Sashe 67
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kin yi kyau Bakinta ta turo ta ce" ba mun yi fada ba, shine ba zaka bani hakuri ba? Abdul ya tabe bakinsa ya ce" shikenan kulun sai na ringa baki hakuri bayan nine yayanki ke kuwa kanwata? Kanta ta juyar gefe sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta shiga dan jefa kafarta daya tanai mata gaba da baya a hankali Kafar ya kaiwa idannuwansa kallo, yatsotsin kafar sun sha jan lale faratunan kansu sun sha jan lale sun yi tsaf da su, Hafsat ba dai tsafta ba A hankali ya dan daga kansa har zuwa fuskarta, ya ga utama shi take kallo irin kallon kurullahn nan Girarsa ya daga mata a hankali ya dan kane idonsa guda ya ce" kallon fa? Ko na maki ne yarinya? Bakinta ta tabe a hankali itama ta ce" kallon fuskarka ne nake, cike da kamala kamar ba kai ba idan ka tafka tsiya wai Abdul ni zaka zane yayana? Kuma ka fadawa malan kiri kiri Baya ya yi ya jijgina da kujerar da yake sama ya ce" ai kece yayanki, ni kuwa na girme shi, kuma ni ba soyaya nake da ke ba bale na kama kafarsa kar ya hana min , ke kanki dan bana iya dukanki aman da ina iyawa na fara kwalo da ke Hafsat sai na kwonce maki kusoshin kai kwaila kawai! Idannuwanta ta zaro waje ta ce" ni ce kwailar? Abdul ya ce" eh ke din, Haushi ya kama ta, zata rama wayarta t shiga kuka, Tana gannin sunnan BS ne ta gyara zamanta ta daga kiran Sosai ta sanyayar da muryarta ta amsa masa, Cikin nutsuwa ta shiga baiwa kowace kalma tasa mahinmanci tana sauraronsa Irin yanda take wasa da idannuwanta da kuma lebenta ya kurawa ido, Mamaki yake irin yanda take zance da Bashir, Mikewa ya yi a hankali ya duka ya dauki kys din motarsa da ya yar wajen mikewar , Bai kuma koda kallonta sau daya ba ya juya da niyar tafia Tana nan zaune tana kallonsa har ya bar wajen kafib ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya, ita kam a kulun tana tausayawa matarsa, zama da abdul wani gagarumin hore ne da za.a baiwa bawa kafin ya mutu bisa laifukansa , shi bakinsa ya kunshi abubuwan haushi da takaici! Ranar juma.a, Yau ne ranar da ya dace a karbi auren Hafsat, wace malan ya yi nuyar idan sun zi zai fada masu a yi abin a kusa kusa, kai shifa idan da hali sai ya daura mata aure a yau din nan dan bai ga me zai ci gaba da jira ba shi kam a shirye yake dukan abubuwan da za.a yiwa yar gata ya tanadarwa mamansa sai dai idan fangin mijin nata ne basu shiryawa hakan ba........ Bayan sallar juma.a, sanye suke cikin shiga ta alfarma, a yau shi kansa Abdallahn ya saka manyan kaya na gani na fada hakama malan ya saka fararan kaya sai murmushi yake cikin nutsuwa Manya manyan tabarmi aka shinfida a kofar gida, aka ajiye kujeru inda anguwa ta dauka cewa Malan zai bayar Da Uwar malan a karo na biyu, hakan ya sa du wani mai jin kwakwaf ya hakarta a wajen mata kuwa suka ringa shiga cikin gidan, masu zuwa dan zumuncin Allah da taya murna ma du sun halara sai gashi kamar da wasa gidan malan da kifar gidansa yana neman mugun cikar da ba za.a iya saka tsinke ba Zaune suke Malan sai Abdul a gefensa na hagu sai aminan malan a na dama, a kan tabarma daya, sai sauran tabarmin du mutane ne a zazaune ana ta zaman jiran zuwan angwaye Ana zazaunen nan awa daya ta shige, ta biyu ta shige, Abdul da malan na yawan duban hanya, A haka lokacin sallar isha.i ta yi, aka ringa fitar da butoci kofa dan yin sallah wa mutane, nan suka ringa dauka suna alwallah karshe dai aka gyara tabarmin malan ya ja sallah Ana salame sallah malan na kallon waje daya, idan ka bincika zuciyarsa zaka ga tana dokawa fiye da yanda ya dace ta doka Abdallah ya mike ya fita daga cikin mutane ya ci gaba da neman layin BS, dokawa yake, layin na ringin sosai sai ya kusan tsinkewa sai a latse shi a kashe kiran, Zuciyarsa ce ya ji ta fara daukan zafi, a haka ya nemi number GN, shima ya yi ta kira aman shiru tasa bata shigama bare har a daga Dawowa ya yi yana gannin yanda ake binsa da kallo, ya ratsa ya shige cikin gidan malan Yana zuwa ba ruwansa da yanda ake binsa da kallo ya samu ya ratsa matan nan da suka cika tsakar gifan ya shige bangaren mama Yana zuwa bai tsaya wata wata ba ya shige ya karasa inda mama take zaune saman kujera, gefenta Hafsat ce nanade da lafaya ruwan maroon ta dukunkune kanta sai sauke ajiyar zuciya take, sai yan uwanta mata uku ciki harda aunty suna zaune jigum jigum Karasawa ya yi inda mama a Ke zaune ya tsuguna a gabanta hakan ya saka du suka juyi suna kallonsa banda Hafsat da ta kara labe kanta a ranta tana fadin yau Abdul har a dakin mamana ya shigi ne ya mun jan ran ko? Na shiga uku kar dai da gaske malan har ya daura min aure? Kafin Abdul ya yi magana , muryar hajia mama uwar gidan aba ce ta karade gidan da budar da sai da ta baiwa mutane mamaki, Mikewa ta yi tsaye ta daga murya ta ce" kowa sai ya kama gabansa, ai ba yau aka fara ba a tara jama.ar da ba.a taba tarawa ba dan yar gwal aman a kwashi kunya, Daurin auren da aka so a yi daidai salar juma.a dan a samawa yar albarkar juma.ar sai dai Allah ai ba lale ya yi maka abinda ranka ke so ba dan kai ka bambanta abu kana so na daya ya fi na kowa ai Allah ba zai yarda a yi haka ba, mata ku watse kowace ta je gidanta ta dora sanwa an fasa auren uwar malan yar gwal domin da za.a daura da an daura shi! Hehehe dadina da gobe saurin zuwa, ba zaka je ka gama yawon ta zubar dinka ba kuma ka dawo a rurufe a yi maka gata duka Allah na kallonka ba! Nan da nan yar hayaniya ta ringa tashi, kowace na tofa albarkacin bakinta wasu na tambayar da gaske an daina? Dama wai wa zai kwashi saura? Abubuwa dai babu dadin ji Da sauri ta bude lulubar da ta yiwa kanta, yar rigar cikin lafayar ce kawai ta yi saura sai na tsatsonta dake nanade, Dubanta ta fara ajiye kan mahaifiyarta dake kokarin jan hijabinta da kyau ta kara rufe fuskarta dan bata so a fahimci halin da take ciki Da sauri ta kai dubanta wajen agogon bangon dakinsu, har magariba ce ke neman yi, Dubanta ta kai wajen Abdul ta ga ya kama hannun mahaifiyarta yana magana kasa kasa sannan ira kuwa tana gyada kanta a hankali, Wajen yan uwanta da suka nufota ta kai dubanta , da sauri ta diro daga saman bed din ta kali auntynta ta ce" aunty, ina wayana? Bani wayana dan Allah Auntyn tata ta bita da kallo sai dai bata bata wayar ba Muryarta ta daga ta ce" aunty wayana nake tambayarki aman kin zura min ido? Ki bani wayana Cikin daga murya mama ta ce" uban me zaki yi da waya? Da sauri ta juyi wajen maman nata, kafarta ta daga ta karasa wajenta Abdul ya dan ja gefe daya, tana zuwa ta kama hannun maman ta ce" mama, zan yi kiran Bashir ne, na tambaye shi lafia suka yi dare haka? Mama kin ji abinda hajia ke fada wai an fasa aurena? Mama bani na kitaye shi ya zo a daura min auren nan ko zata ji kunya ta shafa min lafia, mama na rantse da Allah ba karuwanci na je ba, ni ba yar bariki bace, ban yarda na zubar da mutuncina ba, kuma Allah bai basu ikon zubar min ta karfi ba Dubanta ta kai wajen Abdul da sauri ta damko hannunsa na dama ta rike gam a hannunta ta ce" Abdellah, ka saka su bani wayata na yi kiran shi, maza ya zo da sauri kar dare ya yi, ya zo a dauran aurena , kai ka san yana so na ko? Kai ka san ya fada min shi koma me ake kirana ko ake kalona da shi yana sona a haka, kuma a dazu muka gama waya da shi da sasafe, da sasafe sai da ya fadan yau zai kawo kudin aurena Abdul, ko bashi da lafia ne? Ko bashi da kudin ne? Ka bashi ya aure ni ka ji? Idan bashi da lafia ne a kai ni wajensa ka ji? Hannunta da ta rike shi ya bi da kallo, kafin ya kai kallon nasa wajenta, irin yanda ta rikice take sakin zance na bata cikin hayacinta Aunty ya kala hakan ya sanar mata fa yana so ta kamata ne, Mikewa aunty ta yi ta riko hannunta sai dai maimakun ta sake shi sai gaba dayanta ta afka kirjinsa ta rukunkume shi tana wani irin jijiga shi gaba daya ta yakune masa gaban rigar tasa shadarsa mai ruwan sararin samaniya du ta aniya yakuneta tana jijiga a kirjinsa tana maimaita ya kira mata Bashir tana son magana da bashir! Da wani irin karfi ya cireta a jikinsa ya dauketa cimak ya direta saman bed din da take a dazu kafin ya juyo ya kali yan uwanta irin yanda du suka fita a hayacinsu tsabar tashin hankali sai mahaifiyarsu dake zaune kanta a kasa bata dago bama bare a fahimci halin da take ciki Bakinsa ya buda da kyar ya ce....... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct