← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 94

Sashe 30

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a idannuna ba! Zan so ki kiyaye dokokin gidan nan ki yi doguwar rayuwar da zan iya rayuwa da ke ! Idannuwanta da ta ruruko dan masifar dake cinta na son ta ga mahaifanta, gata ga mahaifinta ya saka aka kamota ta matso sosai kusa da shi cikin murya kakausa ta ce" mahaifana? A raye? A cikin kasa daya da ni? Zaka hana ni ganin su? Shima muryar tasa ya kausasa ya ce" du lokacin da kika yi kokarin guduwa harbe ki shi ne abinda aka ce na yi! To ka harbe ni mana! Ka harbe ni na huta da wannan rayuwar! Ka harbe ni su tabatar da na mutu da rayuwar da suke a matsayin wada na gudu dan gudun auren dole ko me? Ki fice! Ya daka mata tsawa yana kara kusancinsa da ita, Idonsa ya saka cikin nata har jijiyar goshinsa na kara tsayawa dan neman balaki ya ce" ki fice a nan! Idannuwanta ta lumshe dan kokarin mayar da hawayen dake son kubce mata sannan ta karbi abin kunnenta ta mayar ta juya ta fita a motar ta shiga gidan dake zagaye da masu tsaro ta katanga ba tare da sun san da shigarta ba, Tana zuwa waje ta samu ta tsaya ta sada kanta kasa, Wasu irin hawaye masu zafi ne suka shiga bin kumatunta, ta sani ne, in dai wannan maganar ta fita zuwa manyansu to fa za.a iya mayar da ita *KUTKALE*. Gaba dayansu ya tara su su ukun ya tsare su cikin yannayin da ba zasu taba gigin tunanin da wasa a lamarinsa ba ya ce" koda wasa, na tsinci maganar cewa mun kamo BD 01 ta je gannin mahaifinta sai na bibiyi daga inda maganar ta fito na hana mutun zaman lafia! Da hanuna zan shakewa mutun wuyansa har ya daina numfashi! Haka ya gama da su ya koma motar ya zauna ya kai hannayensa saman kansa yana shafa kan cike da yannayin rashin karfin jiki, A cikin zuciyarsa ya ayyana *Sonki nake, kuma ni ne mai rabin samun ki* (ko?) Bai wani jima sosai ba maganin bacin ya sake shi, nan ya ga an dadaure jikinsa jikin bed din da yake kwonce magani na shiga cikin jikinsa, A hankali ya ringa gani da kyau har ya sauke idannuwansa kan sojojin kasar saudiya tsaye kusa da prince Muhammad, Gefe daya kuma kanwar mahaifiyarsa da ta yi saura a family dinsu ce zaune da dogon hijab dinta blue mai ruwan byro, dakin shiru kowane cikinsu na jan carbin dake hannunsa, yannayinsa zai nuna maka halin da zuciyarsa ke ciki, A hankali ya maida idannuwansa ya lumshe dan basu san da ya farka ba, Wani zazafan hawaye, mai mugun zafi da radadi a kwarmin ido ne ya samu damar tsinke masa, Abinda ya hango a lokacin da ya shiga gidan mahaifinyarsa, mamansa ce yashe saman tiles din tsakar gidanta, hasken motar da ya dala ya nuna masa harbin bulet din da aka dana mata a gaban goshinta, Zai iya tuna cikin al.adarta ne idab ta kore shi, tana biyowa tace da mai gadi idan ya dawo yace da shi ta yi tafia, dan ya dauki maganar da suke da mahinmanci, A dalilina, aka kashe uwata? Ni na kashe ki Ummih..... Bugun zuciyarsa ne ya tsananta hakan ya sa injin dake jikinsa mai shaida yannayin hawan jinninsa ko saukarsa ya shiga shaida jinninsa ya fara hawa, Da sauri Muhammad ya nufo wajen gadon yana kiran sunnansa a hankali, Kanwar mahaifiyarsa kuwa ta fita da gudu dan kiran docters, A hankali ya buda idanjuwansa da sukai masa nauyi ya kai dubansa kan Prince Muhammad, A hankali ya buda bakinsa da muryarsa da ta canza amo ya ce" Muhammad, ya haka aka kule ni tamkar mahaukaci? Muhammada na son fada masa dalilin daure shin da aka yi ya ji ya daga murya da karfin amo ya ce"....... Alhamdulilah, an gama freee Du mai son ci gaban labarin naira dari biyu ne ga yan Nigeria, Yan niger kuwa dala dari ne sahelcom ta numberna kamar haka 91466605 *Taku ce, yar mutan niger* *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 2 *wannan nvl na kudi ne, idan kin biya kin shiga na roki alfarmar dan girman Allah ba dan ni ba kar ki fitar min da shi ki yi hakurin har na gama shi sai ki fitar da abinki ki yi yanda kike so da shi bani da matsala da hakan, dan Allah idan kin san dan fitina, ko dan ki wulakanta min kika shigo ki min magana pc daga ni sai ke na biya ki kudinki wato naira 200 ta hanyar accnt din ki ko kati, dan alfarmar soyayarku da annabi muhammad kar ku fitar min da novel, ku bari na gama shi, in sha Allah ba mai tsayin da zai saka ku gajiya da jira bane na gode* Likita ne ke ta kokarin danna kirjinsa, Kin dawowar da ya yi ne ya saka fa sauri aka kawo abin dannar kirji Aka mikawa likita aka matso likid din nan aka goga a sama sannan aka shiga kokarin kara tayar da shi ta hanyar murza abubuwan nan biyu aka dora saman kirjinsa, Sai da ya dago baki dayansa sannan ya koma yarab tamkar matace Wani ihu BS ya saka a fili ya furta" shikenan, ya mutu, mun karasa masu aikin su, mun kashe shi! Kallon da docter ya yi masa ne ya saka daya daga cikin nurse kokarin fitar da shi yanzu kam, sai dai tirjewar da ya yi ya sakata sakinsa ya kara dawowa yana kallo za.a dora masa a karo na biyu Sai da aka kara jonawa aka dora masa, Wannan karron kam alhamdulilah, yana yin saman da kirjinsa sai ko injin ya shiga bada wani kukan dake nuni da ya dawo duniyar masu rai, Da sauri Doctern ya shiga gyagyara du abinda zai gyara nurse na daimaka masa tana bashi du abinda ya ambaci sunnansa, A haka suka gama komai sannan du suka tsaya sunna kallonsa, Nurse di Docter ya umarta da su je, bayan ya cire safar hannun ya rage daga doctet sai BS tsaye kuri sunna duban Abdull Ya jima, ya jima sosai, domin a kadan ya dauki minti talatin a wannan yannayin , Sai can ya shiga kokarin bude idsanuwansa, sannan bakinsa ya shiga motsawa yana mai adu.ar tashi a barci Kamar kuma wani hadin baki sai wani bakin jinni bulbul ya bulbulo daga hancin wanda ya sanya Docter zabura ya nufe shi ya saka abu yana dauke jinnin, inda Abdul ya ringa jin wani sanyi sanyi wani sakayau, a hankali abinda ya rike gansa da wani irin nauyi da duhu ya ringa barinsa har ya sake shi baki daya, A hankali ya bude idannuwansa da suka kara girma sukai jajajir ya sauke a kan BS da docter, sai da ya gama yi masu kallo, sannan ya juya ya shiga bin dakin da yake kwonce da kallo Shi dai bai ce komai ba, har aka jima sosai domin Docter ya fice da jinnin dan aunawa gannin abinda ya hadasa masa haka, ya rage daga shi sai BS sun yi shiru su duka ba wanda ya ce wani abu, ba wai dan muryar Abdul bata dawo ba, aa kawai bin BS da kallo yake yana tunna wasu abubuwan da ya gani da wanda yake tine, saima suturar dake jikinsa wato daga shi sai gajeran wando Docter ya jima da fita kafin ya dawo, sai da ya dawo yake tambayar ya shi ko sha wani abu? BS ya ce" ai bai fara magana ba har yanzu bare na ji abinda yake son ci Docter ya juya wajen Abdul dake dubansu ya ce " to ka kwatanta masa mana, idan baya magana na san abin wahalar da ya sha ne kafin muryarsa ta saki, Matsowa suka yi su duka biyun sunna duban Abdul, nan fa suka shiga kokarin yi masa yaren kurumci sunna kwatanta masa abin ci ko na sha wane yake so, kuma wani kalla? Sai da ya kare kalle su baki dayansu sannan ya yi murmushi yana kokarin mikewa zaune Kama shi suka yi suka zaunar da shi, nan ya dube su kuma, sannan ya ce" bana jin yinwa A tare suka dubi junnansu, kai dama yana magana ka ce bai fara magana ba? Docter ya tambayi BS S kam mamaki ya hana shi magana bale ya baiwa docter amsa, sai kawai ya shiga murmushin shima yana duban Abdul na kokarin cire allurar dake bashi karin ruwa da kansa, Docter ne ya ce " aa kar ka cire, wannan na karin ruwaa ne ko zaka ji dadin jikinka Abdul ya dubi docter da kyau ya ce " likita, ina jin jikina da wani irin karfi walahi, ban jigata ba, hancina ne ya dan zubar da jinni, ba.a dake ni ba, Docter kam zuwa wannan lokacin baima san abinda zai cewa bayin Allahn biyu ba, Abdul ne ya dago yana kallon yanda Docter ke kwonce masa yan abubuwan allurar da ya saka ya sasaka masa a jiki ya yi kamar ya daure shi ya ce" likita, bana son ana daure ni, du sai na ji na rikice , in dai ba mutuwa na yi ba, kar a daure ni Docter kansa kawai ya gyada ya karasa kunce Abdul yana son fada masa sai gobe za.a salame su, domin yama ta yi an fara kiraye kirayen la.asar sai gannin Abdul ya mike ya yi yana kallon dakin
Chapter 30 · 0% Book details