Sashe 46
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daidaikun sojojin dake yawo a tsakar gidan, haka kuma ta mayar da dubanta kan BS da kuna abokin aikinsa dake tsaye wanda BS ne kawai ya bata amsa kan ba zata shiga wajen Abdul ba, hakan ya saka take ta hayaniya tana karawa kan sai an barta ta shiga, domin gidan mijinta ne, tana da ikon zuwa a lokacin da ta ga dama, harma ta gayaci wanda ta ga dama Dubansa ya maida wajen abokin aikinsa, yana tunanin sakawa a fitar masa da wadinnan yan matan yan rainin hankali Abdul ne ya bude kofar dakinsa ya fito cikin takunsa na kakarfan namiji Jikinsa sanye da doguwar riga ta sallah baka mai dan adon goldin Fuskarsa ba fara.a ko ta naira biyar, ya hade fuska tamkar zai kai duka Wata irin firgita Hafsat ta yi a lokacin da ta ga fitowarsa domin bata shirta hakan ba, sam bata yi tsamaninsa a irin wannan lokacin ba Sai da ya ja ya tsaya kamar yanda ya saba, ya kai dubansa wajen Hasana dake tsaye ta shiga taitayinta jira kawai suke ya yi gaba su bi bayansa, Haka kuma ya kai duban nasa wajen Hafsat, Irin kallon dake bata wahalan nan dai ya yi mata, wani kallo mai kama da tsana tsana mai shige da harare hararenta, Tsai itama idannuwanta ke cikin nasa kafin a hankali saman lebent ta furta" *ABDELLAH* ta karasa ta lumshe dara daran idannuwanta ta kuma budewa hakan ya saka ta tara masu ruwan kwallah a cikinsu Gabansa ne ya ji ya rikida ya fadin masa, hakan ya saka shi kawar da dubansa yana mai jin wani ruwa ruwa kadan a goshinsa Hannunsa ya kai wajen goshin ya dan shafo, ya kalla da idannuwansa, *ZUFA* ZUfa ce yake yi dan ya yi ido hudu da yarinyar nan? Juyawa ya yi da sauki ya nufi kofa hakan ya saka su mara masa baya da sauri Yana fitowa BS na gama rufe bakinsa cewar a fitar da su Yarinyar da ta baiwa wajen su BS baya kan ba zata iya yin cacar baki da su bane ta juyo da sauri jin an ce wai a fitar da ita Sai da ta yi masu kallon sama da kasa kafin ta ce" *GIDAN UBAN NAWA ZAKU CE A FITAR DA NI?* Abdul da ya sanyo kai ya fito da sauri ya kai dubansa saman kanta, Itama idannuwan nata ta zuba masa cikin wani kallo na rainin wayo irin na ka.ide tabas shi ne, Gyaram murya ya yi, hakan ya saka su Abdul ja gefe sannan suka sara masa Kallon su ya yi a fakaice sai kuma ya kai dubansa wajen matar da ta gudu da igiyar aurensa kan wai yana cikin hatsari da kuma yar farar yarinyar da suke tare Bai yi magana ba sai idannuwansa da ya jefa masu tambaya da su ta hanyar buda masu su baki daya ya dadage masu giraransa sannan ya dan gumtse bakinsa Bahija ce ta shiga dan kara jan abayar dake jikinta tana kara rufe jikinta sannan du rawar kan nan da take yi nan da nan ta nutsu, ta sada kanta ta kasa kuma dago da kanta ma bale har ta dubi idannuwansa dake firgitata Wace suke tare ce ta kalli yannayinta, murmushi ta yi a ranta tana ayyana lale na yarda matansa na tsoronsa tamkar rai, kamar ba Bahija ba ta wani nutsu nan da nan daga gannin mutun tsaye a gabanta, Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mika hannunta irin su yi musabahan nan ta ce" *hi kanina, sunana Furaira ana kirana da Fulawa, wato fleur, ni yayarka ce wace aka fara haifa kafin a haifi mamanka* Hannun nata ya bi da kallo, nan ya ga baki bakin hannayen nata irin na kana shafe shafen nan sosai ya kasance jikinka ne farin banda hannun naka, sosai ya kone mata hannun du irin kinshin da akai mata dan boye shi kuwa tsaf ana ganninsa A haka ya kuma binta da kallo ita din kanta, Wata irin farar hoda ce akai mata mak up da ita ta yi mata bau da ita, sai gashin idon nan manyan wato na karshen tsayin nan an sakawa idannuwanta da suka fara dan jemewa irin man shafe shafe ya ci fatar idon du ya yamutseta, Wani irin kwali ne aka saka mata mai mugun baki sannan aka ja shi saman idonta sosai kafin a dora mata far bau mai ruwan ja ya yi mata wani irin bau a fuskar, sai jan baki da aka saka mata a leben wanda ya saka bakin yin wani irin dambarere da shi , kai kana gannin fuskarta ka ga rikakiyar yar bariki Abdul kam kallon tsaf yake mata tun daga kanta har kafarta, hakan ya saka hannun da ta miko da gatsali da iya yi ya fara gajiya har ta fara jin wani iri hakan ya saka ta bude bakinta da niyar yin magana tana dan satar kallon yan matan dake bayansa wa.inda ta tabata bodygurads dinsa ne ta yannayin shigarsu wato su Hafsat, da Bahija da su BS sai shi kansa wanda ta zo dominsa ta ji muryarsa a tsakiyar kanta inda ta yi gagawar kallonsa da yannayin mamaki Abdul ya ce" *Dan girman Allah, ku yi hakuri yan uwana, walahi doguwar tafia ce na yi tun karfe biyar na suba sai karfe biyu na dare muka karaso, zaman mota hakan ya saka ina tare da gajiya sosai gabaina na ciwo , ku yi hakuri da kadan dinsa, kun san hannuna zaku ji da yawa daga na ji garai* *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 1 A lokacin da suka fito gaba dayansu da yannayin na zakunna, kowane na jefa kafarsa inda ta je, suka tsaya gaba dayansu a tare sakamakon ganninta tsaye ta zuba masu ido su duka, Sai da gabansa ya yanke ya bada wani irin sautin da kunnayensa suka jiyo masa, Tsaye take kawai, hannayenta gaba daya a sake, wandon dake jikinta irin mai lafewa a jiki ne aman kuma sakake wajen mazaunanta kawai ya rike , sai riga mai botura da wata a ciki wada dalilin bale boturan da ta yi ya saka ake ganninta, kanta dauke da asalin gashinta ba wancen atach din ba, Fuskarta babu ko digon kwali bale a yi hangen hoda ko wani abin, Aman wani fayau da shiga ido da take sai a hankali, dole ta girgizawa namiji lafiyaye zuciya sai dai idan zuciyar taka na hangen wata sai ka kyasa a ranka ka huce wajen, Hannayensa ya daga ya cusa cikin gashin kansa da ya bar suma ta taru sannan baya gyarawa, Sai da ya dan waiwaya ya ga tsayuwar me kuma suke a bayansa? Sannan ya daga kafarsa ya tunkareta, Hannunta na dama ya damka ya jata tamkar rakumi da kala haka ta bi shi ba tare da ta warci hannun nata ba, ba kuma ta yi masa gardama ba, Da kallo suka bi su, inda BS ya daga kafarsa ya bi bayan su da saurin gaske, sai dai yana karasawa Abdul na banko kofar da wani irin karan sautin dake nuna halin bacin ran da yake ciki, Wani irin hankadata ya yi cikin dakin dake mamaye da duhu, wanda yake daya daga cikin dakunan gidan, shi kansa bai san ainahin inda zai je ya kuna fitila ba, sannan tun da ya hankadata yama rasa inda ya hankadata, Garu ya yi nufin kaiwa naushi, wanda sai da ya naushi iska sau uku kafin ya samu hannunsa ya naushi garun da wani irin karfin da da normal ne sai ya ji jiki ainun, aman da yake ransa bace ne sai ihun bacin rai da ya saki murya kausashe ya ce" me kika ji? Me ki ka ji nace? Inda yake kallo daban, inda muryarta ta fito daban, domin ita a bayansa take, a hankali, cikin mutuwar jiki ta ce" ina bayanka, Juyowa ya yi ya yi shiru, inda ya dauke numfashinsa, yana so dole ya lalubota ta habyar numfashin da take saukewa, Fahimtar hakan da ta yi ya sakata tsayar da numfashinta sannan ta canza waje da sauri ta saisaita ajiyar zuciyar da take yi, ta dan labe wajen labulen wajen ta ce" a wajen formation din zama gagarimin sojan dake aiki wa kasashen duniya baki daya, wanda yana da damar yin operation inda ya ga dama, yana da takardun shaidar shi dan kasar da du ya yada zango ne, shi dai wannan mutun ko shugaban kasa na mangarinsa domin ba.a bayar da formation dinsa a kananun kasashe sai irin su chaina, dubai, ko su Saudiya. Japan...da dai sauransu.... Wanda a cikin mutun hamsin bai fi biyar su fita ba, kai ana iya goge kowa a hanawa duka hamsin din! Sai kuma bodyguard , ana koya masa irin wannan abin a sama sama ba a zufafe ba saboda halin rayuwa...... Labulen da ya damka ne ya sakata saurin matsawa ta canza waje , Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta ce" a ciki.... *WANENE KAI ABDUL JABAR ABDUL BASID?* Gabansa ne ya wani irin bugawa sakamakon irin yanda ta ja sunnansa lokaci daya take neman sannin waye shi, a iya yau, a iya hafuwar yau, awowin da ba zasu fi goma sha biyu ba , wanda da yawa da suke tare shekara da shekaru.basu san hakan ba? Jikinsa ne ya yi la.asar, sanyi ya yi sosai da sosai, dan haka sai ya daina neman lalubo infa take ya saki abin sauraron da ta laka