki har benen da aka yi harbin daga shi gashinan waje waje radau ya fito a sama Sai da ya yi wani recherche sannan ya dora wata hanya, wace ke nuna wani mutun tsaye yana ta waige waige bayansa goye da wata jaka sannan kunnensa yana waya da alama wayar a hanzarce yake yinta, A tare suke kallon mutumen, kafin ya dago da dubansa ya dora saman kanta, irin yanda ta matse masa waje ita kanta bata kula ba, ta raja.a tunaninta da hankalinta kan mutumen nan, Yannayin kallonsa ya shaida mata yana nufin wannan shi ne, dan haka da sauri ta je dora hannunta saman computern dan gannin hawa na nawa ne, da yannayin da zai kara tabatar mata da wajen, Da sauri ya tare hannunta, domin gaba daya computern na anfani da emprinte din yatsutsansa ne, dora hannun wani na iya tayar da karan laluwar da ya saka gaba daya a cikin gidan, Fitar mata da abinda ya tabata take son gani ya yi, yana mai dan kara yarda da yannayin aikinta , domin da wanda bai san aikinsa bane yana iya fita da gudu ya shaidawa mutane ai yana nan, a fantsama a yi ta hauka ba.a samu mutumen ba, Maimakun ya ga ta fice da gudu sai ya ga ta kara dan abin hannunta ta ce" BS, suspect din mu na hawa na biyu wajen matatakala yana kokarin saukowa, sanye da bakin jeans da riga baka mai dogon hannu, fari ne kar bayansa dauke da jaka baka mai dauke da bindigar, Yana waya, ku kula yana waya, kar ya jefar da wayar ..... Shiru ta yi ta tsurawa screen din ido , inda shi kuwa ya tsura mata ido yana kallonta, A sakalce ya ce" ke, yo ke bakya zuwa ne? Kin wani sakani gaba kina kale min na.ura? Bata daina kallon computern ba ta bashi amsa a takaice cewar" eh! Murmushi ya yi ya juya ya zauna saman kujera ya daga hannayensa ya dora bayan sumar kansa ya dan daga kujerar daga gaba ya watsa kafafuwansa yana kai kawo yana duban yarinyar, Bakinsa ya tabe , ya so ta bara masa dakin, shima ya fice ta inda zai gyara shi ko zai damki wannan wannan mai harbin, aman ta wani zauna , shi kuwa ba zai yarda saboda haka wannan yar yarinyar ta gane menene aikinsa har ta falasa shi ba! A hargitse mutumen yake doka waya wa wanda ya bashi wannan mission din, Ana daga wayar aka ce da shi" ka tabatar ka yarda layin nan ko ka hadiye shi, sannan ka san yanda zaka kubuce masu, idan kuwa aka kama ka, ka san ko rayuwar wa ka saka a hatsari! To fa........., shin za.a kama wannan mutumen kuwa? Yaya tafiar wannan aiki tsakanin Hafsat da Abdul? Ni.ima fa? Bs Fa? Na ji dadin comment din ku sosai wollah, Ban bayar da amsa ba domin ban zauna ba, Ina biye da ku kamar yanda kuke biye da ni makaranta *KUTKALE* *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 3 Ki zzo gare ni Hafsat, Ya karashe yana mai dafe kansa da dukannin hannayensa kafin yake mikewa kuma da wani irin sauri Fita ya yi ya nufi dakin da computersa ke girke, Yana shiga ya kunna ya kamo ya shiga bi yana kallo daya bayan daya Ba abinda ya gani sai duhu ridim , wato wanda ya dauki Hafsat ko waye ya san inda camerorin suke dan kuwa baki daya sai da aka rufe su aka hana gannin abinda zai wakana Gaba daya Abdul ya fita a hayacinsa, du wani abinda zai tunkara dan gannin ya sameta, ya ganta ya duba , ya bincika aman babu, babu ita babu alamunta A hankali ya ringa jin wani irin zazabi na son rufe shi, hakan ya saka shi neman magani ya hadiya kafin ya juyo inda ya tara gaba daya mutanen dake cikin gidan, wato du wanda ya kwana ya tashi a gidan nan in dai mutun ne dan adam yana halarce a tankamemen falon Abdul du suna zazaune kamar yanda ya umarta shi kuwa yana tsaye dafe da kansa, ciki kuwa harda matarsa ta sunna da kuma Furaira Sai da ya gama saisaita kansa sannan ya shiga bin kowa da kallo, Sai fa ya gama kare masu kallo kafin ya hadr hannayensa cikin wata murya mai nuna tsantsar tashin hankali ya ce" koma wanene a wannan waje, na roke shi da ya saketa ya kama ni, Na yarda, ya gane menene lagona ya kuma dakan harbi a lokacin da nake barci, Ina mai rokarsa, idan har da dan sauran imani da kuma sannin zai yi kwonciyar kabari ya sakar min ita ta yi tafiarta nesa da ni, nesa da hargitsin rayuwata, Ya karashe yana mai kara bin su da kallo, Gaba daya, yana iya cewa gaba daya sun nuna fuskar basu san abinda yake nufi ba, kai ko wa yake nufi gaba dayama, dan haka ya kara gyara tsayuwa ya ce" daya daga cikin ma.aikatan gidan nan aka dauke, wace ke gadina mai sunna Hafsat, mun wayi gari babu ita ba labarinta, ba kayanta
Chapter 33 · 0% Book details