Sashe 34
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sama ko kasa, Sasauta muryarsa ya yi irin na wanda ke azabtuwa da lamarin ya dube su duba irin na neman agaji ya ce" shin , da wanda ya ga Hafsat? Kallon kallo suke yiwa junna, aka dauke wata? Mai bashi tsaro? Aa, kuma? Hankali nan ya fara tashi, da yawa suka shiga mikewa ana mayar da su zaune, inda Ni.ima ta kure shi da kallo, Furaira ta dafe kunci cike da mamakin wannan gida, Muhammad kuwa ya karasa kusa da amininsa ya shiga tausar sa yana bashi hakuri Abdul ya gyada kansa sannan ya ce" ban so mu shiga fannin neman juna ido rufe ba, ban so mu shiga fannin da zan fita farautar mai farautana ba, walahil azim idan ban kashe shi da hannuna ba sai dai karfin ikon Allah, *tunda ya yi gigin taba min ita* nima sai na taba shi! Abdul na gama fadar haka ya juya ya shige dogon lungun daka iya kai shi dakinsa yana mai jin wata irin juwa na neman dibansa ta kayar Da sauri Muhammad cike da tausayin aminin nasa ya dafa kafadarsa hakan ya saka Abdul rage saurin tafiar da yake Muhammad ya ce" Abdul, menene kuma? Me ke damunka haka da yarinyar kuma? Eh tabas dole hankalinka zai tashi da wannan sabon lamarin, to aman sai na ga abin na taba ka sosai, ko da wani abu tsakaninka da ita ne? Abdul ya tako da sauri inda Muhammad ke tsaye ya kama hannunsa da karfi kafin Muhammad ya ankara ya dora hannun daidai wajen zuciyarsa, Sai da ya furzar da huci ya ce" ta bani tsaro fiye da tsaron kanta ne? Dalilin ta dauki harbina ne? Ta iya zama da ni ne? Ko dan na ga tausayina na zahirin gaskiya a fuskarta ne? Tun da abokin aikinta ya fado dakina gudun zuciyata ya ki komawa yanda yake da, kuma yana yi gabana na faduwa ne, Muhammad, nawa suka kashe? Nawa suke son kara kashewa? Ni na san ba son kashe ni suke yi ba, dan walahi da son kashe ni suke son yi na san da tuni sun cin min, Muhammad so suke su haukata ni? So suke na zama dan gidan su? Ko takarduna suke bukata? basu da wasa Muhammad, basu da wasa...... Ya karashe yana mai dora hannunsa ya share zufar da ta zubo masa Muhammad dake kallon sa da yannayin tsoron yannayinsa ya ce" Abdul, soyaya kake da ita ko kwonci? Abdul ya saki hannunsa ya ce" ba zaka fahimta ba, Ita din ba zata kwonta da dan iska ba, bata taba yarda na rike hannunta a yannayin lafia ba bale har a zarfe wani waje da ita ba, Shiru ya yi yana kallon kasa , sai kuma ya yi murmushi ya ce" so? Soyaya? Ina na ga halin yin soyaya ni? Ta ina zan soma? Ko daya , ba wannan wasan tsakanina da ita, soyaya suke da mai gidan su, wato BS Ya karashe yana mai duban gefensa sannan ya saki murmushi ya daki kirjin Muhammad ya ce" zan iya hakurin rashin da aka rigaya akai min, bana jin zan kuma iya rintsa ido idan bamu yi fada yau ba Nan ya bar Muhammad tsaye ya shige ya saka suturar kirki ya fito ya haye mashin ya bar gidan Wasa wasa haka ake neman Hafsat tamkar ana neman zinari, ba inda basa dubawa, ba wanda ke zaune, du wanda ke gidan nan hankalinsa a tashe, GN da kansa ya tako ya zo ya kuma bada gudunmuwar neman Hafsat, Abdul du ya wani firgice, harda lokacin da Muhammad ya tirke shi kan wai me yake haka? Ya fita lokacin da ya yi niya ba tare da an san fitarsa ba , a yi ta nemansa a rasa, baya tsoron masu farautarsa su samu galaba a kansa, baya gudun wani mugun abin ya same shi,? Sai kawai ya karewa Muhammad kallo ya ce" da sun kasheta, da sun kawo gawarta kamar yanda suka saba, tana raye, yau kwananta hudu tana raye a hannun makiyana Muhammad ya ce" ka tabata makiyan naka suka dauketa? Yarinyar da ta saba guduwa abinta ta yi tafiarta? Yau aka fara tsayuwa nemanta? Shaidar basu kasheta ba zai nuna maka cewa kawai ta yi tafiarta ne Abdul ya kare masa kallo kawai ya sa kai ya barshi wajen tsaye Yau an tashi lahadi, kwanan hafsat biyar kennan rabonta da gidan Abdul, ko yau tsaye ya kwana yana kaiwa Allah kukansa Safiya na yi Ni.ima ta fara shigo masa daki, cikin shiga ta abaya a jikinta Waje ta samu ya zauna bayan ta gaisar da shi tana kallon sa, Sai da ya shafa fatihar azkhar dinsa ya kai dubansa wajenta sannan ya amsa gaisuwar tata , Yana kallonta ta ce" me ke faruwa haka ne? Kwana biyar kennan baka waiwayi inda nake ba, baka neme ni a komai ba, wani abin ne? Tsuru ya yi yana kallonta cike da mamaki, kai kwanansa biyar bai nemi mace ba? Ikon Allah, dama akoy damuwar da zata gigita wannan bukatar har ta daina hayo masa a lokacin da ta yi niya? Yawun bakinsa ya hadiya kafin ya yi mata nuni da ba komai Kukan dake cin ranta ta hadiye sannan ta mike da niyar yi masa salama, Har ta fara tafia ta kuma dawo ta duka tana kallon zara zaran yatsutsan kafafuwansa masu dauke da gashi baki sidik sun kwonta luf luf a yatsar ta ce" Abdul, ina son ka, sonka ya saka ni makancewa na bi ka, bani da jiyar gudun ka komai wuya Abdul, kar ka juyan baya dan kuwa a irin take take da kuma yannayinka da na karanta na girgiza na kasa baci, ni ban hanaka kara aure ba, dan kuwa ina son abinda kake so Tana gamawa ta mike ta fice a dakin, inda Abdul ya bita da kallo a wajen a zaune tamkar mutun mutuni Mikewa ya yi ya shiga wanka , Yana fitowa ya saka manyan kaya harda hirami saman kansa ya fito ya nufi dakin Ni.ima A lokacin da ya shiga tana kwonce saman bed tana aikin, wato kuka A hankali ya karasa inda take da irin kwonciyar da ta yi ya saka hannunsa ya dagota zaune, Ido ya dan tsura mata kafin ya ce" ba kyau kwonciya saman ciki, Kanta ta gyada tana kallonsa tamkar ta dauke abinta ta mayar cikin cikinta ko zata ji sasaucin zafin kaunar da kishinsa da take Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" kin san wani abu? Kyautatawa na saka so koda babu shi, Ki lalubi sauran kyautatawar zaman aure, ki rike a hannun ki, ina mai baki albishir din tabas zan maki hira Shiru ya yi cikin jan aji da jan maganar da ya yi sannan ya ce" ban san me yasa kowa ke gannin nuna damuwata wa batar yarinyar da ta damu da ni *So ne*, shi dama ba.a shakuwa sai soyaya? Na shaku da ita, ina walwala da ita, ta iya hira da ni Wannan shi ne kawai tsakanina da ita, Yana gama fada ya mike ya mikar da Ni.ima dake jin wani irin kaunarsa da kara shiga ranta da yake da irin yanda yannayin jan ajinsa da kwaliyarsa ke kasheta , Cikin yannayin nutsuwa ya kai lalausan lebensa wajen goshinta ya mana mata kiss, sannan a hankali ya ce" Allah ya maki albarka Bai tsaya ya kuma kara wani zama ba ya fice a dakin ya fice tare da masu bashi tsaro ba tare da ya fada masu ga inda zasu je ba, haka kuma bai yiwa Muhammad salama ba suka dauki hanya cikin tukin garari kamar yanda suka saba har suka dangana da aeroport Jirgi na daukan su sai da ya kawo su Niger, ya sauka a Niamey Suna sauka wasu motocin suka shiga wa.inda BS ua tanada , Tafia suka yi mai tsyain gaske, dan a kadan sun yi awa daya da minti talatin sunna tafe a cikin banban birnin kafin su karaso anguwar A lokacin da suka karaso masalacin da akai masa kwatance da shi ya saka su karasawa direct har kofar tankamemen gidan A lokacin da Abdul ya fito ya yi tsaye yana bin anguwar da kallo haka kawai murmushi ya kubce masa, Salamar da ta doki dodon kunnensa ta saka shi saurin juyowa, Yau gashi ga kamilin datijon, datijon da yake jin muryar sa a waya, A lokacin da malan ya karaso inda Abdul ke tsaye kasa tsayawa kikam ya yi a gabansa kamar yanda ya saba, dan kuwa wani irin ni.imtacen kanshi ne yake bazawa gashi cikin wata farar shada an yi mata baban dinki gari da yar ciki, kansa da hula da carbinsa madaidaici a hannunsa mai kyan gaske, sai walwali yake na annuri yana karawa Gaba daya Abdul ya kai kasa dan gaisar da Malan, hakan ya sa sauranma zuba masa ido da mamaki, dan basu taba gannin haka ba, du girmanka har sai ya wani karkace zai maka gaisuwar raini sai gashi yau ya dukawa wani datijo Malan kam da ido ya bi shi yana murmushi, sai da ya amsa gaisuwarsa sannan ya mika masa hannu ya taso su kai musabaha ta kirki kafin Malan ya ce" *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, AKOY WA.INDA BASU DA ACCNT, TOH ZAKU IYA TURO DA KATIN KU TA NAIRA DARI BIYU, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida 7 *Free page* Ire iren abinda ke faruwa da rayuwar Abdul kennan, baya iya kwana biyu ba tare da mace ta zo ta sauke masa nauyin dake kansa ba , idan kuwa