← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 94

Sashe 81

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafsat ba zata koma gidansa ba, sai dai ta yi gidan su Sosai malan ya yi mamakin ganninsa an sauke shi a adaidaita sahu, Bai gama mamakin ba wani mamakin ya sake kama shi jin Abdul ya bukaci da a biya mai adaidaitan Shi dai malan cirewa ya yi ya biya sannan suka zauna tare da almajirai ana ta karatu Abdul ya yi tsuru tsuru yana bin malan da kallo, shi kuwa malan ya maida hankali tun bayan da suka gama gaisawa da Abdul din kan dalibansa Sai da ya gama yiwa wa.inda zai yiwa kari, ya kuma karbi harda wajen wa.inda zasu kawo sannan ya takaita dogon zaman karantun ya yi masu salama A hankali suke takawa shi da malan har suka samu wata sansanyar innuwa suka zauna Malan ya fuskanci Abdul, sai da ya dan kara kallon yannayin shigarsa, lale mutun ne mai son saka jalabiya, sai dai shirin abin kallo ne A hankali ya ce" Abdallah, yannayinka bai kwontar da hankalina ba Abdul dake ta kale kale ya dubi malan, a hankali ya sauke boyayiyar ajiyar zuciya sannan ya ce" Malan, a gafarta min, ni din mai laifi ne Malan ya kara fuskantarsa da kyau, a hankali ya ce" me ke faruwa ne?? Abdul ya sada kansa da kyau, can ya ce" dama ta taba nuna min bata son irin haka tun a lokacin da muka yi zaman aiki da ita, tsoron irin rayuwar da na gani, na kuma aikata a da can baya kafin na shiryu ya kasa barin zuciyata har nake daukan mataki, hakan ne ya hasalata har ta min fushi da munanan kalamai, Malan har cewa ta yi wai ta tsane ni Malan dake sauraronsa ya dube shi da kyau, duda bai fahinci laifin da ya aikata ba, domin kuwa Abdul din sam bai fadi laifin nasa ba, sai dai ya ji mamakin mugun furucin da ta yiwa mijinta, miji fa? Miji mai daraja? Ashe du irin nasiha da gargadin da ya bata lokaci mai tsayi yanai mata a banza ne? Bai taba jin ya mugun ji haushin mamansa irin na yau ba, ashe ba zata saduda da duniya ta gane ba gidan zama bace Malan bai iya cewa Abdul komai ba, sai da ya sauke ajiyar zuciya na bacin ya fi a kirga sannan ya ce" a ina take ne maman?? Abdul dake sasada kai cike da kunya ya dan dago jin kamar ton din voice din malan ya canza , a hankali ya ce" na san ta zo gidan ne dan ranta a bace ta shiga adaidaita Malan ya gyada kansa, nan ya kara tabatarwa kansa cewa lale bata san ciwon kanta da na mahaifiyarta ba, yanzu ko dan gudun gorin yan gidansu ba zata yi hakuri ta zauna gidan mijinta ba? Mutumen da shi bai gujeta ba , a irin yanda aka so wulakanta ta, ya dauka ya ce shi a daura da shi, shine zata furtawa ta tsane shi, Sai.ma ya ringa jin haushin Abdul din kansa dan ya nuna muguwar damuwa da shi, a nan take kuma ya shiga tambayar kansa....shin ya mugun sangartata ne ya saka ta irin wannan lamari ko me? Bai iya cewa komai ba sai shiru da ya yi da bakinsa ya mike ya yi gaba Abdul ya mike da sauri yana dan sosa kansa ya bi bayan malan Wajen mitar suka nufa malan ya masa bismillah, wato yana nufin ua shiga Abdul ya bude ya shiga motar ya yi shiru yana kallon waje guda Sai da Malan ya tayar da motar ya fara tafia kadan kadan sai kuma ya take birkin, kallon Abdul ya yi ya ce" kai, dan me ka zuba mata ido ta yi maka rashin kunya baka lakada mata duka ba? Kai zaka bari ta ringa haka ne? Mamana fa idan ta samu haka ba zata taba jin magana ba, mamana ce, ni na haifi abina, na san wacece ita ! Abdul ya tsurawa malan kawai ido, duka, wai ya daki Hafsat, hm Malan ya kuma tayar da motar ya dauki hanyar gidan Abdul na lure da yannayinsa, kamar ransa ya baci sosai, sai dai ya kasa yin wani abin yana dai biye da shi Malan na zuwa ya ja ya tsaya kofar gidan Sauka ya yi ya nufi cikin gidan bayan ya umarci Abdul da ya tsaya Bai jima da shiga ba ya fito, Tsaye ya yi yana kallon yannayin garin, Hankalinsa ne ya fara tashi bata gidan, bata zo ba Juyawa ya yi ya karbi waya a hannun baban yaronsa ya lalubo number yayarsu Amsar da ta bashi bai ji dadinta ba, domin rabonta da Hafsat tun da suka rakata gidanta wai A haka ya ringa kiran yayan nasa har ya fada kan Mariama Inda infa ta fara a lokacin da ya tambayeta Hafsat, Kashe kiran kawai ya yi, ko hular kansa bai cire ba ya koma motar ya tayar Tun da yake bai taba zuwa gidan yar tasa ba, bai taba zuwa ba ko da wasa, ko bata da lafia yana jira har ta zo da kanta sannan sai gashi yau bai jira an yi masa iso ba bai sanar da zai zo ba ya yiwa gidan tsinke bayan ya umarci sirikin nasa da ya biyo bayansa su shiga Nana mariama dake tsaye bakin Pamp ta dago da sauri jin muryar mahaifinta da kuma kamshin turaransa Idannuwanta ta kwalalo waje baki daya, lokaci daya kuma ta gyara zaman hijab din jikinta ta ce" Aba??? Malan ya gala mata wani mugun harara, ransa bace ya ce" ina take?? Marima ta yi gagawar juwaya ta tafi dakin, bata jima ba sai ga Hafsat ta fito, a kan rigar nata dan kwali kawai ta dora ba abinda ya shafeta , Tana fitowa ta nufi malan da yannayin rigima Bata san da haka ba, bata taba tunanin haka ba, bata taba zaton hakan zai faru ba, sai ji ta yi na farko a rayuwarta mahaifinta ya wanka mata mari Daga Abdul, har Nana mariama idannuwa suka zaro a fili a tare kuma suka Furta Aba Ba.a taba yi ba, hakan bai taba faruwa ba, malan bai taba daga hannunsa a kan mamansa ba, bai taba taba lafiar jikinta ba, hakan ya saka lokaci daya Hafsat ta duke a wajen a kan kafafuwanta Kanta ta sada kasa, gaba daya jikinta ne ya dauki rawa Hankali tashe Abdul ya nufeta, yanda ta dukan shima ya duka, gaba daya jikinsa ne ya kwashi rawa, lokaci daya kuma ya kuma dago da dubansa ya kali malan, muryarsa har rawa take ya ce" Aba, nine da laifi fa, walahil azim nine da laifi ba ita ba, Aba ka san me na mata? Aba magani fa............. Da sauri ta dago , duban da ta yi masa bai hana shi son karasa maganar tasa ba, gannin da gaske fadi zai yi ta saka hannunta da sauri ta rufe bakinsa, lokaci daya kuma hawaye na zuba a idannuwanta tamkar an bude fanfo Aunty nana mariama dai jikinta ne ke bari tana kallon mahaifinsu, Bata taba tunanin zai saka hannunsa ya mari mamansa ba Mamaki ne ke neman kashe malan gannin wai Abdul haushi ya ji dan an daki mamansa bayan yanzu ta gama rashin da.ar ce masa ta tsane shi! Ita kanta maman nasa kuma bata so mijin nata ya fadi laifinsa Daina cewa abinda ya yi niyar cewa ya yi, sai kawai ya ce" ki tashi ki koma dakin ki, shi ne tabatuwar kwonciyar hankalinki mamana Yana gamawa ya juya ya fita, Yana fita Hafsat ta saki hannunta daga bakin Abdul ta mike Da sauri ya mike ya bi bayanta sunna shiga dakin nana Mariama ta ja yan yayanta ta hana su shiga ta zauna sai zarar ido take Abdul na bun bayanta ya ja ya tsaya , a hankali ya ce" Hafsat.... Hafsat kamar jira take ta juyo da sauri , cikin bambami ta ce" me kuma kake so? Mahaifina ka je ka tiso? Me yasa ba zan yi daraja a idannuwanka ba Abdul ka dake ni kuma ka hana ni kuka? A hankali yake binta da kallo, sam baya sonta da irin haka, A hankali ya ce" ki daina daga min murya Hafsat, ba kyau..nine mijinki, ke kuma matata, ba kyau kina daga min murya komai bacin rai Hafsat ta yatsina fuskarta ta juya dan cikinta ba wai gaba daya ya daina murda mata ba, Juyawar da ta yi a hankali ta durkusa tana kara damke mararta Da sauri ya je wajenta ya duka shi din ma ya dora hannunsa a saman cikin nata, Shafawa yake yana adu.a a hankali a hankali har ya lafa mata, Muryarsa ce ta kara rikicewa a lokacin da ya ce" ki yi hakuri, ban yi haka dan bana son ki ba, hasalima ban san idan zan kwatanta maki kalmar nan ta inda zan bi ba Hafsat, ki yi hakuri, ki rufa min asiri mu koma gidanmu, ba zan kuma ba, ita kanta Na.imar zan hana ta sha Hafsat kar ki guje ni dan na kasance mai laifi, kiyi min nasiha ki dawo ki cancane ni, Fada fa kike min ki tirsasa ni abinda na kauce, dan me yanzu zaki guje ni? Dan Allah, na tuba...kin ji? Hafsat da idannuwanta ke lumshe, tana sauke ajiyar zuciya tana sauraronsa Abdul ya tsurawa fuskarta ido yana kallonta shima, Sai kuma ya ce" ba ki yi karya ba da kika ce zan so ki dan albarkatun jikin ki, kin san me....nutsatsu ne, wuta suke badawa, suna lasa mon zuma a baki...dan Allah ni da lafiyaye ne dan me zan munafurci kaina? Hafsat, kina da ni.ima, kina bada kala....bakya shaye shayen komai ko cushe cushe...aman kuma tun da na bi hanyar kulum shinfide take da ni.ima , ina son jikin ki sosai kauriyata Yana fada ne yatsarsa mai bima baba na bin dogon hannunta a hankali yana shafawa, Sai kuma ya ce" a haka kika bi layi, dan kawai kina fushi da ni ko?? Hafsat ta dan buda idannuwanta ta dago da duban nata kadan, a hankali ta ce" ba fushi nake da kai ba, tsoron zama nake da kai....ba zaka iya rayuwa irin na mutane bane Abdul? Muna zaune a gidanka mata biyu, ba abinda ya dame ka da muna zumunci ko bama yi, hasalima
Chapter 81 · 0% Book details