← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 94

Sashe 28

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

da babur din gannin yanda BS ya nufo inda take tsaye gadan gadan ta tsura masa ido sannan ta sadakar cewa idan ya zo yana iya dauketa da mari BS na karasowa hannunta dake rike da mashin din ya damka yana dubanta ya ce " ina kika je? Ke da wa kuka je? Me kika je yi? Bakya tsoron wata fitina ta same ki? Idannuwanta ta kikifta tana kallonsa, A hankali ya sasauta damkar da ya yiwa hannunta ya rage ihun muryarsa ya ce" baki damu da damuwata ba? Ya dace ki damu da aikin ki, dan wanda ya dauke mu ya san takun mu Yawun bakinta ta hadiye a lokaci guda kuma ta dan leka bayansa, Ido hudu suka yi da Abdul sannan ya juya ya shige ciki ba tare da ya ce da kowa komai ba Sai a lokacin ta jinginar da mashin din dake kauri ta ce" BS, ka yi hakuri, na gaji da zaman waje dayan ne, shi yasa na fita na sha iska Hasana dake tsaye ido ta zaro tare da fadin" me? Ke kina da hankali kuwa? Ke Bodyguard har wani lokacinki gare ki bale muradinki? Ki dubi idannuwan mutane ki ce wai kin tafi shan iska? Ba laifi, tunda kin shawo iska sai ki zo ki zagaye balbalin gidan nan sau hamsin! A tare suka dubeta, daga BS har Hafsat, Hafsat kam dukawa ta yi ta kara gyara takalmanta sau ciki sannan ta cira da gudu da daren nan ga tarin gajiya , ga yinwa, ga bukatar yin wanka ta shiga gudun punishment domin kuwa Hasana dai ta isa ta sakata ko ta hanata a bangaren aikinta dan gaba take da ita ya zama wajibi ta yi mata biyaya Hannun Hasana ya damka ya juya da ita da wani irin karfi ya hankadata gefe inda ba za.a iya hangosu ko a ji maganarsu ba ya ce" ke a wa zaki shiga hurumin da ba.a saka ki ba? Ina ruwanki da amsar da ta bani? Ke idan a halayanki zan bi ki kina tunanin zan bar ki ki numfasa ne? Bayanta da ya buga da bango ta dafe kafin ta ce" BS , saboda na hora yarinyar dake kokarin rainaka a gabana ne kake wulakanta ni haka? Menene tsakaninka da ita? Wacece ita? Me ya sa na ga du kuna wani rawar kai a gabanta? Idan tana zagayawa da wancen da muke yiwa aiki kaima kwoncin kake da ita ko? Cikin daga murya ya ce" ki rufe min baki da fadin magangannun da ba tsari a nan, Kin ga yarinyar can da kika raina? Ni ita nake so, kuma ki daina kokarin zaginta dan ko daya , ba irinki bace, yanda take jana a kas ya saka nake kara mutuwa kanta, ta san ina sonta, har yanzu ta kasa so na, dan haka ki girmamata kar ki yarda ki mayar da ita abokiyar gabanki , dan na rantse maki ta ishe ki tuwo da miya Sosai magangannun nan sukai mata zafi, tana dafe da bayanta ta ce" aman ka san da ni kake soyaya ko? Kuma ka san aikinka ya haramta maka soyaya da dalibar da ba.a yaye ba ko? Sai da ya shafa gaban goshinsa da sankon kansa sannan ya ce" to ki tona, ke bari ki ji, abinda zai hana ni samunta daya ne, idan ta ce da ni Bashir ka barni haka, bana son ka! Yana gama fada ya juya ya fice ya tsaya can gefe yana hangen yanda Hafsat ke gudu tana raba hanya, Kwarai yana da damar hanawa, ya isa ya hana dan shima yana matsayin gaban Hasana, sai dai ba zai shiga ba ko dan ya kori tsargi sannan ya rike girmansa a wajen yarensa, tausayinta yake ji, kaunarta yake yi, ji yake dama zai karbar mata gudun! Abdul dake tsaye kusan windows din dakin Muhammad ya rike dan labulen ya tsura mata ido yanda take gudu, Muhammad na yi masa magana shi walahi kwata kwatama bai san me yake cewa ba, a haka ya juyo ya ce" *daga ina take?* Muhammad dake dana waya yana nuna masa sabuwar motar da kanfanin Helix suka kera wace ke da tsananin tsada ya dago yana dubansa Sai da ya matso inda yake tsaye ya ce" wa kake tambayar inda ta je? Sai a lokacin Abdul ya farka, tamkar an dan tsikare shi ya dubi Muhammad da kyau, sai kuma ya shiga takawa ya ce " ina zuwa....... A wannan dare haka kowa ya yi barci zuciyarsa a cinkushe, tun daga Abdul, Ni.ima, Hafsat, BS , Hasana, da du wani ikon dake gidan wanda sanadiyar rashin gannin Hafsat da tabatar masa cewar ta fita a mashin ya saka tayar masu da hankali da rantsuwar su saurari du irin abinda zai sameta walahi da hannunsa zai masu! Hakan ya saka du suka firgice suna masu jin haushin juna da jin haushin wanda ya ara mata mashin din Ko da safe ba wanda ya shiga sabgar wani, kowa bakin aikinsa yake tun safe har yama, Ko da yama ta yi , yauma fitowar ya yi , sai dai yau wani bakin yadi sidik ne ya saka ya fito ya nufi wajen shakatarwarsa A lokacin da ya zauna ya mike kafarsa ya kali BS dake kai kawo ya ce" ka ce da dayar nan ta fita can baya ku kuwa ku zo kai da wancen ina son gannin ku A nunin da ya yi, yana nufin a cewa Hasana ta fita, su kuwa ya nuna su zo saman kujerar dake kusa da shi yana son gannin su Abinda ya bukata BS ya aiwatar, inda suka zauna a kujerar dake gabansa su duka suna kallon yanda ya tsura masu ido ya kalli wannan ya kalli wancen Sai da Abdul ya gama kallon su sannan ya ce" *wai ku yaushe kuke zance ne? Wace irin soyaya ce kuke haka bakwa bata kulawa? To yau ku yi zance!* Sai da suka kalli junna sannan suka kale shi a tare tamkar hadin baki, BS ya dan gyara zamansa yana kallon Abdul, Abdul ya girgiza kai ya ce" kai yanzu, katoto da kai, kake jin tsoron wannan yar yarinyar? Bashir maza ka rako duniya ko me? Ka fito kace da Hafsat cewa kana son ta aman sai ka ringa hauka har kowa ya gane kana sonta ita ka kasa fada mata kiri kiri? Sai da BS ya mike tsaye, sai kuma ya koma ya zauna tamkar an dangwarar da shi yana zare ido yana kallon yanda Abdul ke kada kafarsa dake wanke tas tamkar a side, A haka ya bi shi da kallo har fuskarsa, kai shi ko a lakuru bai ga kwalon dan duniya irin Abdul ba, Dubansa ya maida wajen Hafsat ya ga ta tabe bakinta ta dafe gaban goshinta, kuma abinda ya bashi mamaki bai ji ta yiwa Abdul ihun kar ya yarda ya kama sunnanta sunnan mahaifiyar malan ce, ohk wato sai su da aka raina ko? Katse masa tunaninsa ta yi ta hanyar fadin" *ABDUL* idannuwansa ya dauke daga duban gefen da yake , ya saka cikin idannuwanta har da takabe kumatunsa yana kallon yanda ta kankance idannuwanta wai kennan zata yi jaraba ko? Dubansa ya kai wajen BS ya ce" Bashir, ko jaraba zata yi kyau take mata, bara ka ga yanzu ta ce" Abdul, menene haka? Ka bar mu mu koma bakin aikin mu.... Sai ta wurgan harara, sai ta mike ta tabe baki kuncinta ya lotsa , sai ta koma bayana ta yi tsaye ta hade rai dan Hafsat bata son raini! Kallon junna suka kuma yi , Nan Hafsat ta lumshe idannuwanta tana son tunanin girman rainin hankalin Abdul, Sai dai bai bata wannan damar ba ya katse mata tunani da fadin" kina tunanin zan baiwa soja mashin na kasa saka masa abinda zai nunan inda yake shiga? Hafsat me kika je yi cikin jejin da ba wani mahaluki dake rayuwa a cikinsa a sanina? Kina son na saka maki ido a motsinki ne? Shiru ya yi, kafin ya ci gaba da fadin" BS nah? Ka tambayi wajen wanda ta je dan ba zan lamunci hakan ba! Mikewa ya yi ya mayar da bakin gilas dinsa ya juya da niyar tafia, Sai dai sunnan da Hafsat ta ambata ya kusan tainke masa lumfashi, Wani irin ja ya yi ya tsaya sannan ya juyo a haukace ya....... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida
Chapter 28 · 0% Book details