Sashe 49
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yau.....zan zo nima domin zaman kasar nan ya fice min a rai Malan kam kansa kawai yake gyadawa yana kallonsa, haka ya mike ya fice inda suka mara masa baya gaba dayansu Suna fita daga asibitin ya mikawa BS waya, BS na gama sauraron maganar ya kalli Hafsat da sauri, sannan ya kali Abdul, Ganni ya yi Abdul din ba wani alamar fara.a a tare da shi, dan haka ya mika masa wayar ya je kusa da Hafsat ya yi mata bayanin abinda aka ce Ji ta yi kamar tsokanarta yake, dan haka da wani irin gudu ta karasa inda Abdul yake tsaye, Haki ne ya hanata magana sai nuni da take masa, Abdul ya lumshe idannuwansa yana mai jin nauyinta har cikin ransa ya ce" ki je Hawayen idannuwanta ne suka bale, cikin yannayin kuka ta ce" kana nufin..shikenan? Kana nufin na zama mai cikeken yanci? A yanzu ta waya ka saka aka sake ni daga kason da na shiga? Kana nufin zan ga mahaifiyata Dariyar da take ua saka shi tsurawa fuskarta ido, Hannunsa ya dago a hankali, hakan ya saka hannun nasa dake bari bari ya dora yar yatsarsa a gurbin kumcinta da ya lotsa sosai , sannan ya kama dan mayafin nata da ya fadi a kafadunta ya dora saman gashin kanta sosai ya rufe, Idannuwansa ne ya sauke saman kirjinta, lokaci daya gabansa ya buga da mugun karfi, lokaci daya kuma ya rintse idannuwansa a hankali ya ce" *zan waiwaye ki* Suna tsaye suna kallo ya shige wata mahaukaciyar bakar mota ya tayar ya harba bakin titi inda su hasana suka mara masa baya Gaba daya jikinta ne ya mace mata, bata son tafia ta barshi du irin zumudin gannin wannan ranar, Gata dai ga mahaifinta, sannan an tabatar mata da ta bi mahaifinta ta je gida ta huta ba tare da an tsara mata tsarin rayuwarta ba, Sai dai kash, yau ta tabata sabo tirken wawa ne, ita kuwa ta yaya zata iya sabawa da rashinsa bayan ya saba mata da shi a ko wani motsi nata? Dubanta ta kai wajen BD dake tsaye yana yi mata murmushi, sai a lokacin ta waiwaya sai ta ga mahaifinta baya nan, Da sauri ta ce" ina Abih? BS ya saki murmushi yana kallonta ya ce" sun tafi da Abdul, daga can za.a kai shi aeroport n e, akoy abinda zasu yi, mu je a can zamu hadu Ajiyar zuciya ta sauke ta daga kafarta ta shiga motar da ya nuna mata ya tayar suka kama hanya Ko a hanya hira ne BS ya cikata da shi, wanda dadaya take tsinta sai dai ta yi masa murmushi Cikin nutsuwa ya ce" kin taka sa.a, babar sa.ar rayuwa, wace ba kowa ke samun irinta ba, A yau na ga abubuwa da yawa, na ga ribar zuciya daya da girman adu.a, tabas a baya na yi sake da na ringa wasa da Sallah, ashe dai wanda ya rike Allah ba zai ji kunya ko ya wualakanta ba? Hafsat ta sakar masa murmushi tana mai kallon gari, itafa walahi har wata iska mai sanyi ce take ji tana ratsa gabanta..... Muryar BS ce ta tsinke tunaninta a lokacin da ya ce" *me zai hana ki cika min nawa burin nima? 1ki karbi tayin soyayata ki so ni tamkar yanda nake son ki Uman Malan?* Tsurawa fuskarsa ido ta yi tana kallonsa, Menene aibunsa? Dama sallah ce, a yanzu yana yin sallah tun karfinsa, Idan ta kai warhaka da karfinta a sha.anin kutakale tabas harda taimakon BS Yana biye da ita ne dan yana matsanancin son ta, Ita kuwa isan bata so shi wa zata so? Mutun ne shi mai daraja da daukaka, ya kasance mai kaunarta tun bata zama Bodyguard ba, ya kasance mai kawar da kai a irin halayanta na yau da kulun, ya jure iskancinta kala kala, baya hukunta ta, baya sakata kwana cikin maza.......yana kishinta, to ita kuwa wa zata samu ya yi mata irin wannan son? Kanta ta sada cikin yannayin kunya, abinda bata taba nuna masa ba a hankali ta budi bakinta ta ce"........ *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 2 Mamaki ne ya cika zuciyar BS, haskiya ne, shifa ya ga abubuwan da suke da girman da isa da iza ba zata saka a koya ba , sai dai idan an ginaka da abin, Wayar ya kashe ya koma ya dauki jibrin da aka gama yiwa dinki suka nufi gidan Abdul dan ba zai yiwu ya bar shi ya yi jinya a asibiti ba, A lokacin da suka karaso, ya jima tsakanin dakin da aka baiwa Hafsat da nasu, yana ta kai kawo kafin da kyar ya iya bugawa yana saurare da bugawar zuciyar Allah ya sa ta bashi damar shiga, dan wani irin kwarjini take masa kamar ba yarinya karama ba. Amsawa hafsar dake zaune kasa bayanta jingine da gadon dakin , laptop gabanta ta yi shiru tana duban screen din cike da rashin kwarin gwuiwa domin kuwa lale Abdul ya bata labarinsa aman ba wai ya bata sunaye bane, komai a dunkule a baibai ya bata, ta tabata ya yi haka ne dan karta ce zata shiga lamarin da ba nata ba, ya yi haka ne dan kar wani ya kutsa kai cikin abinda bai shafe shi ba, Gashi dai tun da ta shigo sallah kawai ta iya yi ta samu waje ta zauna tana ta binciken abubuwan da ba amsa, sai canke canke take ko zata dace har BS ya shigo dakin nata, Waje ya samu ya zauna a kasa kamar yanda ta zauna yana kallonta, A hankali ya ce" yaya jikin ki? Hafsat ta dube shi da kyau tana mai rufe laptop din, Hannun ta kalla, sannan kuma ta dubi BS , kafadarta ta daga kadan kafin a hankali ta ce" Alhamdulilah, BS ya kureta da kallo, a nitse ya dan muzkuta yana dubanta sannan ya ce" wa ya cire maki bullet din? Itama wannan karron tsura masa idon ta yi, sannan ta ce" Abdul ne, Abdul? Ya maimaita yana mai nuni da wata manufa, sannan ya kawar da kansa gefe yana dan murmushin yake ya kuma dubanta ya ce" da sunnansa kike kiransa haka? Dan sasaucin dake saman fuskarta ta yi kokarin kwashewa, inda ta dora yannayin rashin walwala sannan ta kawar da dubanta daga kansa, BS ya juyo da nasa duban jin ta yi shiru, ya dago hannunsa yana dubanta ya ce" kar ki yaudari kan ki, kar ki sakawa kanki wani tunanin abinda ba zai taba yiwuwa ba, kin san shi kuwa? Kin san ko shi waye? Kina kokarin yin wasa da wuta, kina son saka kanki a halaka ne? Ki sauko daga inda kika hau, aiki ya kawo ki, ki yi shi kawai, ki duba ki ga yanzu da harbin nan a wani wajen da zaki mutu aka yi shi da shikenan kin mace wajen kokarin gannin kin birge shi ko me? Da sauri ta juyo da dubanta wajensa, Ta jima tanai masa wani kallo kafin ta sada idannuwanta , ranta ne take jin yana wani irin tafarfasar da ba zata so yin wani furuci a gabansa a wannan yannayin ba, Me yake tunani da ita, au shi ba zai cire wannan shirmen dake dawainiya da shi a kanta ba? Dan ita bata ga dalilin da zai saka shi duban kwayar idannuwanta ya jefeta da magangannun dake nuni a sakarai ya dauketa ba, an fada masa tana neman kai ko ta zo dan haka ne? Sasauta yannayin muryarsa daga bacin rai zuwa rarashi ya yi ya ce" ba ina miki haka dan na tsaneki bane, ina so ne ki farga tun kafin ya zame maki matsala Hafsat ta dube shi da idannuwanta ta ce" kar wani yannayi naka da ka kasa daidaitawa ko tsayarwa ya kai ka aikata baban kuskure a rayuwarka BS! Kar ka mayar da abokiyar hamayarka.... Shiru ta yi na dan seconni kafin ta dago da idannuwanta da yannayin she's vry serious da abinda take fada kafin ta taune lebenta da hakorinta ta ce" *dan walahi sai na bika har gawarka sai na yi kokowa da ita!* Idannuwansa ya zaro yana dubanta, inda gabansa ke tsannanta faduwa kan irin lamarinta, A dan hargitse ya ce" saboda shi din ne zaki mayar da ni abokin gabanki ko me kike nufi? Hafsat ta kankance idannuwanta dan jaraba hannunta na ciwo aman bakinta ya ki mutuwa ta ce" dan me saboda shi? Me kake tunani tsakanina da shi? Ina jin da ni fasika ce, da na jima da bayar da kaina kafin na shiga *kutkale!* Aman ai dan na yi maganar nan ne kika bata rai haka ko? Ya fada yana dubanta da kyau yana dan matsawa kusa da ita kafin ya dakata yana dubanta , sasauta murya ya yi ya ce" bana daukan ki a fasika, bana miki kallon wawuya, hasalima idan har ya kai ki wajen da zaki sha wahala zamu sha ta tare ne, Shiru ya yi gannin ta kura masa ido, daya daga cikin sunnayenta ya zaba dan kiranta domin ta hana shi kama na asalin, a hankali ya ce" Ummi, ina son ki, kin jima da sannin haka aman kike wasa da zuciyata? Bayan kin san da daya daga cikin sauran na so, da da gudu zata amince min harma ta bini inda zan je ko? Ki bari haka, ki daina haka, ya karashe yana mai dubanta kamar yanda take dubansa, Sai