Sashe 60
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
irin an daketan nan, kura mata ido ta yi cike da tausayawa , ko wa ya dake ta? Me ya hada su? Ledar Boutik din da ta je ta buda ta ga Lipton din da ta siyo, Murmushi ta yi ta mayar mata da kayanta ta mike ta fita a dakin tana mai yi mata fatan alkhairi a kasan zuciyarta Bayan Hafsat ta yi sallar asuba wanka ta kuma yi ta canza kayan jikinta na baci, ta saka hijab dinta na sallah ta dauki ledar lipton din malan da canjin jika biyun da ya bata na taxi ta fito Daya daya cikin yaran gidansu ke wulgawa jifa jifa domin safiya ce karfe bakwai da wani abu gashi ba makaranta, Da ido suke binta, ba wanda ya gaisheta cikinsu dan kuwa iyayensu sun fada masu daga yawon banza ta dawo kar wanda ya girmamata, gashi dama ta girma fiye da yanda malan ke barin yayansa mata su kai bai masu aure ba, hakan ya sa du suke mata wani gani gani sannan suka yarda da maganar iyayensu A hankali ta karasa kofar dakin mahaifinta, hannunta ta saka ta tura kofar da salama a bakinta Tana shiga ta ringa jin maganar hajia, uwar gida kennan ran gida , matar malan ta farko tana magana kamar haka" aman malan yaya zaka ringa nuna rashin adalci a tsakanin yayanka kiri kiri? Nan Zakari tafia ce ya yi neman kudi dan ka hana shi da ya dawo ba irin abinda bai gani ba da ni kansa mahaifiyarsa, Aman malan ita yar gwal din shekararta nawa bata gida ba aure akai mata ba ba karatu aka kaita ba ba dawan makaranta aka kaita ba? Rana tsaka a dawo da ita cikin yayanmu kananu a shigo da ita cikin gida gaban kowa a ringa yi mata oyoyo ana murnar dawowarta ana rungumarta ana nuna mata farin cikin ganninta , malan baka tsawata ba, baka tara yayanmu baki daya ka yi fada ka hukuntata ba, baka nuna wani bacin ranka ba, hasalima kilaceta ka yi ka yi mata dinkuna, bata yi mana aikin fari bare na baki a cikin gida tana nade a daki tana cin abinda ta yi muradi, tana shan abinda ta ga dama, karshe malan da girmanta shekara kusan ashirin da biyu har damar ta zauna tanai maka zance a cikin gidanka da wani kato wanda ba tsaresu ake bare a san me suke yi ko suke cewa ba, malan a jiya a kawo mana wani gabjejen katon da bashi da fara.a ya zo ya tsaya a gabanmu kikam yana harararmu wai a gidansu ta zauna, a fadi haka a gaban yayanmu warwararu da kananu, malan kwakwaluwar yara me ake so su dauka? Me zai hana su suma gobe su tafka tsiyar da ta tafka su kuma dawo mana gida kai tsaye? Koda yake su sun san ba yayan so bane ba zasu yi hakan ba, aman gaskiya malan korafinmu kawai a san abin yi, idan da hali a fitar da ita a kaita can wajen dangi har a yi mata aure, ko a maida ta gidan su yaron da ya zo jiyan muga idan shi iyayansa zasu aminta anai masu irin haka a cikin gida ba aure ba komai! Malan dake zaune, tun da ya bata damar magana shiru ya yi yana sauraronta har ta gama, A hankali ya shiga bin sauran matan da kallo, kowace na zaune kusa da ita da alama shawara aka yi na abinda za.a fada masa , sai aka baiwa wace ta fi kowace tsaurin ido da rashin tsoron zuciya ta fada masa, Dubansa ya kai kan matarsa, mahaifiyar Hafsat, kanta a sade yake, ko daya ba.a gannin fuskarta bare a gane yannayin da take ciki, sai yatsutsanta da take ta murzawa tana karawa tamkar wa.inda take son canza masu kalar fatarsu dake jikin hannun nata, Dubansa ya kara kaiwa kan matarsa, wace ita ce ya dace ta zama mai datako, mai tsawatarwa mai tausasa muryarta mai nasiha gare su da shi kansa, aman kananun sun turota ita ce yau ta buda baki, ta daga muryarta sama da tashi, ta gaigaya masa magangannu irin haka a kan *Uwa*, shi da yake rayuwa a takure , yana boye nuna soyayar mamansa a gaban yan uwanta dan a zauna lafia ashe bai tsita ba? Shi da yake nuna kowani da da ya haifa daya ne a wajensa ashe ba tsira ya yi ba? Me ya ragi yayansa da shi? Bukatunsu, tarbiya, ilimi, ko walwalarsa? Ba wada ya hana masu, kowane ya basu wadatace kuwa, Me suke so da shi ne? So suke ya rufe Mamansa da duka kan laifin da bata aikata ba? Ko a kan zarginsu suke so su dawama harma suke ikirarin ya fitar da ita daga gidansa ? Mamansa? Mamansa ce suke so ya wulakanta haka? Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi wace ta saka mama dago da kanta a hankali ta saci kallonsa idannuwansa sun kada sun yi jajir, tausayinsa ne ta ji ya kama ta, haka kuma sai ta ji haushin Hafsat din, tun tana karama ake irin haka a kanta, a da yana da karfi da yarinta a yanzu da ya fara manyanta ma ba zai huta ba? A bar mata mijinta ya huta haka, in dai a kan Hafsat ne in sha Allah idan bata samu miji bama ita zata kaita inda ta kaita, in sha Allah zata samu ya yarje mata ta kaita nesa da gidan ko kowa zai kwontar da hankalinsa a kan kishin zamanta a gidan da suke, kallonta ta kawar, idannuwanta je suka sauka kan kwalin lipton din nasa da ta ajiye ta juya, Gabanta ne ta ji ya fadi, kar dai a je ta ji? Dama akoyta sabkon zuwa wajensa su yi karatu kafin su yi ta hirar duniya, yakan yi mata labarai su sha dariya, yakan yi mata bayanin dukiyarsa , kai harma da shawara, Kanta ta sada, sai kuma jin muryar malan ta yi ya ce" *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 2 Cikin nutsuwa malan ya yi gyaran murya ya shiga labartawa mama duka kaf abubuwan da Abdul ya fada masa, da kuma gannin idonsa da ya yi, harma ya tina mata lokacin da ya zo ya fada mata a yau mamansa ta ziyarce shi, mamansa na raye dan kuwa a masalaci ya ji a jikinsa ita din ce Idannuwanta cike da hawaye ta kai dubanta wajen da Hafsat ke zaune a saman cafet ta sada kanta sai zubar da hawaye take, A hankali ta ce" Allah ya kara shiryar da ke, ya maki albarka, ya baki miji na gari Hafsat ta dago kanta da sauri ta saka idannuwanta cikin na mahaifiyarta, gaba daya maman nata ta yi wani irin sanyi bata zaci zata zama haka ba, tana shashekar kuka ta ce" mama, uncle din Abdul aziz ne, shi ne ya kai ni gidan kason gagan yan daba dan kawai na mari matarsa, mama ba zan taba yafe masa ba, ya wulakanta ni, ya tozarta ni, ya kai ni gidan halaka wanda Allah kawai ya fitar da ni Mama ce ta gala mata harara ta ce" ko komawa zaki yi ki kara daukan fansa? *UNMIH* ba zan so ki koma irin rayuwarki ta da can baya ba, kin ga taurin kai, jayaya, masifa, raina maganar manya sun bada gudunmuwa wajen saka ki a wannan jarabawa, shiga gidan kaso na abin kunya bane dan kuwa kadarar bawa ne baka isa ka kauce masa ba, sai dai abin lura me kika koyo a can? Yaya kike son tafiar da rayuwarki a yanzu? Mace kike, rayuwarki kadan ce, kar ki yi tsamanin kyan nan naki zai yi ta karuwa ne, daidai da gashin kankin nan zai ringa ja baya a hankali a hankali ne har ya dawo kadan, fatar jikinki zata janye, idannuwanki zasu jeme, furfura zata yi maki salama idan har kin dace! Ki rufa bakin ki, babu rufin asirin da ya kai na kariyar da Allah ya baki, Allah ya baki kariya Unmih ke kin sani...nima na sani...nan gaba kowa zai sani, kar ki yi garajen da Allah zai barki ya ga yanda zaki yin! Tashi malama ki fice min a daki ga kys din dakinki an gyara , je ki zan neme ki! Jiki a sabule ta mike ta karbi kys din dakin a hankali ta shiga takawa tana kuma waiwayen malan aman ga mamakinta bai daka tsawar kar a yi mata fada ba, saima kawar da kai da ya yi tamkar baya wajen Bakinta ta zumburo ta daga kafa ta fice a dakin tana fadin lale malan ya daina son ta Tana fita malan ya kurawa mama ido yana kallonta, Kanta ta sada kafin take kamo dan yatsarta ta shiga dan ja, Malan ya ce" to a huce a kaina mana da za.a saka min uwa gaba daga dawowarta a fara yi mata ihu ana fitar mata da ido? Ni madame me ya sa karfinki kike nuna shi a kan UWATA NE? murmushi ta saki a hankali, ta dago da idannuwanta da sukai jajajir, Sai da ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta fashe masa da kuka marar sauti Murmushi malan ya yi yana kallonta ya ce" menene na kukan kuma? Sai da mama ta yi dan kukanta wanda tamkar na shagwaba kafin ta sasauta tana kallonsa ta ce" tsoro nake ji, du wannan rayuwar da Anmih ta gani bai saka ta daina fada ba, ji