Sashe 21
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce da ni Bashir ka barni haka, bana son ka! Yana gama fada ya juya ya fice ya tsaya can gefe yana hangen yanda Hafsat ke gudu tana raba hanya, Kwarai yana da damar hanawa, ya isa ya hana dan shima yana matsayin gaban Hasana, sai dai ba zai shiga ba ko dan ya kori tsargi sannan ya rike girmansa a wajen yarensa, tausayinta yake ji, kaunarta yake yi, ji yake dama zai karbar mata gudun! Abdul dake tsaye kusan windows din dakin Muhammad ya rike dan labulen ya tsura mata ido yanda take gudu, Muhammad na yi masa magana shi walahi kwata kwatama bai san me yake cewa ba, a haka ya juyo ya ce" *daga ina take?* Muhammad dake dana waya yana nuna masa sabuwar motar da kanfanin Helix suka kera wace ke da tsananin tsada ya dago yana dubansa Sai da ya matso inda yake tsaye ya ce" wa kake tambayar inda ta je? Sai a lokacin Abdul ya farka, tamkar an dan tsikare shi ya dubi Muhammad da kyau, sai kuma ya shiga takawa ya ce " ina zuwa....... A wannan dare haka kowa ya yi barci zuciyarsa a cinkushe, tun daga Abdul, Ni.ima, Hafsat, BS , Hasana, da du wani ikon dake gidan wanda sanadiyar rashin gannin Hafsat da tabatar masa cewar ta fita a mashin ya saka tayar masu da hankali da rantsuwar su saurari du irin abinda zai sameta walahi da hannunsa zai masu! Hakan ya saka du suka firgice suna masu jin haushin juna da jin haushin wanda ya ara mata mashin din Ko da safe ba wanda ya shiga sabgar wani, kowa bakin aikinsa yake tun safe har yama, Ko da yama ta yi , yauma fitowar ya yi , sai dai yau wani bakin yadi sidik ne ya saka ya fito ya nufi wajen shakatarwarsa A lokacin da ya zauna ya mike kafarsa ya kali BS dake kai kawo ya ce" ka ce da dayar nan ta fita can baya ku kuwa ku zo kai da wancen ina son gannin ku A nunin da ya yi, yana nufin a cewa Hasana ta fita, su kuwa ya nuna su zo saman kujerar dake kusa da shi yana son gannin su Abinda ya bukata BS ya aiwatar, inda suka zauna a kujerar dake gabansa su duka suna kallon yanda ya tsura masu ido ya kalli wannan ya kalli wancen Sai da Abdul ya gama kallon su sannan ya ce" *wai ku yaushe kuke zance ne? Wace irin soyaya ce kuke haka bakwa bata kulawa? To yau ku yi zance!* Sai da suka kalli junna sannan suka kale shi a tare tamkar hadin baki, BS ya dan gyara zamansa yana kallon Abdul, Abdul ya girgiza kai ya ce" kai yanzu, katoto da kai, kake jin tsoron wannan yar yarinyar? Bashir maza ka rako duniya ko me? Ka fito kace da Hafsat cewa kana son ta aman sai ka ringa hauka har kowa ya gane kana sonta ita ka kasa fada mata kiri kiri? Sai da BS ya mike tsaye, sai kuma ya koma ya zauna tamkar an dangwarar da shi yana zare ido yana kallon yanda Abdul ke kada kafarsa dake wanke tas tamkar a side, A haka ya bi shi da kallo har fuskarsa, kai shi ko a lakuru bai ga kwalon dan duniya irin Abdul ba, Dubansa ya maida wajen Hafsat ya ga ta tabe bakinta ta dafe gaban goshinta, kuma abinda ya bashi mamaki bai ji ta yiwa Abdul ihun kar ya yarda ya kama sunnanta sunnan mahaifiyar malan ce, ohk wato sai su da aka raina ko? Katse masa tunaninsa ta yi ta hanyar fadin" *ABDUL* idannuwansa ya dauke daga duban gefen da yake , ya saka cikin idannuwanta har da takabe kumatunsa yana kallon yanda ta kankance idannuwanta wai kennan zata yi jaraba ko? Dubansa ya kai wajen BS ya ce" Bashir, ko jaraba zata yi kyau take mata, bara ka ga yanzu ta ce" Abdul, menene haka? Ka bar mu mu koma bakin aikin mu.... Sai ta wurgan harara, sai ta mike ta tabe baki kuncinta ya lotsa , sai ta koma bayana ta yi tsaye ta hade rai dan Hafsat bata son raini! Kallon junna suka kuma yi , Nan Hafsat ta lumshe idannuwanta tana son tunanin girman rainin hankalin Abdul, Sai dai bai bata wannan damar ba ya katse mata tunani da fadin" kina tunanin zan baiwa soja mashin na kasa saka masa abinda zai nunan inda yake shiga? Hafsat me kika je yi cikin jejin da ba wani mahaluki dake rayuwa a cikinsa a sanina? Kina son na saka maki ido a motsinki ne? Shiru ya yi, kafin ya ci gaba da fadin" BS nah? Ka tambayi wajen wanda ta je dan ba zan lamunci hakan ba! Mikewa ya yi ya mayar da bakin gilas dinsa ya juya da niyar tafia, Sai dai sunnan da Hafsat ta ambata ya kusan tainke masa lumfashi, Wani irin ja ya yi ya tsaya sannan ya juyo a haukace ya....... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 1 A lokacin da suka fito gaba dayansu da yannayin na zakunna, kowane na jefa kafarsa inda ta je, suka tsaya gaba dayansu a tare sakamakon ganninta tsaye ta zuba masu ido su duka, Sai da gabansa ya yanke ya bada wani irin sautin da kunnayensa suka jiyo masa, Tsaye take kawai, hannayenta gaba daya a sake, wandon dake jikinta irin mai lafewa a jiki ne aman kuma sakake wajen mazaunanta kawai ya rike , sai riga mai botura da wata a ciki wada dalilin bale boturan da ta yi ya saka ake ganninta, kanta dauke da asalin gashinta ba wancen atach din ba, Fuskarta babu ko digon kwali bale a yi hangen hoda ko wani abin, Aman wani fayau da shiga ido da take sai a hankali, dole ta girgizawa namiji lafiyaye zuciya sai dai idan zuciyar taka na hangen wata sai ka kyasa a ranka ka huce wajen, Hannayensa ya daga ya cusa cikin gashin kansa da ya bar suma ta taru sannan baya gyarawa, Sai da ya dan waiwaya ya ga tsayuwar me kuma suke a bayansa? Sannan ya daga kafarsa ya tunkareta, Hannunta na dama ya damka ya jata tamkar rakumi da kala haka ta bi shi ba tare da ta warci hannun nata ba, ba kuma ta yi masa gardama ba, Da kallo suka bi su, inda BS ya daga kafarsa ya bi bayan su da saurin gaske, sai dai yana karasawa Abdul na banko kofar da wani irin karan sautin dake nuna halin bacin ran da yake ciki, Wani irin hankadata ya yi cikin dakin dake mamaye da duhu, wanda yake daya daga cikin dakunan gidan, shi kansa bai san ainahin inda zai je ya kuna fitila ba, sannan tun da ya hankadata yama rasa inda ya hankadata, Garu ya yi nufin kaiwa naushi, wanda sai da ya naushi iska sau uku kafin ya samu hannunsa ya naushi garun da wani irin karfin da da normal ne sai ya ji jiki ainun, aman da yake ransa bace ne sai ihun bacin rai da ya saki murya kausashe ya ce" me kika ji? Me ki ka ji nace? Inda yake kallo daban, inda muryarta ta fito daban, domin ita a bayansa take, a hankali, cikin mutuwar jiki ta ce" ina bayanka, Juyowa ya yi ya yi shiru, inda ya dauke numfashinsa, yana so dole ya lalubota ta habyar numfashin da take saukewa, Fahimtar hakan da ta yi ya sakata tsayar da numfashinta sannan ta canza waje da sauri ta saisaita ajiyar zuciyar da take yi, ta dan labe wajen labulen wajen ta ce" a wajen formation din zama gagarimin sojan dake aiki wa kasashen duniya baki daya, wanda yana da damar yin operation inda ya ga dama, yana da takardun shaidar shi dan kasar da du ya yada zango ne, shi dai wannan mutun ko shugaban kasa na mangarinsa domin ba.a bayar da formation dinsa a kananun kasashe sai irin su chaina, dubai, ko su Saudiya. Japan...da dai sauransu.... Wanda a cikin mutun hamsin bai fi biyar su fita ba, kai ana iya goge kowa a hanawa duka hamsin din! Sai kuma bodyguard , ana koya masa irin wannan abin a sama sama ba a zufafe ba saboda halin rayuwa...... Labulen da ya damka ne ya sakata saurin matsawa ta canza waje , Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta ce" a ciki.... *WANENE KAI ABDUL JABAR ABDUL BASID?* Gabansa ne ya wani irin bugawa sakamakon irin yanda ta ja sunnansa lokaci daya take neman sannin waye shi, a iya yau, a iya hafuwar yau, awowin da ba zasu fi goma sha biyu ba , wanda da yawa da suke tare shekara da shekaru.basu san hakan ba? Jikinsa ne ya yi la.asar, sanyi ya yi sosai da sosai, dan haka sai ya daina neman lalubo infa take ya saki abin sauraron da ta laka masa nan ya juya ya lalubi kowa ya bude ya fice a dakin, Bai yiwa kowa magana ba, sai dakinsa da ya je ya shige ya rufe , Bakin bed dinsa ya zauna ya dora kafarsa daya kan daya ya daga kansa sama, Wasu zafafan hawaye ne suka shiga bin gefen kumatunsa a lokacin da ya tuna mahaifiyarsa da irin rayuwar da ta yi cikin duhu, haka kuma irin mutuwar da kanwarsa ta yi, da irin rayuwar da mahaifinsa ya yi , Shi kansa