← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 94

Sashe 50

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ta lumshe idannuwanta ta ce" BS, ka yi hakuri ka ji? A yanzu, babar damuwata shine na fita a aikin nan lafia na samu incina na yawo inda nake so a lokacin da nake so, na sadu da iyayena mu sansanta tsakanin mu, walahi na fada maka gaskiya rabona da na ji wai ina iya soyaya tun wace ta kai ni *KUTKALE* me ta anfana min ne soyaya? Ita ta saka na kara zama fitsarariya, dalilin soyaya na tarbi gaban malan gaban yayansa masu jin kunyarsa na yi tsalen albarka na ce" *Malan, ba aure zaka min ba? To sai na yanka mijin!* Haka ya bini da kallo da adu.a, na sha na tashi tsakiyar dare na ga mamana na tofa min adu.a, cikin ikon Allah sai na je na yi wanka wai na wanke adu.ar dan ta dankwafar da ni ne take min tofi salon a min auren ko yana wulakanta ni na zauna ko? To kar ta kuma min tofi! Dalilin soyayar nake duban du wani yayana da ya yi garajen tsawata min na lalaya masa maganar da zai ji ya tsane ni har karshen rayuwarsa, Dalilin soyayar na ringa kirta rashin mutunci da nake jin daidai ne, kaina daidai yake da na kowa idan dai za.a taba min abin so na! Wata alfarma ta yi min soyayar dake saka ni fita tsakiyar dare tare da kato mu je gidan rawa ni ba karuwa ba, ni ba arniya ba, ina kallo ana abubuwan da ba daidai ba aman a gobema na koma dan bacin ransa na nufin tashin hankalina? Ita soyayar nace dan ubanta me ta tsinana min bayan *bakin jini, hau, tabewa, shiga uku, rayuwar da ko a mafarki ban taba tunanin ganina ciki ba, wato rayuwa irin ta dakarun sojoji?* Tsagaitawa ta yi da maganar da take yi jin kanta na sarawa ta dube shi ta ce" ban ce bana son ka ba, ban kuma ce ina son ka ba, hasalima na mance kalar soyaya ne...ko nace na rasa sunnan da zan bata, *fara, ko bak'a* aa, *zaki ko madaci ce?* , *rayuwa ko mutuwa ce?*, a yanzu burina shi ne *ABDUL* ya rayu, ya fita a damuwarsa ko zai salame mu mu koma gaban GN ya bani inci cikake na arta a guje sai gaban Malan Shi kam du kallonta ne yake, wai bata soyaya? Wai ta daina so take son fadi? Shi kam ya kasa yarda, yana tsoron irin yanda kusancinsu yake da girma tsakaninta da uban gidansu ya girmami tunaninsa ya zarce mizanin dan bashi tsaro ne kawai Kansa ya kawar gefe, har tsakar ransa yana jin haushin irin yanda yake wareta ita kadai yana bata kulawa, du sun lura ba shi kadai ba irin yanda yake sakar mata murmushi ko idan ita ta yi masa tambaya zai tsaya ne ya bata amsa yanda take so , yana bata lokacinsa , har tsayuwa yake ya cire mata hular gashin dokin da take dorawa, yakan dora kujera idan sun biyo bayansa in ya zile masu ya zauna dangagal a matsayin da gare shi a dukiyarsa ya ringa binta da kallo tana faman kuftayar a saketa ta yi masa kashedin kar ya kuma yi masu haka, da an harbe shi fa? Me yasa hannayin damuwar da take nunawa ke birge shi? Ko meye hakan ke nufi? Ita kanta takan nuna bacin ranta da dukan karfinta tamkar an taba rayuwar wani na jikinta wanda take matukar so? Eh lale haka ake koya masu, ana koya masu cewar rayuwar wanda zasu je baiwa kariya ta fi tasu mahinmanci, su baiwa rayuwar girma su kareta da dukan karfin su, aman ita ta zurma da yawa, ta shiga da yawa, haka ake yi? Har ya mike, ya dawo ya tsugunna yana dubanta kafin ya ce" ki kwana lafia, ki kwontar da hankalin ki, in dai gidan nan ne za.a turo wa.inda zasu canje ku, domin kun ji ciwo ba zai yiwu ku ci gaba da aiki ba, a gobe gobe GN zai turo masu canzarku ke da Jibrin, a mayar da ke camps, hankalina zai fi kwonciya, ki je can ki yi jinyar hannun ki, idan kika warke sai a sama maki wata mission din mai sauki ki yi ki gama a baki damar fita inda kike so, a lokacin da kike so! Yana gama fada ya juya ya bar mata dakin cike da yannayin damuwa, da tsoron rasata, dan shi sonta yake , koma mecece ita sonta yake Da kallo ta bi shi, Ya Allah, hakane fa, za.a iya mayar da ita fa, shikennan yanzu ta sha bulley din banza kennan? Eh mana tunda dai wata mission din za.a kuma fitar da ita, bayan ta shiga wannan? Bayan ta sha wahalar nan maimakun idan an mayar da itanma a ajiyeta a matsayin ta gama fita mission da sunnan camps din sai dai a turata wata? Idannuwanta ta rintse tare da shiga tashin hankali, ita fa so take daga nan ta je camp a matsayin wace ta ci nasara ta samu incinta! A hankali ta buda idannuwanta ta shiga kokarin mikewa bayan ta kashe laptop din Fitowa ta yi ta nufi dakinsa kanta tsaye, Tana zuwa ta shiga bugawa, jin shiry ya sakata kara kunnenta, sai dai abinda ta dan fara jiyowa ne ya sakata saurin matsawa gefe tana mai jin gabanta na faduwa, Sai a lokacin ta dafe kanta da hannun da bashi da ciwo ta ayyanawa kanta cewa....kema baki da kai, a wannan lokacin kike tsamanin samunsa a hayacinsa? Zama ta yi a wajen, inda BS ya yi kai kawo ya fi a kirga yana aikinsa bai ce da ita komai ba, ya ajiyeta a zata yi ta gama ne, A kadan sun kwashe awa uku a wajem, daga masu baiwa Ni.ima tsaro, da BS da ita kanta, Suna kallon juna lokaci zuwa lokaci, suna jiran fitowar Ni.ima , kowa na kallon kowa da ido , basu da abin cewa, sunna zaune ne, kowa kuma ya san me ake yi a cikin dakin, basu da katabus sai ido, dan kuwa rabonsa da ya je dakinta tun da ya mayar da ita cikakiyar mace, ya kasance ita ke zuwa kowani lokaci ya bukaci hakan bisa abinda ya dora mata A lokacin da suka ji karan buda kofar kowa ya kawar da kansa sannan ya kimtsa kansa, BS kuwa murmushi ya sakarwa Hafsat yana mai yi mata nuni da ba ta gani ba? A lokacin da Ni.ima ta fito daga dakin ta yi gaba suka bi bayanta Hafsat ta mike ta nufi dakin da niyar shiga,. Damtsen hannunta BS ya rike ya saka idannuwansa cikin nata ya ce" zaki je ki wanke abinda baki saka bane ko zaki je ya gama koshi? Ki farka, ko aure yake ba zai aure ki ba! Hannunta ta fuzge daga rikon da ya yi mata, ta zabga masa wani harar tsana zata yi magana kennan idannuwanta suka sauka saman Abdul dake tsaye yana hangen su, Kwafa ta yi ta nufi dakin da niyar idan ta fito zata kirta masa rashin mutuncin da ba zai taba mantawa da ita ba Tana shiga ta rufe dakin ta yi tsaye gabansa, Da alama bai jima da fitowa daga wanka ba dan kuwa jalabiyar jikinsa na like masa a jikin, Kawar da fuskarta ta yi dan ita ta tsani wannan kallon rashin kunyar da yake yiwa mutane, sam bai iya kallon adini ba! Ba wani kwane kwane ta ce" *Abdul, ka hana a tafi da ni gobe, dan Allah Dan karamin tawul din da yake tsane kansa ya dan yarfe ya matso kusa da ita a hankali ya ce" kin shaku da dan baiwa Abdul ne kema? Wai ya aka yi mata basa son yin nesa da ni ne? Bata san lokacin da ta dawo da dubanta wajensa ba, kai wannan mutun idan da asirima to walahi da hali, Kanta kawai ta iya girgiza masa kafin ta yiwa fuskarta kalar kaucona ni Hafsat, Abdul ya dora mata tawul din mai dan lema lema wanda ya gama gogo ruwan kansa a kafadarta ya yi gaba , Janye tawul din ta yi ta ajiye nan tana yatsina fuska ta juya inda ya nufa , Gani ta yi ya ciro karamin wando yana kokarin saka abinsa bayan ya san tana dakin Da sauri ta juya gaba dayanta, inda ya saci kallonta ya yi murmushi tare da girgiza kansa, Wandon ya saka sannan ya mike da kyau ya nufi wajen bed dinsa ya zauna, Fuskarsa ya talabe da hannu daya yana kallonta kafin ya yi gyaran murya Idannuwanta ta bude a hankali, ganninsa zaune ya sakata sauke ajiyar zuciya, Wajensa ta nufa, ta samu waje ta zauna tana dubansa a sace sannan ta ce " dan Allah, ka yi min alfarmar nan, Abdul ya saki talabe fuskar tasa da ya yi ya ce" dalili? Hafsat ta tsayar da dubanta kansa ta ce" savoda ina son na gama aikina daga nan lafia, ina son inci, Abdul ya tabe bakinsa sannan ya kuma dubanta ya ce" ke yanzu kina mace har wani inci kike tunanin samu? Tafia ta yi tafia fa aure za.a maki, ki je ki yiwa mijin bauta, yi na yi bari na bari, ki masa girki, ki yi shara, ya maki ciki ki haihu ki shayar da su daga shi har yaron ki rin..... Dan Allah ya isa, wai kai da kowama haka kake magana marar da.a ko nice kake yiwa kallo mn yar bariki? Ka je ka yiwa matarka mana? Sai ka 2ani saki baki kanai min magangannu mararsa da.a? An gaya maka ni yar iska ce? Kallon da yake mata ne ya sakata tunawa da a gaban wa take, Hakan ya sakata yin sororo, tsawa fa ta daka masa, ta yi masa tsawa , bayan yana mai gidanta kuma ta zo neman alfarmarsa ne? Nan da nan idannuwanta suka ciko da kwala, Juyawa ta yi ta shiga tafia a hankali tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki, Har ta kusa fita ta ja ta tsaya tare da juyawa ta dube shi , a hankali ta ce" ka manta abinda na zo nema, dan ban ga anfanin karasa aiki a cikin irin wannan rayuwar ba, Hawayen idannuwanta ne suka zubo daga kwarmin idon, muryarta ta shiga rawa
Chapter 50 · 0% Book details