← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 94

Sashe 62

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kali na tsayen Muryarsa ya dan daga dan zuwa lokacin ta ga dama ta kallo infa yake ya ce" tsakaninka da Allah da wannan tsatson tamkar zaka karye da kuma wannnan jar fatar taka uwa yumatir ne zaka zo ka tsaya gaban wannan yarinyar kanai mata bunsuranci kaima ga namiji ko? Yanzu kaima dan iska ne? Daga Hafsat har mutumen kallonsa suke baki da ido bude,.... Hafsat har sai da ta murje idannuwanta tana kallonsa, dama kiran da ya yi mata dan ya tardota infa take ne? Kanta ta girgixa ta kara dagawa mai taxi hannu aman ya fice ba tare da ya tsaya ba Abdul ya sasauta murya ya ce" Kauriyata mu je mana Dai da ta galawa motar harara sannan ta ce" wai kai haka Malan ya yanka min ragon sunna? Abdul ya kikifta ido yana kallonta sannan ya girgiza kai ya ce" aa Ta kebe bakinta gefe sannan ta kawar da kai Mai jan kunnen nan da wani mamakin kuma ya kalli Hafsat, gannun kamar fitsara ce ta yiwa wannan fitsararan aman ya bata amsa a sanyaye Ki shigo mu tafi kin ji? Abduk ya fada cikin muryar rarashi da kwontar da murya Motar ta karewa kallo, sannan ta shagwabe fuskarta ta ce" ni aa, ka je kawai Fuskar ya kurawa ido dan ta yi hakan ita kanta bata san ta yi ba aman ba karamin kashe shi abin ya yi ba, Motar ya shiga citewa a ky sannan ya ce" idan baku shigo ba, na rantse zan fito na dauke ki na saka ki a motar nan bayan na fafala maki mari Hafsat ra kale shi da kyau ta ce" Malan fa? Ya hana ni shiga motar karti! Sai da ya zazaro ido sannnan ya yi murmushi ya ce" daga wajen malan din nake Maman malan A hankali ta faga kafarta ta nufi mitar cikin nutsuwa ta bude ta shiga ta zauna Mai siyar da shadojin nan na tsaye yana kallon ikon Allah yau ya hadu da tantiran da suka fi shi iya shegantaka har Abdul ya tayar da motar ya harbata bakin titi Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" gaske kike dizga maza! Abdul na fara tafia ya juyo ya kali Hafsat, bata ankara ba ta ji ya saka yatsarsa ya lakaci man leben da ta goga a bakinta, Kansa ya girgiza ya ja tsaki ya ce" kema yanzu sai kwaliya da saka kaya masu maki kyau dan ki yi samari ko? Samarinma maimakun ki sami jarumi ingarma aa sai wannan lange langen tamkar igiyar leko? Hafsat kin ji kunya, kin ji kunya kin kara jin kunya! Hafsat ta lumshe idannuwanta tana jin yannayin wani iri, Abdul ne ya dawo niger da zama? Shine da walwalarsa? To aman yaya ya yi da damuwar Muhammad? Yaya ya yi da Muhammad? Abdul ya kaleta ya ga shi ke haukansa ita batama san yana yi ba ya girgiza kai daidai sun tsaya a danja ya yi shiru Hafsat ta karkato ta kale shi a hankali ta ce" me ya sa jiya ka min magana kuma ka min banza a waya? Sannan wama ya baka number wayana ne? Abdul ya juyo yana kallonta ya ce" number wayarki satowa na yi a wayar malan a lokacin da zai ja salar juma.a ya banu komai ajiya ni kuwa na koma gefe na sata! A jiya kuma a daidai lokacin da muke magana da ke madame ta farka, tana farkawa ta jefo min kallon kauna, lokaci daya na rikice na fita a hayacina, kin san lafia idan ta yi yawa , ga na koshi, a hankali na kamo matata na kwontar na..... Niyar Abdul fayace mata abinda ya yin sai horn din mutane ya saka shi waiwayawa ya ja tsaki ya tayar da motar ya kara daukan titi a nitse yana tafia a hankali Cikin nutsuwa Hafsat ta ce" sai mun biya ta chateau 9 na kai dinkin Aunty Kansa ya gyada mata ya dauki hanyar chateau noeuf din, aman yana tafe yana neman fitina yana takalarta rigima ita kuwa ta yi malakas tamkar ba ita ba Sai da suka tsaya wajen dinkin ta sauka ta nufi ciki a ranta tana girmama girman masifar Abdul, wai yaushema ya zama haka ne? Wato duka kaf masifar da yake era mata ne yake sauke mata a yanzu, to wai inama tuwansa ne? Ita kam ta ga ta kanta A lokacin da ta bayar , Nadiar ta umarci daya daga cikin yarenta fa ya dauki awon yannayin jikin Hafsat, Dan kwalinta ta warware dan ta ce a yi mata baban wuya sosai Daukan abin awon ya yi da litafin rubutawa ya zo da nuyar dauka sai ji suka yi Nadia na gaishe shi ta mike da kanta tana tambayar dinki aka kawo ne? Kallonta ya yi yanda man shafe shafe ya bi ya kokona mata fuska, shagon cike da karti sai dinki suke da wasu irin manyan yan mata irin yan dunuyan nan kowace sai fama take da atach cike a kai ya kada kansa sannan ya kaleta ya ce" ke baki iya aunawar bane zaki saka wannan ya dauki awonta ko ita tace sai namiji? Kallonta ta kai wajen da ya nuna, da sauri ta ce" yi hakuti oga, Sannan ta karasa ta karbi abin awon ta shuga auna Hafsat da kanta Sai da ta gama Hafsat ta tambayi kudin, nan ta yanka mata tsada sosai na dinkin nasu ita da auntynta , dan haka ta buda jakarta ta ciro kudin ciki baki daya ta mika mata ta ce zata kawo sauran idan an gama Yana tsaye yana kallonta har ta gana ta fice ta shiga motar kamar ta zabga masa mari dan haushinsa take ji sosai, Daya daga cikin yaran ya yafito ya juya shima ya buda motar ya shiga, Cofre ya ja ya janyo yan jika goma goma har kwaya takwas ya mika masa ya rufe motar ya kana hanya Yana kama hanya Hafsat ta kale shi ta ce" Abdul, ya isheka haka ka ji ko? Mme ya shafe ka da dinkina ne? Makan da zaja ringa yi min ihu a ka wai yarka ce ni? Haba haba, kuma walahi idan ba.a yi min wuyan da na zaba ba ba zan saka shadar ba, kuma sai ka mayar da ni ma karbi canjina dan ban iya almubazaranci ba! Satar kallonta yake yanda take daga murya tana dukan cinyarta wai ita nan tsakaninta da Allah masifa take masa? Bakinsa ya hade sannan a hankali ya ce" kin zama fitsarara kin gama! Hafsat ba dai ni ba ko? Ni dai ne ko? Na ji Shiry ta yi tana kikifta ido tana kallon hanya har suka shigo anguwarsu, Suna shigowa ta sasauta muryarta ta ce" Abdul, dan Allah ka ajiye ni a nesa da gida na karada gidanmu a kafa kar a je wani ya ga an ajiye ni a wannan motar a ci gaba da jifana da munana kalmomi fa munanan furuci ka ji? Kallonta ya kara yi, yanda ta marairaice, wani tausayinta ne ya ji ya tsirga masa, dan haka ya fage gudun aman bai tsaya ajiyetan ba Tun tana kallon kamar zai ajiyeta har ta ga ya iso lusan gidansu, Sai da ya tsaya kofar gidansu ya danna horn Wangame get din gidansu aka yi dan ana tunanin malan ne zai sako motarsa, sai dai gannin wannan wuleliyar mota ta saka mai budewar kansa yayansu tsayawa yana kallo A hankali ya ja motar ya shige cikin gida da ita, Motar ya tsayar yana kallon yanda du ake lekowa ra taga ana kallon abinda ke faruwa Tsoro ne karara ya bayana a fuskarta, harma wata kwallah ta tarun mata a idannuwanta, kallonta ta kai wajensa a hankali ta ce" ka san a zaginsu wanda ke tayar min hankali har nake tsoron wataran su kaini bango? Bama son suna saka mahaifiyata a shirmen su, idan sun yi kirana da karuwa shin du lalacewar uwa zata aiki danta ya je ya yi karuwanci ne? Abdul me ka yi haka? Yaya zaka sako ni har cikin gidanmu da irin wannan motar? Wa zai ki yarda cewa ni karuwa ce? Sai fa ya rintse idannuwansa sannan ya bude, bai taba tunanin hannunsa zai kai jikinta ba sai yau, dan kuwa hannunsa ya daga ya tsinka mata marin da ya sakata saurin saka hannayenta bibiyu ta rufe fuskar cike da tsoro tana kallonsa Sai da ya daki kujerar motar hakan ya sa mitar ta dan motsa dan gaba dayansa ya girgiza Yatsarsa ya nuno mata da kakausar murya ya ce" ba zan lamunce wani ya kiraye ki da wannan sunnan ba tare da na halaka shi ba kafin ya gama furta kalmar karshe! Kin ci sa.ar ke ce, kema kuma na farko ne! Walahi Hafsat Muhamadu kika kuma kiran kanki da wannan kalmar sai na cire harshen daje cikin bakin ki na cinye, idan kika kuma sai na lalata maki rayuwa ta hanyar hana ki farin ciki, Hafsat Allah ya isa idan kika kuma kiran kanki da wannan kalmar, na tsani wannan kalmar ga makiyina bale wace na fi a duniya! Motar ya bude ya saka kafarsa waje daya, har jikinsa rawa yake dinkin kaya blu fin shada ce a jikinsa harda hula ta mugun karbarsa Har ya juya zai fita ya dawo yana kallonta ya ce" dama motar malan ce da aka kawo, idan kin yi niya ki fito ki shiga ciki, iran baki yi niya ba ki zauna ki dawama a nan! Da kallo ta bi shi har sau da ya fice yayansu na kallonsa sannan ta lumshe idannuwanta hawayrn suka shiga bin kuncinta, A hankali ta waiga nan gabanta ya kara bugawa dan gannin du sun firfito sunna tsaitsaye ba wanda babu cikin matan gudan da yayansu ciki kuwa harda bakuwar kanwar aunty amarya Jikina ne ya dauki rawa gannin mamanta na nufo motar..... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA
Chapter 62 · 0% Book details