Sashe 23
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yiwa maza? Na fada maki Ke gardi Bodyguard nonsense! Ni zaki biwa rayuwa? Aikin ki, ki tare min harbi, ba wai ki min bincike ba, Na maki alkawarin sai na binciki taki rayuwar nima! Mu je zuwa ni da ke! Cikin yannayin bacin rai Hafsat ta kara matsowa kusa da shi, bayan ta janye kafarta da ya take da takalminsa sako kafafuwanta suka shige takankannin nasa , ta yi zama irin na neman fitinan nan ta dago idannuwanta da suka cika da hawaye dan jin haushi tana kallinsa yana kallonta ta maida hawayenta gaba daya ta ce" *SUNNAN KA ABDUL JABAR ABDUL BASID* , AN haifeka a cikin niger garin Niamey, Ka kasance jikan Buraima mai cefa, dan Hajia Mariama Kabir! Shekara goma sha daya ka yi tare da iyayenka mahaifinka ya tura ka kasar Saudiya dan larantar kasuwanci, wanda kake basaja da shi cewar kai dan kasuwa ne, Kanwarka ta rasu a shekaru goma sha shida, Mahaifinka a shekara hamsin da bakwai, Mahaifiyarka a shekara hamsin da uku, Kai a yanzu shekarunka talatin da uku da sati hudu da kwana biyar da awa tara da minti arba.in da sakwani........ anuna ko *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 3 Hannun suka kalla a tare, Da sauri ya janye hannun dan wani irin tsam gaba daya jikinsa ya ji, dan kuwa ba tsintsiyar hannunsa ne ta damko ba, aa damtsen hannun ne Basarwa ta yi ta shige gaba da niyar fitan itama, Abinda kunnensa ya jiyo masa na muryar Hasana tana fadin" sire kar ka fito, domin an harbe Matar da ta fita yanzu ne, yanzu haka gatanan su BS sun shigo da ita ana duba ta Da sauri Hafsat ta juyo da dubanta wajensa, aman sam bata fahimci halin da yake ciki ba dan kuwa fuskarsa bata nuna mata ba, sai ma juyawa da ya yi da wayar dake hannunsa ya nemi waje ya zauna ya shiga dadana wayar Tagar dakin ta duba da kyau ta ga a rufenta take dan haka ta juya da sauri ta fita itama ta nufi wajen su BS dake ta haya hayar aikinsu suna bata taimakon gagawa kar ta tafi dan samun labarin abinda ya faru, dan kuwa sojojin nan ne suka kawota da gudu suna fadin tana tuki bata idasa fita a anguwar ba aka harbeta, su kam sun hadu da wani irin aiki mai gardama, sun rasa gane abinda ke faruwa, Mubarack, abokin aikin su BS ne ya dago daga kokarin tsayar da jinnin ya ce" oga, wannan dole a yi gagawar zuwa asibiti, tana zubar da jinni kar ta kai inda zata kasa daukan hakan BS ya gyada kai ya juya wajen Hasana ya ce" zaki shiga da ita gari ta hanyar baya, ki samu wanda zai duba lafiyarta, ki kula fa Hasana ta yi gagawar amsa masa, nan suka kamata suka fice da ita da niyar kai ta asibiti dan kuwa sam bai ji ransa ya amsa da barinta a gidan nan ba Hafsat biye take da bayan BS tana sauraron irin yanda yake kara shirya shirin kare Abdul, du irin tsare tsaren tana sauraronsa da kyau tana kuma shanyewa a cikin kwakwaluwarta, Suna haka har suka shige tsakiyar dakin inda ya juyo yana gyara bindigar dake hannunsa ya kalleta zai ci gaba da maganar ya yi shiru yana kallon yannayinta Muryarsa ya sasauta ya ce" me ke damun ki? Saurin girgiza kai Hafsat ta yi, tana nufin ba komai ba BS ya yi murmushi yana kallonta ya ce" kina tsoron wani abu ya same shi ne? Da sauri ta kara kallon sa tana kikifta idannuwanta sak yannayin wace ke firgice na tare da ita, sai dai bata bashi amsa ba Kansa ya gyada ya kara rage muryarsa ya ce" kar ki manta waye shi, ko daukan mu da ya yi ba dan zamu iya yi masa wani abu ba sai dan ya rufe ko shi waye wa duniya Kara zuba masa ido ta yi tamkar tana son karantar wani abu a fuskarsa, Tana son BS ya shiga lamarin binciken nan na cikin gida, ita ta san waye BS, mutun ne mai shegen naci da shiga waje mai hatsari, da ace yana cikin wannan lamarin ta tabata komai na iya faruwa, ta tabata kai da tuni ya kara mata haske a wajen da take gannin duhu, Sai dai ina, ba zai yiwu ta fito fili ta fada masa ainahin sirrin Abdul din ba, domin kuwa ko ba komai sirri ne Kansa ya girgiza ya juya ya nufi dakin da bakuwa mai sunna Furaira ta zo, ita kuwa ta koma wajen dakin Abdul Dakin Abdul din ta tura ta shiga bayan ta bubuga an bata damar shigowar Zaunen dai inda ta fita ta bar shi, nan ta hango shi, A hankali ta karasa tana kallonsa ta tsaya dan kusa da shi sannan ta ce" BS ya ce na ringa dafa maka abinci daga yanzu, idan da hali ka daina fitowa har mu ga tafiar Bakuwar nan Sai da ta gama Abdul ya gyada kansa , a hankali ya ce" ba zan iya ba Hafsat ta gyada kan itama ta ce" dama na san ba zaka yarda ba Abdul ya ce" Hafsat, ni mai taurin kai ko? Ni mai gardama ko Hafsat? Kin ga dai ina cikin damuwar an harban min abar kaunana, kar ki karan wata damuwar! Bakinta ta yatsina ta daga kafadunta tana kallinsa sannan ta juya ta fice a dakin Murmushi ya saki bayan fitarta yana girgiza kansa, Wayar dake hannunsa ya danna kira Ana dagawa cikin mutunci da girmamawa suka gaisa da shehin malamin sannan ya shiga kora masa bayannin wani rudun da ya tashi da shi a yau Cikin nutsuwa Malan Muhammad mahaifin Hafsat da Abdul ya saka aka samo masa numbersa na whatsupp suke magana har suka yi mugun sabo yake karbar adu.o.i na neman tsari , a hankali har ya aminta ya yi masa voice cewar yana cikin duhu mai tsanani, yana son adu.ar da zai lazumta ko Allah ya warware masa haske a duhu Shi ne ya ringa taimaka masa da adu.o.i da shawarwari, a wadinnan lokutan har ya bashi kadan daga cikin labarin rayuwarsa ya boye masa wasu, ya dai shaida masa ana harin rayuwarsa ne, Cikin muryar datako ya ce" Abdul Jabar kana ji? Ba wanda ya isa ya saka , ko ya hana sai Allah, tabas Allahn da ya ankarar da kai cewa ana harin rayuwarka, shi ke tsare ka, ina so ka farga cewa da ya yi niyar baiwa mai bin sahunka sa.a a kanka da tuni mai faruwa da kai ta faru, Mai runfar na sama yana kallo Abdul, Kuma wannan magana da ka ce an fada maka cewa makashinka na tare da kai, kar ya baka damar zargin kowa, wannan ma kuskure ne, ka dai ci gaba da adu.ar in sha Allahu Allah zai kawar da mai son kawar da kai da kansa Kansa yake gyadawa har ya gama sauraron muryar datijon mai magana cikin nutsuwa, wanda ke amsa kiransa bayan bai taba haduwa da shi ba, bai san ko shi waye ba, bai san ko mai niyar cutar da shi bane ko na kirki ne? Wato su dai malamanmu Allah ya saka masu da alkhairi, suna aikin Allah tare da dogaro da shi da zuciya daya da imanin du abinda ya same su daga shi ne, Ajiye wayar ya yi yana lankwasa yatsutsansa, Ya yi mata magana kan kar ta saka kanta a wannan lamari, lale zai ji dadi idan ta bi maganarsa, shi ya sa bai mata maganar da wata hayaniya ba , ya bita a laluma ya kwatanta mata wannan sako daga cikin ransa yake Wani digon tsaki ya ja ya mike ya shiga cire kayansa dan kara shiga ya yi wanka ya je bangaren bakuwarsa mai rawar kai, wace ya dasawa hajia , a fili ya ce" Hafsat, bakya jin magana! Mai taurin kai kawai! Uwar gardama, , mai kyauna Hafsat na fita a dakin Abdul zuwa ta yi ta dauki abubuwan aikinta ta fito cikin tafiar basarwa irin tana cikin aikinta ne na kare lafiar Abdul ta nufi garden , Tana zuwa wajen abin shilawar wajen ta je cikin sando ta makala abin hannunta sannan ta bar wajen ta kuma dauki hanyar dakin Furaira Tana zuwa sojan dake kofar tsaye ya hanata shiga, ya ce oga ya hana kowa shiga Bakinta ta yatsina ta juya tana kallon yannayin wajen da fatan abinda ta wurga a lokacin da ta daga hannunta da niyar shafa gashinta ya makalu a labulen dakin, Bangaren su Abdul ta koma cikin nutsuwa take takunta ta nufi dakin Ni.ima Tana zuwa ta shige dan a nan ba wanda zai hanata shiga Tana shiga ta tarar da Ni.ima na zaune gaban madubin dakinta ta dira kanta saman table din madubin hannunta rike da tamfatsetsiyar wayarta Bata ji shigowar mutun ba hakan ya sa bata motsa ba, wannan ya baiwa Hafsat damar aiwatar da du abinda ya kaita dakin sannan ta juya ta fice ba tare da ta san ta shigo dakinta bama ta lula duniyar tunanin damuwar dake damunta Haka Hafsat ta kara sadadawa ta shige dakin Muhammad domin sojojin dake gadin kofarsa sunna tsakar gida sai zagaye suke tun da aka yi harbin nan, Sadadawa ta yi ta shige dakin, abinda ya kaita ta aiwayar ta zo fita kennan ya fito daga bayi daidai kuma Abdul ya shigo dakin Da mamaki