Sashe 89
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amsa, lokaci daya tsoro ya darsun mata , tsoro ne ya shigeta da fargabar menene wannan kuma ke damunta? Yaya abin dake bakon lamari a wajenta ke neman zame mata wani banban muradi na zuciya? *kar ki raba jikina da ni.imtacen dumin jikin ki da kanshi mai dauken nazarina* Ajiyar zuciya ta sauke mai karfi kafin ta kara jan jikinta tana mai jin haushin kanta, domin maganar tasa ta kara birgeta fiye da fushin da take Mikewa ya yi zaune dangalgal, ba wata kunya ko tunanin rufe yannayinsa ya kamo hannunta ya ce" menene??? Da sauri ta rintse idannuwanta zuciyarta ta shiga dokawa fiye da da, muryarta ne ta shiga rawa rawa a lokacin da ta buda bakinta ta ce" i.m tired, zan je dakina Murmushi ya saki gannin yanda take kakaucewa kamar ba mijinta ke gabanta ba, salon kunyar tata kuma sai ta bashi sha.awa, Lebenta ya kurawa ido irin yanda ya yi jajajir tsabar ya sha wahala yau a hannunsa, sai rawa rawa yake A hankali ya duka sosai kusa da ita ya damki leben nata ya shiga tsotsa Bata san daga ina ba, bata san ta yaya ba, ita dai ta tsinci kanta da daukan hannunta na dama ta talabo shi da kyau ta shiga bashi taimako domin zuciyarta bata da muradin da ya fi a koma abinda aka dauki lokaci ana yi Abinka da kwarare a fannin sai kawai Abdul ya karbi tayin maman malan ya kara lulawa duniya mai cike da lada yana hako du wasu arnawa yana kashe au cikin sauki Shi kansa ya tausaya mata a lokacin da komai ya lafa , cikinta ta damke tana hawayen wai yinwa take ji Taimaka mata ya yi da niyar ta fara wanka kafin ta ci? Sai dai ruf ta rufe ido kan sai ta ci Ido kawai ya tsura mata a lokacin da take kai loma bakinta , wato tana yin hannu baka hannu kwarya ba sasautawa Ba ita ta dan dakata ba sai da ta ji wajen da kamar an mata sata ua cike sannan ta dawo hayacinta harma ta fara jin mugun zogin da jikinta ke mata Sai a lokacin kuma ta tuna cewar ta rushe tsarin jan ajin da ta yi niyar yi in dai tana gabansa na cin abinci, wato sam ba zata yarda ya gane irin yannayin cin abincinta ba, sai gashi rashin lafiar da take son kai kanta asibiti wace ta sameta a kwana biyun nan na cin abinci ta tona mata asiri a gabansa Fuskarta ta tsuke, Ta mugun hafe girar sama da ta kasa , Ta hade gabas da yama Irin ba zata saki fuskar da za a kawo mata wargin bama Murmushi ne ya subuce masa yana kallonta Hannayensa duka biyu ya saka ya talabe habarsa, A hankali ya ce" ban taba hora kaina irin na jiya da yau ba Dara daran idannuwanta da suka sha wahala suka wani lumshe da su ta maido kansa, Bata yi masa tambaya ba, sannan bata daina kallon kyakyawar fuskarsa mai sakata jin yana fuzgarta Hannayenta ya kamo, du da kuwa ta so kin bashi, sai dai ta kasa hakan sakamakon babu wani karfi a tare da ita, tunanin bata da lafia ya fara damunta A hankali ya ce" Hafsat? Idannuwanta da suka fara cika da kwallah ta zuba masa tana kallonsa A hankali ya kuma cewa" ban iya karya ba, ban iya tsokana ba, ban iya wasa da wannan lamarin ba.....ni dai na samu kaina a ciki tun lokacin da kika kasance mai shiga lamarina, kikai min fada dan ina aikata masha.a Hafsat, shi ne damuwata, tashin hankalina, Hafsat du yanda na yi dan kar wani ya birge ki, sai da ya tashi ya wani shiga rayuwarki, ina ji ina kuma ganni harma zai aure ki Shiru ya yi yana dan murza hannayenta, Muryarsa ce ta kara yin wani irin sanyi ya ce" sai dai wani baya auren matar wani, can can dama Allah bai yi ba shine mijin ki, Idannuwansa ya dago ya sauke a fuskar tata, a hankali ya ce" zaki taimaka ki rufa min asiri, ki daina maganarsa ko tunaninsa? Walahi idan kika ci gaba lumfashina zai iya barin gangar jikina domin hakan na kai ni tunanin cewa har abada ba zaki tana so na ba dan kina da wanda kike so, Jikinta ne take ji yana amsawa da dukan kalamansa, Jikinta ne ya yi sanyi, A hankali ita din ma ta ce" Abdallah, tambayar da na yi maka a ranar nan ce ta saka ka daukan fushi da ni? Idannuwa kawai ya tsura mata ya kasa amsata Hannayen nasa ta dan jimke kafin ta ce" ban san dadin so da har zai kai ni haka ba, ban san muguntarsa da har zai kai ni tunanin wani da kalmar so bayan da aurena Koda makiyina na aura a duniya ina fatan daga bakin da na amsa kira da sunnansa zan girmama igiyarsa dake kaina Wacece ni? Me na aikata na tarin ladan da zan yi tunanin koda na kauce hanya haka zan ci riba wa wajen? Na yi maka tambayar nan ne da ina cikin damuwa, na yi maka ne dan ina cikin tunani mai zurfi, mamakin dan adam ne ya kashe ni na irin kalaman dan adam da suka zama na yaudara Abdallah ban san yanda zan kwatanta maka lamarina da Bashir ba, aman ka sani babu *kalmar so* a tare da lamarin Idannuwansa ya sada yana jin nauyin da kirjinsa ya yi masa ya ragu, Dadi ne ya ji na irin yanda har ta iya fahimtar da shi abinda ke ranta, ashe zata yi saukin kai da dadin zaman gidan aure haka? Ashe du irin taurin kanta da rigimarta da tsayayarta idan aka zauna magana ta fahimta da ita za.a ga laushinta? Ajiyar zuciya ya ringa saukewa kafin ya dago ya saka idannuwansa cikin nata, a yau ya kara gane wani lamari cewa Hafsansa baiwa ce da Allah ya bashi domin kuwa a wasan da ya buga da ita a yau ya nuna masa idan ta gama zama kwarariya idan ya shige daka sai safe A hankali yana kallon kwayar idannuwanta wa.inda ta ki cire nata dan tana son ya yarda da maganarta , sam ita bata wani saka maganar son Bashir ba , ta yi tambayarta ne dan gane dalilinsa na wulakantata a ranar aurensu Bata tsamaci kalmar da zai yi mata kennan ba, bata tsamaci zai yi mata wannan tambayar ba hakan ya saka ta shagalta da kallonsa tana jin dadin yannayinsa a ranta, rigarsa mai botira ce kawai ya dora saman gajeran wandonsa baki , bai baka botiran ba hakan ya bashi kalar black American din nan A hankali ya ce " *Hafsat? Dan Alllah, ni zaki so ni? Watarana zaki so ni? Kina tunanin na saka hakuri da juriya na tsayin lokaci watarana zaki so ni nima? Hafsat Ni Ina son ki* Ji ta yi tamkar za.a jefota daga kujerar da take zaune Dakin ne ta ji ya yi masu kadan su su biyu rak, A hankali ta fara jin lumfashinta na gudu ba kamar da ba, Ita dai bata da cutar athsma, sai gashi lokaci daya ta shiga huka da tari tamkar mai ciwon Athsma, Sama da kasa kirjinta yake nan da nan ta mike ta shiga neman wajen da zata je ta tsere ta labe kar ya kashe ta, Jikinta na rawa tama faman kaucewa rikotan da yake kokarin yi Kuka ne ta ji zai kwace mata, wani irin dadi da kuma tsoro ne suka haifar mata da emotions din da ta sakata tarin mai huka, zubewa ta yi jikinsa tana kallon tashin hankali karara a fuskarsa, Zata so shi? Shin watarana zata so shi? Shi yana son ta? Ita kanta sai ta tsinci kanta da yiwa kanta tambayar shin menene ke saka ta a irin wannan yannayin a duk lokacin da take tare da shi tun farkom lokacin da ta ganshi tare da mace na neman tubewa dan ta bashi kulawa irin wace bata cancanta ba a matsayinta na baligar da ba muharamarsa ba A hankali ta ringa tariyo irin yannayin da takan shiga a duk lokacin da ta je kakabe masa shinfidar da ta tabata ya je dakin matar nasa ne dan sqnub nutsuwa da ita duda ba hutuminta bane sannan ita Na.ima din ta kasance matarsa ta sunna sai ta wuni cikin kasala da bacin rai Tana tune da lokacin da aaka so harbinsa harbin ya sameta ajiyar zuciyar da ta sauke ba na ta samu kare mutun a kan aikinta take bane, aa, ta sauke nanauyan ajiyar zuciyar dake nunin ta ji dadin da ba shi ba aka harba abin ya sauka a kanta? Murnar aurenta da Bashir da ya taya ta sai ta tsinke waya ta ringa jin haushinsa? Shin na menene? A hankali ta ringa jin lumfashinta na daidaita a lokacin da ta fahimci idan ba da kyar ba tama rigaye shi fadawa a tarkom da ya fada na soyayarta, ashe itama zuciyar tata lusara ce? Har take jin haushin yan matan dake nuna masa suna son sa ashe itama halin da tata zuciyar take kennan? Har take mugun jin haushin matarsa irin yanda so ya sakata zama tana jurar kayan haushinsa ashe du jirgi daya ya kwaso su? Bambancin su kawai ita bata fito da maitarta ba, bambacinsu ita bata nuna ba, Ashe ashe tashin balagar tsararan shegantakarsa itama ya haukata tunaninta? A hankali ta saka hannunta ta bayansa ta rungume shi, Bakinta ta kai daidai kunnensa ta ce" is ok Abdellah Shima rungumeta ya yi a jikinsa yana mai jin tashin hankalin kar dai ba zata taba son nasa bane har ya sakata cikin wannan yannayin? Dan haka ya ce" i....i.m sorry, Hafsat ta lumshe idannuwanta tana mai jin yannayinnan fiye da kowani yannayi, dama haka ake ji? Kamar ya kunna wani abu ne a jikinta dake mace a da, can kasan zuciyarta ta masa shi da I love u too, aman a fili sai ta ce""""""" Saura kiris....eh saura kirisss in sha Allah *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA