Sashe 48
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yawo jiki a bude, na busar da mace, ruwan jikinki yanzu haka ba komai , du ya tafi, haka kuma Shut up! Ta fada ranta bace, fuskarta har ta yi ja dan masifa.... Sai fai kafin ta yi shiru da hakan muryarsa ta daukaki tata, ta fi tata nuna masifa ta hanyar fadin" *u shurrrp!* Karya na maki ne? Uban me ya kawo ki harkar aikin da maza ke yi kuma ki ce sai an kiyaye harshe wajen yi maki maganar da ake yiwa maza? Na fada maki Ke gardi Bodyguard nonsense! Ni zaki biwa rayuwa? Aikin ki, ki tare min harbi, ba wai ki min bincike ba, Na maki alkawarin sai na binciki taki rayuwar nima! Mu je zuwa ni da ke! Cikin yannayin bacin rai Hafsat ta kara matsowa kusa da shi, bayan ta janye kafarta da ya take da takalminsa sako kafafuwanta suka shige takankannin nasa , ta yi zama irin na neman fitinan nan ta dago idannuwanta da suka cika da hawaye dan jin haushi tana kallinsa yana kallonta ta maida hawayenta gaba daya ta ce" *SUNNAN KA ABDUL JABAR ABDUL BASID* , AN haifeka a cikin niger garin Niamey, Ka kasance jikan Buraima mai cefa, dan Hajia Mariama Kabir! Shekara goma sha daya ka yi tare da iyayenka mahaifinka ya tura ka kasar Saudiya dan larantar kasuwanci, wanda kake basaja da shi cewar kai dan kasuwa ne, Kanwarka ta rasu a shekaru goma sha shida, Mahaifinka a shekara hamsin da bakwai, Mahaifiyarka a shekara hamsin da uku, Kai a yanzu shekarunka talatin da uku da sati hudu da kwana biyar da awa tara da minti arba.in da sakwani........ anuna ko *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 A hankali malan ya koma ya zauna , Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" da baka yi magana irin haka ba, da na bar wajenka cike da tsoro da tunani dan kuwa idan ba mahaukaci ba sai mai kishirwar ramuwa zai hadiye irin wannan lamari lokaci daya Abdallah , imani da Allah da yarda cewa a cikin mutane akoy masu cuta akoy masu tsoron Allah, Imani, hakuri ne kawai zasu saka ka yarda da wani mahalukin a nan duniya Zan so ka kasance mai hakuri ka cinye jarabawar nan Abdallah Kansa ya sada yana mai jin yanda zuciyarsa take cinkushe bata da wani yannayi na wanda zai iya samun nutsuwa, Kansa ya kuma dagowa ya kalli malan ya ce" da idona, da kunnena na jiyo shawarar aminan mahaifina na zasu hada ni da bin mata, duda bata fadi komai ba idannuwanta sun karantar min komai Zan so a ce ba daga bakinta haka ya fito ba ko na samu damar musawa har na fuskanci dan uwana Malan ya kara matsa kujerarsa kusa da gadon yana kallonsa ya ce" ka rage zurfafa kauna , haka kuma ka rage zurfafa kiyaya Tsananin kaunar da kake masa da yardar da ka bashi dari bisa dari ne ya rufe maka ido ka kasa gannin ainahin wanene shi, sannan wacece ta fada maka? Kar ka yarda ka hau kan abu ba da kwakwaran shaida ba Idannuwansa ya dago yana kallon Malan, Sai da gabansa ya yanke ya fadi, a lokaci daya kuma irin yannayin da ya tarda ta ya fado a idannuwansa, Shikenan, ta dalilinsa rayuwarta ta bace ko me? Anfani ya ringa yi da ita? Shi kam me ya yiwa Muhammadu a duniyar nan? Me ya yi masa da zafi haka? Da sauri ya kali malan, tausayin malan da na Hafsat ne ya ji sun mamaye zuciyarsa, ta jure gwagwarmayar rayuwar nan, ta shiga Kutkale ta fito lafia, ta shiga gidan horon maza ta fito lafia, du bata rasa mutuncinta ba sai a dalilin bashi tsaro? Bashi tsaroma ya dace ya mayar da ita tun harbin da akai mata aman ya kasa hakan ya riketa a wajensa gashi ya jaza mata wannan balaki? Muryar malan ce ta dawo da shi daga dogon tunanin da ya saka shi mayar da ido ya rintse dan jin wani irin kyankyamin Aminin nasa, Bai taba jin kyankyamin zina, kallon matan wasu ba irin na yau....sai a wannan lokacin ya ringa hasko dubunnan matan da ya ganni tsirara dan kawai ya samu biyan bukatarsa, Sai a lokacin ya yi tunanin wa.innan mutanen fa y'ayan wasu ne, iyayen wasu ne, yayun wasu ne, kuma kannun wasu ne, duda su suka kawo masa kansu aman shi dan rashin tsoron Allah da rashin kunya ya mike ya mika masu abinda ya fi sirri a jikinsa suka lumda suka bashi nutsuwa ta hanyoyi daban daban....sai gashi shi ya ki ya haihu dan kar a yiwa abinda ya haifan aman cikin ikon Allah, Allah ya saka masa muguwar shakuwa da yarinyar da basu hada komai ba, shekarunsu ba daya ba , fatarsu ba daya ba, shakuwa irin ta yan uwantaka wace yake jinta har cikin jinninsa, yake yi mata so daya da ba hadi... an yi mata abinda yake gudun a yiwa yayan nasa? Dama ba.a isa a zagaye ikon Allah ko a yiwa Allah dabara ba ko? Dama lokaci Allah ya ara masa na ya gama zagaye zagayensa kafin ya rike shi? Kai, ya san ba zai iya ja da amininsa kan maganar kisan kan da ya ringa yi....wannan Allah zai saka masa! Cin amanar aminta da ya yi ..shima ba zai wani hukunta shi ba, Aman baya jin zuciyarsa zata iya amince masa ya hadu da mutumen da ya tsaga jikin Hafsansa ba tare da igiyar aure ba dan kawai cin mutunci da wulakanci ba tare da ya gile shegiyar da ta kai shi aikata hakan ba, tabas sai ya yi masa kaciya da faratunansa zai tsinke abinda ya kasa rikewa a wandonsa sai da ya ketawa Hafsat hadi! Shiru Malan ya yi gannin wasu guntayen hawaye na biyowa gefen fuskarsa , carbinsa ya ci gaba da ja yana mai dubansa a kasan zuciyarsa kuwa yana nema masa sauki a wajen ubangiji A haka BS ya shiga dakin ya ja ya tsaya, Ya jima a yannayin da yake na sarawa Abdul na kallonsa kafin ya iya daga masa hannu ya sauke hannunsa Yana saukewa a hankali ya ce" takarda ce daga saudiya, suna bukatar a mika masu mai laifi dan an karanta masu komai an kuma tura masu dukan hujoji ta hanyar computer shine suka turo da sakon a mika masu shi can Kafarsa dake ajiye yana karkadawa a hankali ya ce" idan aka basu shi me zasu iya yi masa? BS ya yi shiru domin ya tabata tambayar ba ta neman amsa bace Abdul ya dago jajayen idannuwansa ya ce" zasu saka masq fararan tufafi ne, su dauko shi su shigo tsakiyar gari da shi, su saka masa bakin yadi su rufe masa fuskarsa su dauki doguwar takarda su karanto laifinsa sannan su saka doguwar wuka sun gile kansa..... Sai da ya tsaida idannuwansa cikin na BS ya ce" an bashi mutuwa mai sauki, bai ga duniya ba an tafi da shi lahira..... Malan dake kallonsa sai da ya ji dar din Abdul din, dan kuwa gaba dayansa ya mike zaune ya kara kallonsa da kyau ya ce" ka bani wayoyina Da sauri ya juya ya yafito su Hafsat dake tsatsaye Suna shigowa ya karbi wayoyin Abdul din dake hannun su Hafsat ya mika masa su kuwa du suka juya suka layu daga kan Bs Har su Hafsat din kusan garu inda malan ya bi Hafsat da kallo dan kuwa yanzu ba hijab din a jikinta cikin damararta na aiki da ta saba Abdul kam mikewa ya yi tsaye kan kafafuwansa da kayan asibiti a jikinsa ya danna kira, Ana dagawa ya canza harshe ya shiga magana cikin yannayin zafi zafi , yana yaran larabawa wanda Hafsat da Malan suna fahimtar duka kaf abinda yake fada Cikin yannayin tsoronsa ta kafe shi da dara daran idannuwanta, dan kuwa ya fito sak a baban mutun ma.aikaci mai zaman kansa mai iko da kansa wanda ya san hakokinsa da wa.inda ba.a isa a take masa ba Maganar da ya karasa da uta shi ne" *in dai ba za.a sake shi a saki amininsa a fili a basu damar kashe kansu ba, to fa ba.a isa a tura shi saudiya ba, a barshi a Minna su yanke masa hukunci....a kai shi Niger a saka shi a cikin gidan kason KUTKALE* Yana gama fada ya ajiye wayar ya daga manyan damatsunansa ya cusa hannayen nasa a cikin gashin kansa Ya jima a haka ba wanda ya ce komai a cikinsu har ya yi niya da kansa kuma ya juyo a hankali Yana juyowa ya kurawa Hafsat dake kusa da BS ido, A hankali ya kai dubansa wajen BS din, da kuma Hasana.... Haka kawai ya tsinci zuciyarsa na cewa" ba abinda basu gani ba Rigar asibitin ya shiga cirewa hakan ya saka Hafsat saurin sada kanta daga dubansa da take, ba ita daya ba du wanda ke wajenma sai ya kawar da dubansa a kansa , wasu na mamakin shi bashi da kunyar cire kaya ne? Wa.inda suka san ko shi waye kuwa basu wani yi mamaki ba Wando da riga ya saka bakake lut, sannan ya saka gilas a fuskar tasa ya juyo wajen Malan dake tsaye, Zuwa ya yi sosai kusa da shi sannan ya duka har kasa, a hankali ya ce" na gode da mutuntani, da adu.o.i da nasihohi, in sha Allah zaka juya da Hafsat a yau