Sashe 65
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yanda take dukawa ta matse kayan sannan ta mike ta shanya saman igiya, har dira take dan ta gyara shanyar da kyau Idannuwansa ya lumshe a hankali ya furta" ANGEL Hafsat dake shanyarta bata ma san yana wajen ba, sai da ya ga hakan ba gyara shi zata yi ba da sauri ya matso inda take ya tsaya a gabanta tana shanya kayan tana juyowa suka kusan hada kirji Da sauri ta ja baya tana kallon sa Murmushi ya sakar mata a hankali ya ce" wanki kike ne? Ina mai wankin ki? Kin bashi amsa ta yi , saima juyawa da ta yi ta dauko wata shanyar zata shanya Kara matsawa kusa da ita ya yi ya ce " wai fushi ake da ni ne? Hafsat ta tsaya da shanyar tana kallonsa, Abdul ya saki murmushi ya ce" yi min murmushi kin ji? Hafsat ta zabga masa harara tana kallonsa sannan ta shanya kayanta Zuwa ta yi ta dauki bokicin karfen ta zubar da dan sauran ruwan cikin bokicin sannan ta juyo da niyar tafiarta Da sauri ya kama kunnayensa ya ce" na tuba, dan Allah ki min magana ko daya ce Hafsat Hafsat ta kale shi sama da kasa sannan ta juya ta yi shigewarta cikin dakinta Ji yayi gaba daya hankalinsa ya tashi, a hankali ya lalubi kofar ya fita ya shiga motarsa ya ja, Tukin dai kawai yake, aman gaba daya kunnayensa sun rikice, bukatarsu shi ne su ji muryarta, idannuwansa kuwa su ga murmushinta, Hannun nasa da ya mareta da su ya kara kallo, sai kawai ya kai yatsarsa guda wajen bakinsa da niyar cizawa Ko me ya tuna, ya fasa ya ci gaba da wani irin tuki har ya karasa gida Yana shiga gidan wayarsa ya dauka a cikin motar ya shiga kiranta, Tun yana kirga kiran da yake mata tana reject har ya daina irgawa ya zauna kawai bakin bed dinsa ya cire belt din wandonsa ya bale mabalin rigar ya dan sasauta wandon kasa ya dafe gaban goshinsa da hannunsa yana kara gwada kiranta hankalinsa a kanta gaba daya Can ta daga, cikin wata irin murya mai cike da kasala da sangarta ta ce" Abdul, ka barni na yi hira da mijina mana, yaya ina waya da shi kana kirana sai titit yake ya kasa jina yanda yake so Idannuwansa ne ya lumshe, a hankali yake jin maganar na girmama a zuciyarsa, kamar da wasa ya ringa jin maganar tamkar ta zagi mahaifiyarsa , wani irin dacin maganar yake ji, A kasan ransa ya maimaita" *tana hira da mijinta?* Zuciyarsa ce ya ji ta wani irin bugawa, a hankali ya ce" ki yi hakuri kin ji? Ki daina fushi da ni Hafsana Ita kanta yannayin yanda muryarsa ta fito sai da ta ji gabanta ya fadi, a hankali ta janye wayar a kunnenta ta duba shi dai ne, Mayar da wayar ta yi a kunnenta ta yi shiru tana sauraronsa, sai wata irin ajiyar zuciya take saukewa wace ke sauka da lumfashinta tana dirar masa har kahon zuciyarsa Ji ya yi idannuwansa sun yi masa wani irin nauyi, a hankali ya ce" ba zan kuma marinki ba, kar ki hora ni da fushin ki Hafsat Sai da ta ja numfashi kamar wanda ya toshe mata lumfashin nata ta ce" ba dukan da ka yi min ya tsorata ni da kai ba Abdul Abdul ya yi saurin cewa" menene? Hafsat ta ce" irin yanda ka nuna rashin damuwarka a halin da zan shiga da kuma mamana bayan na fada maka bana jin dadin hakan, Abdallah, ka san girman matsayinka a wajena? Kai yayana ne, abokin sirina, aminina, Abokina, Abdallah ina jinka a raina sosai, ni ba zan yarda na saka ka a damuwa ba, aman kai sai ka saka ni ka yi tafiarka, ka san halin da nake ciki a gidanmu ne? Ji yake harta gaban jikinsa sun yi masa nauyi, du wani furuci nata sai ya kayar masa da gaba, wai me ya sa ne ta kasance mai karfin ruguza shi, sannan mai karfin saka shi risinawa? Shin me ya sa take da madaukakin iko a kan muradinsa da akasinsa? A hankali ya buda bakinsa ya ce........ Hapoy sallah yan uwana, Allah ya karbi ibadun mu, ya maimaita mana *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 A hankali ya kuma iya daga bakinsa ya ce" Hafsat... .. Wani irin jan sunnan ya yi, ya karasa shi da ajiyar zuciya wanda ya hakan ya saka Hafsat rungume fillow din dake kusa da ita ta lumshe idannuwanta baki daya ta shiga neman saisaita lumfashinta, domin gagarar buda bakinta bale har ta iya amsawa ta yi A hankali ya ce" bani da uwa, mahaifina yana jin kunyata da ba zai iya kuma rayuwa tare da ni ba, Na tara dukiyar da ni kaina ban san adadinta ba, Ina kwana da sannin ni ba kowa bane dare daya mala.ikan mutuwa zai zare raina na zama gawa Shiru ya yi kafin ya ce" a da na zauna zaman ni sai na ga mace an min asiri, ko wata rana sai na ga wani kalar tsiraicin daban bayan na kwana da sannin mai kallon tsiraici baya tsufa da ido, tun a gidan duniya bare irin girman hukuncin da zan tarar aman haka nake tafe watara na hadu da yarinyar da na haifa da cikina, wata rana na hadu da wace ta haife ni da cikinta aman da yake aikin shedan ne haka zan zauna na bita da kallo har ta gama karanta min karatun nata na zubar da najasar tawa a kasa kusa da abin wankana! Hafsat, sai da kika zo rayuwata na fara fahimtar eh lale idan da asirima to ni kaina na baiwa abin gaskiya, Hafsat ke ce ta biyu bayan mahaifiyata da nake jin kunyar ki kama ni ko ki san irin halin da nake ciki daga bakin lokacin da na fahimci kina tare da ni da zuciya daya da niyar gama aikin ki lafia ki yi gaba abinki Hafsat ba irin kalar iskancin da ban nuna maki ba aman sai ki juya abinki ko idan abin ya yi maki tsauri take kike wanke ni tas bakya raga min harma ki zubar da hawayenki dan takaicina Ina sane, ina sane da dukan motsin ki, Hafsat, ba zan iya hadiye abu a kanki ba, ba zan iya kawar da kai a dukan wani wanda zai cutar da ke ba, Ban san dalili ba, har ji nake lumfashina zai tsaya idan na ji ki a damuwa, Abin haushinma sai kawai kike son canzawa daga matakin mai kare yancin kanta ki koma wata mau tsoron mutun, ban kai hanuna fuskarki ba sai tukukin haushin kin kirayi kanki da muguwar kalma, Hafsat, koda a ce haka kike ina nufin kalmar nan ke din ita ce ta haramta ga kowani mutun ya fade ta, ina iya soya masa idannuwa dan ubansa! Wani irin tsam tsam tsam ta ringa ji a gaba daya jikinta, lale ta yarda da maganar nan cewa a duniya ka ji a damu da kai ba karamin jin dadi bane bare ka gani da idannuwanka, A hankali ta ce" kai mafadaci ne Abdallah Murmushi ya yi, wanda bai yi shirin yinsa ba, wai Hafsat ce ke cewa wani yana da fada Sai da ya gama murmushin ya ce" takura maki ake a gidan nan ko? Me suke maki ne? Wa da wa ke maki? Ta so sakin baki dan fada masa , sai dai a likaci daya kwakwaluwarta ta tina mata wanene shi, da kuma magangannunsa ba cika baki bane yana iya aiwatar da alkawarinsa ko furucinsa, Dan haka sai kawai ta ce da shi" ba wani abu ni dai ka taya ni da adu.a samun saukin rayuwa Haka suka yi ta tautaunawa har kusan raba dare, sai da ya ji yannayin saukar numfashinta ya canza, a hankali ya ce" baci ki ka yi? Shirun da ya ji ne ya saka shi sakin murmushi a fili ya kai dubansa agogo, karfe biyu har da rabi, adu.ar baci ya yi mata wato ta tsari daga wayar da niyar Allah ya kai mata domin suna tsakar hirar bacin ya yi awon gaba da ita ta gaji ainun gashi ya tsareta har wannan lokacin Da duku duku, da duhu duhu kamar yanda ya saba jiransa har ya karaso yau har tarbo shi ya yi Tun da ya hango shi ya tabata akoy abinda ke faruwa dan kuwa mahaifinsa nasa na kiyaye a ganshi tare da shi ko dan kar a san a yanda ya same shi ya jaza masa matsala a ma.aikatarsa Motarsa ya bude ya shiga , kafinma ya gaishe shi sai ya ji ya balbale shi da fada kamar haka" lale lale Bashir kana wasa da wuta! Tun lokacin da ka je yi masa aiki na gargadeka cewa wannan mutumin da kake gani basaja yake dan kar a gane meye asalin aikinsa, na bayana maka ko waye shi mai gidan mai gidanka kuma ubanka ne shi! Aman da yake cikin kwakwaluwarka majina ne cike shine har kake son sako shi a lamarinka? Har ya kasance shi zai yi bincike kan yarinyar da kake so kuma? Yaushe zaka daina zuwa gidajen yan mata kana nuna kana so ? Nawa ka saka har muka je tambaya ka dawo ka fasa? Nan yarinyar nan har ciki kuka zubar kuna soyaya daga baya ka watsar da ita da ka gama samun abinda kake so,