Sashe 68
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 5 *Yan uwa ya bakwa comment zaffaafa ne? Ko labarin ba siger ne? Haba kuma na fns, ina mugun yi da ku, ku kuwa kun daina bani comment zafafa? Idan har yanzu cikin sallah muke na dakatar idan aka gama shagulgulan sallah sai mu ci gaba Bakinsa ya buda da kyar ya ce" menene haka? Haba aunty, ku yi hakuri, zamu yi jiransa daga nan har karfe goman dare Yana gama fada ya juya ya fice , nan Hafsat ta kara mikewa da niyar dirowa daga bed din, sai dai kafin ta karasa hanzarin nan nata ta ji saukar wani gigitacen mari, Kuncinta ta dafe da sauri ta kali fuskar mahaifiyarta, sai da gabanta ya yanke ya fadi domin kuka mamanta ke yi hawaye ne sosai ke zuba daga gurbin idannuwanta Yatsarta ta nuna mata ta ce" binsa zaki yi? Kuma bace mana zaki yi? To ki je ANMIH! na ce sai ki tashi ki kara fita a irin wannan halin, ke dama zagin mutane ko magangannunsu ba damunki ya yi ba, sai ki mike ki je ki raba abin fadan kin ji? Zaki nuna min rashin hankali da rashin da.a ne? Ko kuwa tarbiyarki ce ta koma haka? Ke idanma wahainiya kike mai canza kala a dukan wani lokacin da ta yi niya dan ubanki a yau ba zaki je neman namiji ba, meye? Me kike tsoro? Me kike gudu? Menene baki gani ba? Shiru ta yi sakamakon kukan da babar yarta ta fashe da shi tana rike mahaifiyar tasu, Dubanta ta mayar wajenta, tanai mata kallon nan na abin tausayi Tana hawayen ta ce" baki koya mana daga murya ba, ki sasauta muryarki ummah, Menene bamu gani ba muka kashe muka birne tsakanin mu? Daga muryarki na iya tona sirrin mu, Ummah, rayuwa ce, jarabawa ba irin yanda bata zuwa, na sani , uma na san kina cike da tashin hankali yannayin rayuwar maman malan, sai dai kuma ina so mu zauna mu zubawa sarautar Allah ido, malan kanda ya yanke hukunci yi mata aure ne dan ya fitar da ita a gidan nan ko zata ji sanyi da ranta, A wajenmu ne take samu sanyi, ba zan yarda wajen namu ya koma ya zame mata gidan kurkuku ba! Ummah, ai maman malan ta yi sauki, a ganina an samu ci gaba a halayar maman malan Hannunta ta janye a hankali ta juya ta shige bayin dakinta ta dauro alwallah Tana fitowa ta dube su muryarta sanyi kalau ta ce" ku tashi ku yi alwallah, sallar magariba ake kira, kar ta shige Daya bayan daya suka ringa shiga ciki suna dauro alwallah suna fitowa domin sun kasa fita waje bale har su yi anfani da bayin wajen Ita kanta Hafsat alwallar ta dauko ta zo kusa da yan uwanta ta tayar da sallar magariba, Gaba daya ta cire du wani abu mai iya sakata kyalkyali ko annuri, Bayan ta gama sallah a hankali ta ja jikinta ta jingina da jikin gado ta kurawa waje daya ido, Tana jan carbinta tana tana kaiwa wayarta dake saman gado kallo, idonta na kara lumshewa tamkar zata fasa ihun kuka sai dai ba hali A haka aka yi kiran sallar isha.i, cikin gidan sai kakayatu ake magangannu sai isko su suke da shewa kala daban daban, sai dariya ake shekaya ana kashewa kowace ta sha ado ana buga waya ana fadin yau malan ke aurar da yar gwal aman ana jiran angwayen tun rana har yanzu basu karaso ba Dakin mama sun yi shiru, ba mai yiwa dan uwansa magana, suna lazumi dai kowa na neman sauki a wajen Allah Mama ce ta dubi yayanta baki daya, cikin murya a shake ta ce" dare fa na yi, ku tashi ku lalubi gidajenku mana Mariam? Nana Mariama ta dubeta, ta kai dubanta wajen agogon dakin , karfe tara da rabi ce ta yi, Mikewa ta yi a hankali ta matsa kusa da maman nasu da niyar yin magana Wata irin buda ce aka saki a tsakar gidan, buda mai karfin tsiya, buda ce irin ta harshen buzaye wace ake kada harhen ana ajiyewa ana kuma dauka ba tare da an sauke lumfashi ba Matar da ta shigo daga waje, wace take marokiyar anguwar ce, macen da ta zo tun da rana dalilin daurin auren aman gannin an fasa kamar yanda hajia mama tace kowa ya watse sai yan tsegumi dake lekowa jifa jifa suna jin kwaf suna fita A yanzu haka ta dawo ne sakamakon mai yar lasifikar da ya shaida za.a daura aure, Za.a daura auren Hafsat a irin wannan lokacin Ba wanda bai yi mamakin irin lokacin da angon ya saka ba, du mutanen dake kusa sun halarci daurin auren da ya gigita su, Hafsat? Yar gidan malan, yarinyar da ta kwashe tsayin shekarun rayuwarta tana rayuwa mai hatsari, rayuwa marar tsari, rayuwa tamkar wace ta fito a tsatson arnawan da basu san kalmar musulunci ba, yarinyar da baki da yawa a dazu sun ambaci cewa su sun zo ne dan ubanta mutumin mutane ne, sun zo ne dan kawai su amsa gayatar mai zuwa gayar mutane, aman kowa ya sani ko sadaka zai bayar da yar nan tasa sai ya hada da bada hakuri da jari harma da wajen zama, dan a yi hakuri a zauna masa da ita, yarinyar da ta sha marin saurayi? Daidaiku ne suka yi mamaki rashin zuwan ango a kan lokaci, sai dai daurin auren da aka kusan karfe goma na dare ya saka mutane da yawa mikewa tsaye daga zaunen da suke...... Dubansu du suka kai wajen mutumen da aka ce shi ne mijin Hafsat, nan yan kananun magangannu suka fara tashi, sai dai a lokacin da ya yi bayanin kyautar uwa da ta uba sai baki ya mutu, ya kasance du wanda suka yi ido hudu da shi sai dai ka ga ya sakar masa murmushi ko yana kokarin karasawa dan ya samu shiga a hankali aka fara canza salon zagi zuwa yabo, a hankali aka fara dan yaba magana cewa" ai ita uwar malan barta da fadanta, aman yarinya ce mai mutunci da mutunta wanda ya girmeta Malan dake zaune, zuwa wannan lokacin ajiyar zuciya kawai yake saukewa sannan yana bin mutane da kallo, a yau ya ga rana ta mamaki, rana wace a yau kawai Allah ya nuna masa mai zaune da shi dan rufin asiri da mai zaune da shi dan moriyar wani abin, Ashe dan adam yake? Marokiyar nan sai da ta ja ta tsaya ta kara rangada buda, Wani tsaki ne yayar su Hafsat ta ja, kafin ta ce" wai Ummah, ba za.a tsawatarwa mutanen waje idan na cikin gida sun zame mana dole ai banda na waje Maganar da marokiyar ta fara fada ne ya sakata katse maganarta, lokaci daya kuma ta zabura ta mike da niyar fita Hafsat da ta dago kanta da sauri, lokaci daya ta hango wayarta ta bada wani haske, Mikewa ta yi ta lumshe idannuwanta sai kuma ta bude tana dariya dariya hadi da kuka, irin emotion din nan, A hankali ta buda bakinta ta ce" ni na san wani abu mai girma ya tike shi, mama, na san zai zo komai dare, mutumen da ya gama min rantsuwar irin soyayar da yake min? Sai da ta gama maganar ta nufi wayarta, Dai dai nan marokiyar ta ce" *lale komai nata daban ne, tauraruwa ce yar malan, mai sa.a ce maman malan, uwar masu gida wanke ki bamu ko jikokinmu sa dauko wannan farin jini da farar sa.a, yau ku zo ku duka ku gaisar da masu garin, ta auru, uwar malan ta auru, sai da ta dandanje ta zabo dalele kakarfa, sai da ta gyagije ta dauko zakara mai takun zaki, to yaya zata yarda yan bukulu su gane mata shi bayan tanai masa takun kura wace safiya maraicenta ce? Ba fa dan iska bane dan baiwa ne, maman malan ki je da ni na zauna a gidan gilas domin ko a aljanna in sha Allah muna fatan Allah ya yi mana domin* Daidai nan du matan da suka rarage du sun halarta suna kallonta, kowace jira take, sauraro take ta fada mata sunnan mijin da take yiwa wannan uban kirarin sai kace wace ta auri dan shugaban kasa ko wani gagarumin dan kasuwa? Da sauri Nana mariama ta ratsa su, bata iya yiwa kowa magana ba famanta ta karasa wajen marokiyar nan, Tana zuwa ta ce " ladiyo, me nake ji kina fada kamar an dara auren maman malan? Bakinta ta buda ta ce" aure kuwa gangariyarsa, sanadiyar na rangada gidar daurin auren nan kin ga damin da ya bani angon da kansa Hajia mama da gabanta ke tsale yana wani irin dokawa, hankalinta a tashe ji take tamkar ta matse wuyan ladiyo ta matso ta ce" ke dallah rufe min baki, waye mijin wa sunnansa, waye shi a garin nan da zai iya daukan kyauta irin haka ya maki dan kawai kin yi murnar daurin aurensa da yar da ta gama yawo? Du kallonta mutanen wajen suke, dan sam bata iya ta rufe abinda ke ranta ba a irin wannan lokacin Sai da ladiyo ta rangada guda ta matso sosai kusa da Hajia mama ta ce" A daidai lokacin ne Hafsat ta dauki wayar andoid dinta kirar samsung ta duba message ne akai mata Buda message din ta yi tana murmushi dan ta tabata albishir zai mata ko ya yi mata barka Message ne kamar haka *zaki rayu kuwa da ni? Tsoronki nake, ina tsoron haduwata da ke, sai dai na ceci jin kunya da kuma kwana da zulumin malan, mama, su aunty da ke kanki, ki gafarce ni da kalmar da zan fada, aman daga yau igiyoyin aurena sun rataya a wuyanki, Hafsat U.R MINE* Wayar dake hannunta ta daki, lokaci daya ta kwala ihu ta silale nan kasa Su mama da basu bi aunty Mariama