Sashe 20
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta daidaita lumfarfashin da take kafin ta bi jikinta da kallo, du sun ji mata ciwo, bama fuskarta du sun kumbura mata gefen ido ne, baki ne, ita dai halitarta suka canza mata a dan kankannin lokaci, Rarafawa ta yi ta karasa kusan tsohuwar dake taimaka mata da ruwa , Tana zuwa kuwa tsohuwar ta kare mata kallo, Kanta kawai ta girgiza ta mike daga alwalar da take ta kwonce canji a bakin zaninta ta je wajen wanda ya siyar mata da ruwan ta karbo wani ruwan ta kawo ta mikwa mata sannan ta juya ta tafi dan gabatar da sallah, Jikinta na rawa ta fara kuskure bakinta ta sha ruwan sannan ta dadarwaye jikinta, nan wajen dai ta samu ta kare gabanta ta yi tsarki, ta kara wanwanke inda fitsarin Eliz ya taba sannan da dan sauran ruwan ta yi alwallah ta fito ta nufi ciki inda kowa ke binta da kallo sunai mata dariyar shakiyanci da nunata suna kiranta jaka dan kuwa ta zama jakar zama daketa ne a kulun ya fi a kirga, Salla ta gabatar a nitse, duda suturar jikinta bata da nutsuwar, Tana gamawa ta daga hannunta sama ta shiga karanta rabanoni, Ba ruwanta da yanda wasu ke kallonta , ba ruwanta da kyamar da suke nunawa adininta, domin diyawa basu da adini ma , Sai da ta gama a fili sannan ta shiga adu.a a zuciyarta kamar haka" Allah, ka yafe min, ya Allah ka yafe min, ya Allah ka wanke ni, Allah ka rufa min asiri kar na komawa iyayena da tabon gidan kaso, ya Allah kar ka basu ikon cin mini, ya Allah ka shiryar da du wani mai irin halina, kar ya tsinci kansa a irin rayuwar da na tsonci kaina a ciki, KUTKALE ko fita ka yi dan guduwa baka da hanyar bi bale ka kai kanka gida, Kutkale gidan kason masu mumunan laifi, yai gani cikinsa, ban kashe ba, ban birne ba, ban ci kudin wani ba, na tainci kaina ciki sanadiyar rashin jin maganar iyayena, Sai da ta nisa kafin ta ce *Mijin da suka aura mini*, Ya Allah ka.......... Bata karasa adu.ar ba ta ji an doke hannunta, cikin hargagi ta ce" dan ubanki jiya ki rasa wanda zaki bi sai Usman? Du mazan gidan nan ki rasa wanda zai zaga da ke sai saurayina? Shigiya mai fata kamar ta bunsurun dan akuya! Usman ya fi karfin uwarkima ba ke ba! Hannunta ta kuma dagawa ta karasa adu.arta da gagawa ta shafa, daidai lokacin ta fincike mata dan rufar kan nata da ta yi salar da shi, Mikewa ta yi da sauri ta warce abin, domin shi kadai ne da ita da shi take sallah, Wurgawa tsohuwar nan dake girgiza mata kai ta yi , bata tsaya wata wata ba, bata dubi irin raunin jikinta ba, bata karya ba, daman jiya ta kwonta bata ji ba, ta ja tirjiya kafin ta yi ciki da abokiyar fadan nata suka je kiiiii suka fada cikin tabo da kwatar dake wajen...... *WACECE WANNAN?* *ME YA KAWOTA PRISON?* MENENE MAKOMARTA? KU BIYO NI, DAN JIN ME KUTKALE YA KUMSA? *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 2 Tana kokarin tayar da mashin din ta hango wani irin mutun, Mutun ne zabaya namiji kuma wada , Kai ba dan ba dan ba sai tace ko ta yi gamo ne? Dan kuwa mutumen tsayawa ya yi yana kallonta kamar ya ga bakuwar halita Adu.a ta yi sosai ta tofa masa yana kallonta tana kallonsa, Gannin ya ki motsawa ya kuma kin yi mata magana ya sakata saukowa a hankali ta nufe shi inda gabanta ke luguden kida Tsayawa ta yi dan nesa da shi ta yi salama, Ga mamakinta sai ta ga ya matso kusa da ita sosai Sai da ya daga kansa ya kaleta domin ya matso kusa da ita kafin cikin muryarsa dake nuni da manyantakarsa ya ce" ke kuwa, kin ari musulunci ne ko musulmar ce ke? Kanta ta sada dan kallonsa da kyau itama kafin ta ce" kama gare su ne musulmai ko salamana ne bai cika ba? Kansa ya gyada kafin ya juya da niyar tafiyarsa , Gane hakan da ta yi ya sakata matsawa da sauri ta ce" dan Allah, ka taimake ni, ina son sannin waye Muhammad bine Abdul Basid Abdallah? Ko zaka iya kai ni inda yake? Sai da ya kare mata kallo sannan ya ce" ki je dare ya yi, ki dawo zan kai ki wajensa, aman yanzu akoy nisa ga kuma dare Ta so ta yi magiya ko zai saurareta, sai dai gannin bashi da niyar hakan ya saka ta juyawa ta hau mashin din ta tayar ta dauki hanya wanda a lokacin tuni isha ta kawo kai, a kadan zata iya kaiwa awa uku ko zata isa Gudu kawai take yi, gashi a lokacin da zata bar gidan Abdul sai da ta ajiye du wani abin aikinta da zai bada damar a san inda ta nufa, ta tabata yanzu an farga da bata nan, fatanta kar ta kai BS bango ya dauki mataki a kanta ya kawar da wani gudun bacin ranta ya saba mata! Ta jima, ba karamar wahala ta sha a hanyar ba kafin ta karasa anguwar, a haka har ta karasa kofar gidan Tun daga irin kallon da sojojin ke binta da shi ta dan sha Jinnin jikinta, sai dai bata saka komai a ranta ba ta samu ta shigar da mashin din ta karamar kofar sannan ta sauka ta shiga tura shi ta ci uwar tafia kafin ta karasa farfajiyar gidan Dare ne, aman ko.ina ya dauka da hasken fitila , hakan ya saka du wani mai motsi ana iya ganninsa da dukan abinda ke tare da shi Tun da ta shigo gabanta ya yanke ya fadi, dan kuwa du wani bodyguard da ya kwana ya tashi a gidan yana tsaye cirko cirko , BS sai doka waya yake haka kuma sai duba agogo yake, gefe kuwa Abdul ne tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa ya zubawa hanyar da ta fito ido Turus ta yi da babur din gannin yanda BS ya nufo inda take tsaye gadan gadan ta tsura masa ido sannan ta sadakar cewa idan ya zo yana iya dauketa da mari BS na karasowa hannunta dake rike da mashin din ya damka yana dubanta ya ce " ina kika je? Ke da wa kuka je? Me kika je yi? Bakya tsoron wata fitina ta same ki? Idannuwanta ta kikifta tana kallonsa, A hankali ya sasauta damkar da ya yiwa hannunta ya rage ihun muryarsa ya ce" baki damu da damuwata ba? Ya dace ki damu da aikin ki, dan wanda ya dauke mu ya san takun mu Yawun bakinta ta hadiye a lokaci guda kuma ta dan leka bayansa, Ido hudu suka yi da Abdul sannan ya juya ya shige ciki ba tare da ya ce da kowa komai ba Sai a lokacin ta jinginar da mashin din dake kauri ta ce" BS, ka yi hakuri, na gaji da zaman waje dayan ne, shi yasa na fita na sha iska Hasana dake tsaye ido ta zaro tare da fadin" me? Ke kina da hankali kuwa? Ke Bodyguard har wani lokacinki gare ki bale muradinki? Ki dubi idannuwan mutane ki ce wai kin tafi shan iska? Ba laifi, tunda kin shawo iska sai ki zo ki zagaye balbalin gidan nan sau hamsin! A tare suka dubeta, daga BS har Hafsat, Hafsat kam dukawa ta yi ta kara gyara takalmanta sau ciki sannan ta cira da gudu da daren nan ga tarin gajiya , ga yinwa, ga bukatar yin wanka ta shiga gudun punishment domin kuwa Hasana dai ta isa ta sakata ko ta hanata a bangaren aikinta dan gaba take da ita ya zama wajibi ta yi mata biyaya Hannun Hasana ya damka ya juya da ita da wani irin karfi ya hankadata gefe inda ba za.a iya hangosu ko a ji maganarsu ba ya ce" ke a wa zaki shiga hurumin da ba.a saka ki ba? Ina ruwanki da amsar da ta bani? Ke idan a halayanki zan bi ki kina tunanin zan bar ki ki numfasa ne? Bayanta da ya buga da bango ta dafe kafin ta ce" BS , saboda na hora yarinyar dake kokarin rainaka a gabana ne kake wulakanta ni haka? Menene tsakaninka da ita? Wacece ita? Me ya sa na ga du kuna wani rawar kai a gabanta? Idan tana zagayawa da wancen da muke yiwa aiki kaima kwoncin kake da ita ko? Cikin daga murya ya ce" ki rufe min baki da fadin magangannun da ba tsari a nan, Kin ga yarinyar can da kika raina? Ni ita nake so, kuma ki daina kokarin zaginta dan ko daya , ba irinki bace, yanda take jana a kas ya saka nake kara mutuwa kanta, ta san ina sonta, har yanzu ta kasa so na, dan haka ki girmamata kar ki yarda ki mayar da ita abokiyar gabanki , dan na rantse maki ta ishe ki tuwo da miya Sosai magangannun nan sukai mata zafi, tana dafe da bayanta ta ce" aman ka san da ni kake soyaya ko? Kuma ka san aikinka ya haramta maka soyaya da dalibar da ba.a yaye ba ko? Sai da ya shafa gaban goshinsa da sankon kansa sannan ya ce" to ki tona, ke bari ki ji, abinda zai hana ni samunta daya ne, idan ta