← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 94

Sashe 69

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba suna zaune suna sauraron abinda ake fada daka dakin ne suka zabura a tsorace suka yi infa Hafsat take yashe a sume A daidai wannan lokacin Ladiyo ta ce" mijin da aka aurawa uwar malan lale shi ne uban masu gida Sunnansa *ABDUL JABAR ABDUL BASID* wannan da NURU WALAM ke talar shagunansa a dukan kafofin talabijin dake niger, wa.inda du abinda aka saka idan aka cire za.a saka wani sai an hasko daya daga cikin shagonsa an yi talarsa , Wannan yaro karamin mai tashen.... Ke ki rufe mana baki , mu zaki kawowa zancen banza a nan? A ina? A ina zata ganshi? Wacece ita? A irin wannan anguwar? Kin san da wa kike magana? Amaryar malan, jinnin sarauta, yar shuwa ta fada da wata irin tsawa tana katse ladiyo, daidai nan baban dan hajia mama ya shigo gidan a wani irin haukace, wanda yake adawa da yayan Maman su Hafsat, bale Hafsat din Yana shigowa ya ce".... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 5 Yana shigowa hankalinsa tashe, karara fuskarsa take hargitse har ya kasa zama ya taya mahaifinsa salamar mutanen da suka rage ya afko gidansu a orin wannan lokacin da yan uwansa da iyayensa da bakin fuska ke tsaitsaye ya ce" ummah, ummah kin san waye wannan Abdallahn? Wannan yaron gayen dake zuwa gidan nan ne, wanda ke da iko da cikin gidan nan fiye da mu yayan da Malan ya haifa, Hankalinta ne ya kara tashi ta ce" kana nufin dama shi ne mai wannan dukiyar? Wannnan yaron mai shige da yan daba mai magana ba risinawa mai yi mana kalon sa.aninsa shi ko wa? Harde hannayensa ya yi ya ce" shi fa, shi da kansa Wani wawan tsaki ta ja tana waskewa ta ce" dama wa zai kwasa idan ba abokin yi ba? Da sauri nana Mariama ta kaleta, tana yin shiru amaryar malan ta ce" ai dama sai abokin aiki ya san kan aiki, wa zai dauki saura? Ai shi dai da ya saba shi zai kwashi abinsa Nana mariama ta kaleta da kyau, wani abu ne ta ji ya kasa ficewa a kirjinta, a yau ta ji ba zata iya yin shiru ba dan haka ta ce" eh ai ba laifi bane, idan kika ga har ya kara nacewa mota tabata ya ji dadin tukinta, wata mitar dan ubanta komai gyaran da za.ai mata ba zata tashi ba sai dai ta ja kara ta zubar da bakin hayaki! Guda matar nan marokiya ta kara saki tana dariya, domin kamar an saka su buda baki a tare abinka da ko.ina haske na haska dakin sai ya kasance du ana kallon su Wace ke bima mama ce ta ce" ikon Allah, Mariama dama kema baki da kunya? Dan kanwarki ta auri mai kudi har bakin ki ya bude? To a yi dai mu gani ku tsaya ku ga zaman kafin ku fara takun kasaitar Sai da ta juya dan nufar dakinsu ta ce" zama daram Uwar karuwa a cikin wuta! Du da kallon mamaki suka rakata, domin kaf a cikin yayan mama ita ce mai lafia , koda an tabota takan labe ta sha kuka ne bata tankawa bata kula kowa haka har Allah ya rabata da rayuwar gidan malan Sai bayan ta shiga cakartun magana ya bi bayanta, bata damu da juyowa ba ta yi shigewarta falo ta shige cikin dakin mama Tana shiga ta tarar mama na shafa goshin Hafsat sun shinfideta saman bed sun gyarata sauran na tofa mata adu.a Yannayinsu ya shaida mata da suma ta yi, da sauri ta karasa tana tambayar me aka yi? Menene? Mama ta ce" wayar ce ta yi kara , sako ne tana dubawa sai kawai ta ihu ta fadi, mun shafa mata ruwa kamar ta farka aman kuma kin ga idannuwan a rufe mu dai munai mata adu.a Zama itama ta yi tana gyarawa yarinyarta hijab din jikinta sannan ta dauki wayar ta duba message din Bakinta ta tabe ta ajiye tana hararn Hafsat din a kasan zuciyarta kuwa fadi take banza ba suma ba sai dai ki mutu muna nan ma ga irin lokacin da zaki dauka baki farfado ba! Suna nan zaune su Mama sai tofi suke mata suna tofa mata adu.a aunty nana mariama kuwa na zaune gefe tana baiwa yarda madarar da ta kada mata Gidan ne ya dauki shiru, shirun lokaci daya haka marokiyar kanta ta yi dif tamkar ta fita a gidan Dan lokaci aka dauka sai ga Malan ya bayana a kofar dakin yana salama Mama ce ta mike da sauri ta nufi kofar tana goge fuskarta tana gyarawa dan ba zata so ya ga yannayin da take ciki ba Cikin nutsuwa ya shigo dakin, A hankali yake bin su da kallo, kafin ya amsa gaisuwar da suka jero masa sunai mata su duka Sai da ya gama amsawar ya ce" Alhamdulilah, zaku iya tashi mazajenku na waje suna jiran ku Ba wace ta tsaya tsaye tsaye du suka mike suna daukan abubuwan da suka san nasu ne, sukaiwa mamansu salama A hankali malan ya karasa bakin bed din da mamansa ke kwonce Ido ya tsura mata na dan lokaci, a hankali ya ce" mamana, tashi mana, ba kyau fa irin haka Idannuwanta ne suka dan yi rawa jin muryar babanta, tana son buda idannuwanta tana tsoron ta bude ta ji wannan labari mai kama da almara, ita bata san da me zata kwatanta wai wai tap, ina ba zai yiwu ba, ba zai taba yiwuwa ba! Ita ta rayu da Abdul a matsayin mijinta? Mutumen da suka raina juna? Mutumen da karara ta san waye shi a harkar mata? Mutumen da macen dake gidansa kanta sai dai ta isko shi? Abdul bai iya yiwa mace yar murya ba bale ya rarasheta, bai iya bin mace ba, bai iya yabawa mace ba, ta rasa wani banzan tunani na kar ya bar malan cikin zulumi ya saka shi wasa da maganar aure, shi kennan a wasa da komai rayuwarsa zata kare? Haba dan Allah! Bama zai taba yiwuwa ba Murmushi malan ya yi gannin bakinta na murgudawa da alamomin tsaf ta farka , kansa ya girgiza yana girmama rigimarta, wato a haka take a sankame du sun zagayeta bayin Allah Juyawa ya yi ya yafito mama da hannunsa ya yi gaba Sai fa mama ta dan kara waigawa tana mamakin malan hala bai san a sume take ba yake mata magana? Ko ji yake da gangan ne? Da sauri ta taka ta cin masa ta karbi kys din hannunsa Sai da suka haue sama ta ga matan gidan a tsaitsaye da alama kowace ya kiraya Bude dakin ta yi sannan ta koma karshe ta tsaya, sai da malan ya shiga, suka shige sannan ta bi bayansu Zama malan ya yi a babar kujerar da yake zama wace ba mai hawa sai shi Su duka a kasa suka zazauna suka tankwashe kafafuwansu Sai da malan ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" tsarki ya tabata ga Allah ubangiji subahanahu wata.ala, Alhamdulilah, Kamar yanda kuka ji, an daura auren mamana yau bisa sadaki mafi kankanci jika goma , sai kyautar uwa da ta uba mota kirar Ferari daya daya, sai motar jigilar kaya wato babar mota ta uba, sai kujerar haji in sha Allah ta uwa uba da yan uwanta da iyayenta wato ku A tare suka kalli juna sannan suka kale shi Malan ya ci gaba da fadin" za.a kawo lefenta jibi idan Allah ya nuna mana sannan za.a saka bikin kusa kamar yanda kuka sani bana taron wunin biki a gidana, ba.ai min kade kade bale wata diner, almajirai nake tarawa a wuni ana sabkar alkur.ani mai girma da neman zaman lafia a wajen Allah Shiru ya yi yana kallon yannayin kowace, shirun da ya biyo baya daga garesu ne ya saka shi guara babar rigarsa yana sauraron su Hajia mama ce ta muzguta ta ce" uhum Malan ya saki murmushi yana kada kai, sauraron su kawai yake yana jiran jin fatan alkhairi daga bakin dayarsu, aman cikin ikon Allah shiru ba wace ta yi fatan alkhairi Dubansa ya kai wajen mama ya ce" Ramatu Da sauri ta dago da dubanta ta kali malan Malan ya gyara zama ya ce" daga yau, na umarce ki da ki nuna kulawa wa yayan da kika haifa, na soke maganar jin kunya kawar da kai ko kara, na umarce ki da ki buda baki ki yiwa yarki adu.a, ina so ki kula da shirye shiryen tarewar yarki! A karo na biyu ta kuma kallonsa, kwarai ba wasa da gaske malan yake, da gaske yake ba wasa a maganarsa Hannayenta ta hade ta shiga murzawa a hankali , Cikin nutsuwarta ta ce" Alhamdulilah, Allah ya basu zaman lafia Malan ya gyada kansa yana murmushi ya mike ya shige ba tare da ya kuma tankawa kowace ba A hankali ta mike itama dan ficewa a dakin dan gaba dayanta hankalinta a tashe yake , bata taba irin haka ba, ba.a taba haka da ita ba, hasbunallahu wani.imal wakim Tana fita a dakin ta kama sauri, aman cikin ikon Allah sai da hajia mama ta cin mata, matar sosai dajikantaka ta fara bayana a jikinta aman dan tsabar fitina ta riko hijabin mama ta ce"malan ya yi haka dan ya nunawa duniya daban take da sauran ko? To kudinsa baya damuna! Sannan bana son kujerar makar domin ni ba zan je bautar
Chapter 69 · 0% Book details