Sashe 91
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baby Idannuwanta dake kallonsa ta ji sun mata nauyi cike da hawaye A hankali ta ce" Abdallah *I LOVE U* gaba dayansa ya ji kafafuwansa zasu gagara daukansa, hakan ya saka shi zama saman kujerar dake ajiye kusa Idannuwansa ya lumshe, sai ga wasu hawaye masu dumi Yau babar rana ce a gare shi, yau ya tashi cike da ni.ima , Alhamdulilah shi ne abinda ya iya fada Sai kuma tunanin mahaifinsa ya diro masa a zuciyarsa Dama haka ya ji a lokacin da ya san matarsa na dauke da cikin dansa na farko? Kai, wannan madaukakiyar soyaya ita uba ke ji idan ka ji zaka samu yaro? Ajiyar zuciya ya sauke suka mike ya kama hannunta dan du yanda ta ki sai da ya riko gam a hannunsa suka fito Murmushi kawai yake saki, sai ya kaleta, ita kuwa kunya ta cikata dan likitocin nan sun sha dariyar irin yanda ya zaburo ya ringa bata muah du inda bakinsa ya kai cike da murna da farin ciki gabansu ba wani kunya , harma suka yi sabo da doctern inda ya kara fahimtar inda ya nufa harma ya ji ya birge shi A hankali ya karasa anguwar da malan ke zama , Farin ciki ne ya mamaye zuciyarta a lokacin da ta hangi mahaifinta zaune cikin shigarsa ta kamala Tana kallon yanda Abdul ya duka yana gaishe shi aman Malan ya mikar da shi yana ta doka masa murmushi Tana kallonsu har suka karaso wajen motar aka bude nan Malan ya yi tozali da yarsa da yake ji tamkar nama daya kwal a cikin miya Murmushi ta yi hannunta cikin na malan, shima yana kallonta yana mai jin farin ciki a ransa, ko ba.a fada masa ba shi ba yaro bane, koda basu sani ba shi ya fahimta, yarsa ce fa, shi ya raini abinsa, ya gane me ke tare da mamansa, lale ya godewa Allah, murna ce cike da ransa wace ya salame su bakinsa kamar ya kai kunne Gidan mama ya ajiye Hafsat inda ya ki shiga ya ce da ita zai je wani waje ya dawo Bai zame ko.ina ba sai kasan wata bishiya mai cike da innuwa sanyayen waje ne mai cike da ni.ima Zama ya yi waje guda ya dauki wayarsa ya danna kira Kiran na shiga aka daga Shiru ne ya dan ratsa kafin a hankali ya ce" ka dawo cikin Gari Abu Abdellah Da sauri mahaifinsa ya cire wayar ya kali sunnan, ya kuma mayarwa a kunnensa Bakinsa na rawa rawa a hanklai ya ce"""" *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 6 A hankali ya ce" Abdu? Abdul ya yi murmushi mai sauti ya ce" Abih Ajiyar zuciya ya sauke, da sauri ya ce" dama zan kuma jin sunnan da murmushi a lebenka? Abdul ya kuma yin murmushi bai dai ce komai ba Abdul Basitt ya ce" ko yanzu Allah ya amshi raina na cika burina Abdallah, na gode, na gode, baka san irin farin cikin da ka saka ni a yau a yanzu ba, baka san irin yanda na ji a zuciyata ba Abdul ya ringa sauke ajiyar zuciya shima jinsa yake sakayau, ashe ka riki mutun kanai masa fushi da gabama ba wai wani jin dadi bane sai tarin nauyin fake azuwa saman zuciyarka da faduwar gaba idan ka ji sunnansa? Mahaifinsa ya tafka kuskure a rayuwa, ya aikata laifi mumuna na hanyar saduwa da yar da ya haifa, sai dai hakan ya faru bisa sharin magabata, sharin abokan zama , banzayen abokai masu kai mutun ga halaka, An kasheta dan a dora masa laifi Ya yi nesa da su dan tarin kunyarsu, yana jin kunyar haduwa da mahalincinsa a irin wannan rayuwa hakan ya saka shi kauracewa kowa ya kadaice kansa da neman gafarar ubangijinsa da neman zabinsa Dansa cilo ya rayu cikin kunci da tunanin bayan bata rayuwar yar cikinsa shi ya kasheta haka kuma ya kashe mahaifiyarsa sannan yake bibiyar rayuwarsa dan dukiyarsa Du irin abubuwan nan suka taru suka saka gaba mai tsanani da rashin fahimta tsakanin dan da uban Aman da yake buwayi gagara misali ya kaiwa kukansa Ya duka ya zubar da komai nasa Ya kasance babu wani abu tsakaninsa da Allahnsa wanda bai fito ya fada ba, Ya yi kukan jin kunyar ubangijinsa da irin abubuwan da ya aikata Ya nemawa yarsa da matarsa gafara Ya kuma roki da ya tausasa zuciyar dansa cilo ya kasance koda shi daya zai wanki gawarsa ya yisa yana mai bi a hankali yana yi masa shinfidar kabari mai ma.ana, Sai gashi sarkin sarakuna Mai mulkin da ba algus Wanda zaka roka ya baka in ka kuma roka ya kara maka ya yi ta baka ba tare da ya gotanta maka ba Wanda zaka yiwa laifi mai tsanani idan ka tuba ya karbi tubanka harma ya daukaka ka? Mai annabi aban fati ya nuna masa ranar da dansa na cikinsa ya nemi da ya dawo kusa da shi bama a ya mutu ba Bashi da bakin magana, Bashi da abin mamaki Burinsa ya kafaice ya kai sujada Idan goshinsa a kas yakan ji kansa sakayau ne, yana jinsa a cikin nishadi kasancewa a fadar Allah, zai je ya tsaftace wajen salarsa, ya kara saka turare ya kai goshinsa kasa ya yiwa Allah kirari, ya yabi manzanninsa da sahabansa Zai rubar da hawayen farin ciki kafin ya tatara ya kaura kusa da shi Cikin muryar farin ciki ya ce" Abdallah, Alhamdulilah Abdul kansa dake jin dadi har ransa ya ce" Abih, zan so ka zauna cikin gidana, kusa da mu duka , Abih zan so matana su yi zumunci da soyayar junansu, zan so su zauna da ni da zuciya daya Abih, basa fada, basa gaba, sai dai basa shiga harkar junna kuma daya bata damu da halin da yar uwarta ke ciki ba Shiru Abih ya yi , tun da ya ce ya koma cikin gidansa da zama da ta fado masa a rai, Da gaske ya huce harma zai yarda ya zauna tare da matansa bayan ya afkawa yarsa ta cikinsa???? Abdul ne ya katse masa tunaninsa ta hanyar fadin" yanzu ita Kauriyata dake cikin wannan yannayin idan aka yi katarin tana da wani bukatar ni kuwa bana nan sai dai ta yi hakuri? An ce ba.a son mai ciki ta nemi abu ta rasa, idanma haihuwa ta kamata bana nan yaya za.a yi kennan? Ko hali na rashin lafia? Wani murmushin ya saki a fili ya ce" inyeh, zan zama papy? Ita maman malan din? Shiru abdul ya yi, sai kuma ya ji wani yannayi mai shige da kunya ya kama shi, A hankali ya kashe kiran yana sosa bayan keyarsa yana murmushi, Message ya shigo masa mai tsayi , budawa ya yi ya karanta kamar haka" kai zaka zama jajirtacen namiji a cikin gidanka Abdu, kai zaka hada kan matanka, sannan ka yi ta adu.a Zan dawo cikin gari kusa da kai aman ba zan zauna da tsufana da komai a cikin gidanka ba , aa ba zan sakawa yara ido ba, zan dai kama wani gidan da ya fi kusa da kai, sannan ka sani ba zan lamunce su dorawa dana daya cilo hawan jini ba, koma waye zan dauki tsatsauran mataki a kansa ehe! Murmushi Abdul ya saki, sai kuma ya rubuta "HARDA KAURIYATA ABIH? murmushin shima ya yi ya ce" *Eh harda maman malan, kai koda kai da kanka ne* Jinsa yake cikin nishadi, karshe dai hirar haka ta kare ya dauki hudubar Abansa cewa ya yi masu jan ido idan suka ki shirya kansu, zaman kishi ai ba hauka bane, kuma aure sunnan ma.aiki ce Hafsat dake gidansu yau ta yi matukar mamakin irin yanda mamanta ta ringa nan nan da ita, Bata gama mamakin ba aka shigo da kayan kwadayi wai malan ya ce a kawowa mamansa Ai kuwa ta hau tande tande tana murna dan kuwa azumi tun a wajen likita ya fice domin sai da ta cika cikinta da ruwa kafin a yi mata aikin da farko ta so kiyawa Abdallah ya ce shi ai dama ba da izininsa ta dauki azumi ba, ita dai bata ce da su ga abinda ta kunso ba, kuma bata fahimci sun fahimci hakan ba sai ta dauka dan ta jima basu hadu bane ya saka su yin nan nan da ita Halayen matan mahaifinta na nan yanda suke, amarya ce ta yi yaji wai malan ya kwashe kayan abinci kaf da dukiyarsa ya aikawa yarsa sai kace ita daya ya malaka wai gara bayan mijinta ya ce ya hutashe shi aman ya cika motoci aka kaiwa maman malan abinda bai taba yiwa wata yar ba dan rashin adalci irin nata bayan malan din bai yiwa mamansa kayan daki ba, wannan din ma fin karfin abdallah ya yi! Ita dai sha.aninta ta wuni yi hankali kwonce,, nan kafarta ta mike jikintama haka ta samu ta samu walwallah sosai domin kadaici mugun ciwo ne Sai yama Abdallah ya je daukanta nan ya shiga ya gaishe da su mama cikin jin kunya da girmamawa kafin suke mikewa su fice Sai da ya yi yawo da ita a garin Niamey har kiraye kirayen sallar magarib ya fara kafin ya dakata wani waje su gabatar da sallah baki dayansu domin nesa suke da gida Sai bayan sun gama ya dauki hanyar gidansu , Yana tafe yana yi mata hira cikin nutsuwa da birgewa suna cikin nishadi har