Sashe 64
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai dai rigar bayanta gaba daya a bude yake, ahigar sam batai mata dadi a ranta ba, Jiki a sanyaye, muryarma a sanyaye ta buda baki zata yi magana ta kasa, ta kara budawa zata yi sai kawai ta shiga inda indar da bata saba ba, haka kuma jikinta ya dauki rawa, muryarta ne take rawa sosai a lokaci daya ta ce" *MAMA* muryar mahaifinta da ya kasa hakurin jiran har su je gaishe shi ne ta katseta a lokacin da ya ce" *UWATA?* A tare suka juya , shi kuwa ya tako ya shiga cikin dakin a nitse, sai da ya kali Hafsat din sannan ya kalli mahaifiyarta , Da hannunsa ya yi mata nuni da ta zauna, Cikin nutsuwa ta zauna jikinta a sanyaye dan ta tsorata da abinda ya tsoratar da yarinyar nata har haka harma ta kasa magana, Sai da malan ya kara dakin sannan ya zauna cikin nutsuwa ya ce""" *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 Cikin kakausar murya aba ya ce" ku tashi ku tafi Kowace sai da ta kale shi, baki mama uwar gida ta kebe kafin ta fara mikewa da sauri ta yi gaba kasa kasa kuwa sai guna guni take Bayanta suka rufa baya , sai mama kawai a zaune kanta a sade Aba ya kawo dubansa wajenta, cikin kakausar murya ya ce" ba nace ku tafi baki dayanku ku bani waje ba? Da sauri ta mike tsaye tana maida kukan dake cin zuciyarta, Juyawa ta yi har ta kusa fita a dakin ya ce" daga yau a fara shirya Uwata, in sha Allah zan karbi kudin aurenta karshen makon nan! Mama kam kanta kawai ta gyada ta fice a dakin, wannan shine a dakeka a hanaka kuka, shi dama malan idan ransa ya baci kowama hadawa yake ya hukunta ba ruwansa abinsa, Yanzu dai sun jaza masu fada da fushin malan, a kan mamansa ransa na kololuwar baci fa! Sai da suka fita baki dayansu Malan ya dauki katuwar wayarsa irin rakani bayi din nan mai hasken tsiya ya latsa numbobin ya samo sunnan da yake nema ya danna kira Abdul dake zaune yana shan lipton dan safiar yanzu ta waye a wajensa ya daga kiran cikin nutsuwa ya yi salama Sai da suka gaisa a mutunce sannan malan ya sauke ajiyar zuciya cikin yannayin nutsuwa ya ce " ka yi hakuri na yi maka kiran samako ko? Abdul ya ajiye dan abin shan lipton din dake hannunsa ya gyara zama tamkar malan din na gabanshi ya ce" aa, ai na jima da farkawa malan Malan ya ce" masha Allah, dama ina so ne na fada maka, ka fadawa wannan yaro mai neman auren Uwata, idan har da gaske yake ya turo da magabatansa, sannan ina so ka taimaka min wajen bincike kamar yanda ake yi Shiru Abdul ya yi, har sai da malan ya dubi wayar yana fadin ko dai bai ji ba network din nan da bashi da tabs Abduk ya sauke ajiyar zuciya ya ce" in sha Allah malan zan shigo idan na sauka a aiki Salama suka yi Abdul da malan, nan Abdul ya mike ya nufi dakinsa dan kimtsawa ya tafi wajen aiki A lokacin da ya fito suka hadu da Na.ima, ta sha doguwar riga ja mai duwatsu, rigar ta bi dan jikinta mai tsari, kokarin karasawa dakinsa take suka hadu a nan falo Hannunsa ya saka ya kamota jikinsa, goshinta ya sakarea kiss ya shafi gefen fuskarta kafin a hankali ya ce" zan tafi wajen aiki Idannuwanta ta lumshe kafin ta ce" zan yi missing dinka Murmushi ya yi mata sai kuma ya juya daga shi sai ky din motarsa ya dauki hanya Ya yi aikin awa uku, a kampaninsa na atampa daga nan ya dauki hanyar doguwar tafia, Hankali kwonce yake ratsa jejin har ya karaso dan nesa kadan da wajen sannan ya sauka ya daga hannayensa sama sakamakon mai tsaron da ya kurma ihun ya daga hannayensa sama sannan aka shiga tambayarsa waye shi, wa ya zo nema, wa ya gwada masa wajen? Shi dai a tsaye yake har suka karaso inda yake suka shiga da shi wajen horon bodyguards din suna masu taka tsantsan da mamakin waye shi kuma daga ina ya zo masu wajen sirrin nan? Sai da aka yi jiran GN ya zo sannan suka sake shi bayan ya bada umarni A hankali suke takawa GN da shi, cikin yannayin mamaki GN ya ce" yaya aka yi ka kawo kanka wajen nan? Abdul ya kale shi ya ce" a ranar da aka maida mu tare da mahaifiyata, tun a ranar na saka maku abinda zai nunan inda kuke dan tsaro, A ranar na san inda kuke ba.a dai yi falilin da zan zo bane sai yanzu GN ya jinjina kai yana kallonsa, wato dai shi bai yarda da kowa ba? Abdul ya ce" waye BS? A ina iyayensa? Ta yaya ya zo base? Menene halayensa? GN gabansa ne ya ji ya fadi yana kallon Abdul, Tsoro ne ya ji ya kama shi kar a je BS ya janyowa kansa wani balakin? Abdul ya juya ya fuskanci GN da kyau , ya yi masa wani kallon dake nufin shi yake sauraro GN ya sauke ajiyar zuciya ya ce" BS, bazabarme ne, domin ni ne mahaifinsa, mun same shi ne da mahaifiyarsa a lokacin muna soyaya, Allah bai yi zan aureta ba aka aura min wata Abdul ya kafe shi da ido cike da mamakin wai ashe BS dansa ne? Aman yaya aka yi bai amsa sunnansa ba? Duda ya ji ya ce ba da aure ya same shi ba, Kansa ya girgiza ya furzar da wata iska daga bakinsa, shi kam bai san me ke damun mutane ba, ya sani akoy kadara aman wai har wata kunya yake ji a yanzu ko me? Tsaki ya ja a fili ya ce" yaya aka yi ya ci jarabawar zuwa wajen nan, harma ya zama Bodyguard soldier? Shin takardubsa suka bashi dama ko babansa? GN ya kali Abdul ido cikin ido, sam bai ga tsoro ko alamun zai risina masa ko dan ya girme shi, dan haka gwara ya fito a mutun ya bashi du wasu informations kan questions dinsa, fatansa dai ba wani laifi ya yi ba Bakinsa ya buda ya zayanewa Abdul du wata tambaya tasa a nan a inda suke tsaye dan GN ya so su karasa su zauna abdul ya ce sauri yake Sai da ya gama Abdul ya gyada kansa ya ce" masha Allah GN ya ce" aman, sire wani laifi ya aikata ne? Abdul ya kale shi, sai da ya gama nazartarsa sannan ya daga kafadunsa duka biyu ya ce" bai aikata ba tukunnan, ka bashi sako yarinyar da yake neman aurenta idan har da agske yake mahaifinta ya ce ya fito a cikin satin nan a yi komai a gama, idan kuma ba da gaske yake ba, abinda nake so da shi shine ya janye a hankali, ba tare da ta zubar da hawaye dalilin hakan ba, dan na tabata zata samu wani idan shi baya yi Yana gama fada ya mikawa GN hannu suka gaisa sannan ya sakar masa fuska suka yi salama tare da mutunta junna suka rabu Abdul bai koma gidansa ba masalaci ya je, yana zuwa ya tarar da Malan zaune da jama.a ana ta karatu dan haka ya gaishe su kawai ya juya ya koma gidansa Da dare bayan salar isha.i suka shigo da malan, sai da suka zauna Abdul ya fadawa malan cewa ya je, ya binciko, in sha Allah ya fadawa mahaifin yaron idan har sun tashi auren da gaske to su fito Malan kam godiya ya ringa yiwa Abdul, wace har sai da ya gaji da amsawa Sun jima zaune suna hira jefi jefi, sai malan ya ji Abdul ya ce" wani abu ya faru da ita ne? Malan ya kale shi, sam bai gane wa yake nufi ba, aman gannin ya yi jim ya saka shi cewa" wa fa? Abdul ya dago yana kallon malan, shi fa gaskiya ba zai cewa Hafsat wai mama ba, shi kuma ba zai kama sunnanta kiri kiri gaban malan har a je ya daina gannin mutuncinsa ba, dan haka sai ya ce" ita wace za.a yiwa auren Malan ya kada kansa yana murmushi ya ce" Abdallah, bana son yaro ya ringa yi min dogon zance a gida, ai kawai idan yi yake ya fito a yi a gama, idan kuwa ba shi ne rabon ba sai ya bada waje ko zata sami wani ya aureta itama ta je ta raya sunnar ma.aiki Abdul ya gyada kai sannan ya kawar da dubansa, wani haushi ne ya ji yana ji, wai ko ta samu mai aurenta, Hafsat din rasa mai sonta zata yi ne? Yarinyar mai daraja mai hankali mai ilimi mai kyau? Me ta rasa a jikinta na mace har da malan ke son saka gagawa a lamarinta? Yau bai cika dare ba ya yiwa malan salama, Yana saukowa ya hadu fa ita tana shanya saman igiya, ita daya ce kwal a tsakar gidan da yake lokacin kamar da sanyi sanyi kowa yana daki ya labe, itama wankin kayanta irin dogon wando ne ya sakata yi da dare sannan ta kwashe da wuri dan basa barin kananun kayansu na shawagi a tsakar gidan, wannan mahaifiyarta ce ta yi mata wannan horon Tsayawa ya yi ya harde hannayensa duka biyu yana kallon