← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 94

Sashe 14

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kam dubanta ya yi cike da kulawa, gannin ranta ya kai kololuwar baci ya saka shi yin gaba yana mai cewa" ki hanzarto mu je nemansa Sai da ra mike ta bi wajen da kallo, haka kawai zuciyarta ke fada mata yana wajen, sai dai bata ganshi ba, bata ga alamunsa ba, dan haka ta juya ta bi bayan BS ta bude bayan motar ta shiga suka daga suka nufi gidansa ko can ya koma, Zuru ta yiwa waje daya cike da jin haushin kanta, yama aka yi ta fito ta bar masa wajen bayan ta gama fahimtar mutumen lale na cikin hadari kuma shi da kansa yana mai kara saka kansa a hadarin? Yama aka yi ta yi saken yin hira a lokacin da ana iya harbe kan wanda suke baiwa tsaro? Kanta ta girgiza ta jinginar da jikinta jikin motar ta lumshe idannuwanta, Murmushi ta saki a fili kafin ta dubi BS dake bin du wani motsinta da kallon mamak8n yanda take abubuwanta, ta ce" ka san me? Shi din, bayan sannin abinda yake yi da ya yi, ya kuma kware a aikinsa, tabas jarumi ne! BS ya kauda dubansa daga kanta ya mayar bakin titi har suka karasa gidansa, Du inda suka san zasu same shi a cikin gidan sun duba, aman ba shi ba alamarsa, Sai a lokacin kuma suka fara afkawa cikin tsoro, tsoron da suka shiga ba na komai bane sai na tunanin idan fa dauke shi aka yi aka raina masu hankali da wannan saurayin? A lokacin da ta yi wannan tunanin sai da hanjin cikinta ya motsa tsabar kaduwa da ta yi, Ba shiri suka juya wajen, sai dai saurayin na nan bai wani tafi ba, da alama wajen nasu ne, nan yake wuni idan ya zo, yana ta aikinsa da mutanen wajen, Jiki sanyaye suka koma gidan nasa, du sun yi wujiga wujiga a tsakar gidan, har sun yi kiran GN sun sanar masa inda cikin tashin hankali ya nemi layin ogansa ya fada masa....... Muhammad kansa tsaye yake cike da tsoron fitowarsa , shi fa ya zama na daki, baya zuwa komina, hakama Ni.ima sun tsatsareta sun canza mata yannayin gadon dakinta, kai windows din gaba daya sun rufe shi ruf irin yanda ba za.a iya hango na ciki ba du jarabar mutun, Tun da ta ji hayaniyar ana neman mijinta hankalinta ya gama tashi, gashi babu waya kaf gidan du an cicire sai tasa da ta masu tsaronsa kawai, ta rasa ina zata tsoma ranta ta ji sanyi dan kuwa tana son fita sun bi sun tsare sun hanata fitowama bale ta nemi yanda zata yi ta samu labarin inda yake, Hafsat kam, haka ranar nan ta daketa, yama ta yi ta kasa tsaye ta kasa zaune, ita fadan da GN ke yi tamkar zai ci namansu danye ba shine damuwarta ba, wani irin abu take ji mai shige da matsannanciyar damuwa kan rayuwarsa, Tun a jiya da ta ji kadan daga cikin labarinsa take jin wani irin tausayi da jinkai a gare shi, tsaye take, ta yi shiga ciki da fitowa ya fi a kirga, Bata kai ko ruwa bakinta ba bale cikinta ya tsamaci wani abin, Ta gama fita a hayacinta ga GN fada kamar ya shako su ta computer da ya yi vidio call ya yanyanka su ya huta, Wasa wasa har aka fara kiran sallar magariba, aka gabatar da sallah aka gama, inda duhun magariba ya fara sanyo kai Wani babur ne aka budewa gidan ya shigo, wani irin hayaki babur din ke yi da wani shegen kuka irin ya tsufan nan har yana faman bugawa dan kansa, Gaba dayansu ido suka bi babur din da shi da mamakin ya aka yi aka budewa wannan babur haka gida ya shigo? Tsayar da babur din ya yi ya sauka, Kayan dake jikinsa kansu ba da su ya fita ba, du ya yi wani budu budu da shi haka yannayinsa na nuna a matukar gajiye yake, Basu gama yarda da shi bane sai da ya karaso inda suke tsatsaye da shirin ko ta kwana ya ja ya tsaya ya rike kugu yana mai bin su da kallon nan na son kure mutun kafin ya sakar masu murmushin nan na raini ya ce" hi! Dankari, gaba dayansu da mamaki suke binsa, kafin du a nufe shi masu bashi tsaro suka fara tunkararsa inda BS ne shugabansu shi ya dube shi da girmamawa da yannyi na son jin gaskiya ya ce" sire, aman ina ka shiga? Me ya same ka haka? Wannan suturar fa? Wannan yannayin fa? Bamu ga fitarka ba sai nemanka muke tun da safe? Abdul ya gama sauraronsa da kyau, kafin ya kai dubansa wajen Muhammad dake saurin karasowa shima da yannayin murnar gannin shi da aka yi, A hankali ya ce" kana zance a wajen aiki yaya zaka gane na fita? *baka san aikin ka ba Bodyguard soldier* Yana kokarin ratse su sai ga Ni.ima da gudunta ta fito, inda macen dake bata tsaro ke biye da ita tana mai son dakatar da ita kar ta karasa wajen nan aman ina Tana zuwa jikinsa ta shige ta fashe da kuka, Sororo ya yi yana dubanta, basu gama gannin hakan ba ta cika shi da jin haushi ta juya ta dale mai bata tsaron nan da kallo inda gaba dayansu sai da suka zaro ido, tunbama Hafsat dake cike gefe tana kallon du abubuwan dake faruwa, Cikin muryar kuka ta ce " ya zaki hana ni fitowa na ganshi? Ke din banza ke din wofi? Aikin ki bani tsaro ba bani umarni ba, dan me zaki hana ni fita kuma yanzu da ya zo ki hana ni fitowa ganninsa? Mai kashe mun ya jima bai kashe ni ba a kansa! Gaba dayansu kallonta kawai suke, inda Hafsat har wani sarawa kanta ke yi na irin abubuwan dake faruwa a yau din nan, Haushi bai kara kumeta ba sai marin da aka wankawa abokiyar aikinta sannan aka wulakanta ta dan kawai ta yi hani da kar ta fito wajen da ake iya daukan ranta a banza? Idannuwanta ta rintse , gannin ya cika hannun Ni.imar kuma ya nufi wajen Muhammad da abinda Ni.ima ta yi ya kashe masa jiki yana dubansa, Yana zuwa sukai gaisuwar larabawa kamar yanda suka saba, Muhammad ya rike hannunsa da kyau ya ce"ka je ka yi wanka, Murmushi ya sakar masa kafin cikin dabara ya sinar masa da abin hannunsa , da ido ya yi masa signal din yana zuwa, Dubawa ya yi ya ga du sai kallonsa suke , da hannunsa ya yafito Hafsat dake tsaye fuskarta tamkar ta fashe da kuka dan haushi ya ce" uzurina na je, wanda bana son bindina na biye da ni....ku gane man, yanzu na dawo gidan farautana, zo mu je ke mai kula da ji ki duba dakina, na wuni bana ciki kar a je wani ya yi ajiya Ya karashe yana mai kane ido daya ya juya ya yi gaba ba tare da ya baiwa BS amsar tarin tambayoyinsa ba, ba kuma tare da ya kula irin abinda Ni.ima ta yi ba, Haka suka juya suka bi bayansa, sauran suka koma bakin aikinsu, Haka mai tsaron ni.ima ta kuma bin bayanta tare da namijin cikin yannayin nuna halin ko.in kula da abinda ya faru da ita domin qn hore da hakan na iya faruwa da su, Idan Hafsat ta tankawa abubuwan da ya yi, to tabas rigar jikintama ta yi magana, Haka ta fara shiga dakin , ta nufi wajen bed dinsa ta fara bincikawa, ta koma dakinsa na baci ta bincika, ta dawo ta shiga bayi ta hada ruwan wankan bayan ta bincika ta kuma gyara komai, ta fito da niyar barin dakin ta ganshi tsaye daure da tawul, jikinsa sai warin rana yake da alama fitar nan da ya yi ba karamar wahala ya sha ba, Murmushi ya sakar mata ya ce" yau ba fada ne my Bodyguard *budurwar dan ta.ada?* Dan tsai ta yi, kafin ta girgiza kai ta kara daga kafa zata fita ya ce" *Nadia abdallah* (wato sunnan da aka basu kennan na Hafsat a can gidan formation) Ya dan taka ya bude bayin yana mai cire tawul din jikinsa gaba daya sannan ya ce or *Hafsat Muhammad* , ba zaki ban muryarki na ji ba? Da wani irin sauri ta juyo , juyowar da ta tsorata ta, ta....... .............comment nah?....... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 9 *Free page* daga page 10 an gama free Cikin sanyinsa ya ci gaba da fadin" dan Allah ku yiwa kanku adalci, yanzu ke kin je kin yo shafe shafenki, kin cika hoda ta kara janye fuskarki, kin zagaye lebe ya zama dan dagwas, da a duhu zaki zo mini shikenan kin ribace ni? Duba ki ki ganni, fatar jikinki ta fara janyewa irin alamun shekaru sun tarun nan aman dai har yanzu wannan bata isheki ba? Ya fada yana mai nuna .....dinsa, Manyan idannuwansa ya daga sama kafin ya maido kanta ya ce" da yarintata yanzu ni hariki ta yiwa wulakanci na kale tsohuwa tas har ina shirin mika mata abuna ta yi wasa! Gaskiya baki yiwa bariki adalci ba, Ki saka kayanki kin ji? Ba zan iya rike wannan takalman ba, Ya fada yana mai nuna kirjinta, Gaba dayanta ji ta yi ta muzanta, so take a hakanma ta kara jan ramayinsa, sai dai ina, ba wani hayanniya ya yi
Chapter 14 · 0% Book details