Sashe 7
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kam, (wayo Ni.imana, ashe ke wuni da gashinma ba na dalili bane? Yau kam zaki yi gashi) Yana fitowa ya tarar da ita dai tsaye, Gaba ya yi tana biye da shi a baya har suka shiga dakinsa, Suna zuwa ta kakabe shinfidarsa, ta bude frij ta ciro hollondiar nan biyu da ruwan gora ta ajiye ta juya ta fice a dakin inda ya rakata da kallo kafin ya zarce bayi dan yin wanka........ Kwonci tashi, yau har kwannan su Hafsat goma a gidan Abdul, sun ga fitintunnu da abubuwan mamaki da tarin takaici a tare da wannan bawan Allah, Abdul, bai taba yin wani yinkuri dan nuna masu yana son kare lafiarsa da ransa ba, bai taba basu damar su fuskanci inda zasu kare ba, Ya sha dan iya shege su fita ya zile masu du tsaron su, du kulawar su ya dawo gida kawai dan ya saka Hafsat ta yi ta balaki kamar ta kai masa mazga yana zaune yana dubanta yana murmushi, kuma du fitar da zasu yi, Hafsat na kula da takunsa basu taba fitar da ba wani abin mahinmanci na lamarin aikinsa ya fitar da shi ba, cikin dabara take hada abinda ta samu itama har ya zile masu! Kamar yau ma da karfe biyar na yama , Abdul ne ya fito daga dakinsa cikin shiga ta kayan gudu, wato yau dole su yi sports dai? Yana fitowa bai yiwa kowa magana ba ya dauki hanya ya falla da gudu, Sai da Hafsat ta dora hannu a ka gannin wani balakin kuma, sannan ta cire rigarta ta sama ta fala da gudu ta bi bayansa hakama su BS gaba dayansu sunna biye da shi da wani irin gudu , Sunna shan kwana, kamar daga sama wata bakar mota ta shanyo kwanar a guje ta ........... . ........ *Toh fa, lamarin na Abdul ba sauki Ku yi hakuri da yannayin rubutuna, ina iya yina dan baku pages mai yawan gaske a hakan, ku min uzuri plz *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 2 Koda Hafsat ta koma dakinta wanka ta shiga ta yi ta fito ta saka wata riga fara dake cikin kayanta ta zauna tana kallon waje guda, Kwata kwata wani lokacin idan ya yi irin abubuwan nan sai ta ji ta tsani kanta, Mikewa ta yi ta dubi madubi, Tabas yannayinta tamkar ba yar musulmai ba, suturar jikinta a kulun ba kamilaliya bace irin ta yayan musulmai, Gashin kanta rabon sa da dan kwali ya zauna daram a kanta ba lokacin sallah ba tun tana gidan mahaifanta, Sam aikin zama bodyguard ba aiki ne da zai ja maka mutunci da girmama ba a kasar Musulmai, Kai dai kulun ka kare a saka wando, da rigar da ba zasu iya hanaka gabza fada ko dankarawa da gudu ba ? Kai dai haka zaka kare a bushe? Zama ta yi tana mai jin haushin irin yanda yake nuna mata iya shege a fili duda ba shi ne na fari ba, aman nasa na yi mata ciwo, bata san dalili ba, bata san me yasa du idan ya ambaceta da gardi, ko yace da ita a bushe sai abin ya yi ta yi mata yawo a kwonya! Tsaki ta ja tana zabgawa bed din da zata kwonta harara a fili ta ce" ba dai na shayar da uban ba, aa shima na mayar da shi cikina na haifo shi! Kuma gwarama na bar aikin naka dan banda neman kai ni barzahu ba abinda yake, ga wulakanci! In sha Allah zan tafiata gobe ka je ka zama abinda zaka zama sai me? Idan ban samu incin daga wannan aikin ba sai me? Na yi hakurin duka wannan lokacin dan wannan ba zai kashe ni ba! Haka ta yi ta magangannun bacin rai, har ta raba dare kafin ta yi kwonciyarta a nan kasa ta nemi rintsawa, Du irin yanda ta cika dare, kiran sallar farko a kunnenta, dan haka ta ciciba ta mike tana mai jin hannun ya dan yi mata nauyi dan kuwa ko ba komai ciwo ne da ya kwana ya yi tsami bale harbin bindiga Zuwa ta yi ta yi wanka, ta kiyaye wajen bata jika ba, haka ta gama du wani uzurinta ta dauro alwallah ta fito, A daidai lokacin da take kokarin tayar da sallah ta ji shigowar mota, A hankali ta daga labulen dakin tana hange, Bakar mota ce ta shigo , gannin BS tsaye a wajen motar ya sakata juyawa ta tayar da sallarta, sai da ta gama a nitse sannan ta dauki dogon wandonta baki da riga baka ta saka, rigar mai karamin hannu ce bata dora ta samanta ba dalilin ciwon hannunta, Bata shafawa fuskarta komai ba, sai harhada kayanta da ta yi cikin yar akeatinta dama kayan ba wasu masu yawa bane sai bindigarta da ta daura a tsatsonta ta ja rigarta ta rufe bindigar, Wajen madubin dakin ta je ta tsaya, tsurawa madubin ido ta yi, a hankali ta furta" shikennan, haka zaki bar shi tsakiyar wannan tashin hankalin? Fuskarta ta yatsina ta dubi madubin da kyau ta ce" kwarai, mutuncina, da son haduwa da iyayena ya fi mani aikin nan da kowama, dan haka zan kara gaba! Murmushi ta yi ta duka ta dauki akwatin ta shiga janta a hankali, kanta bude ba dan kwali sai gashin kanta da ta daure da dan karamin ribom, A lokacin da ta fito katon falon gidan, BS ne kawai tsaye , Ido ya tsura mata, kai yarinyar ta hadu ne, du irin gudun da aka sakata bai saka mazaunanta rage fadi da tudu ba, cikinta kiwa tamkar babu hanji a ciki, fatar jikinta wani urin fresh da ita, domin kuwa mayukan da sabulansu na wanka ba jagaliya bane, sun karbeta sosai, haka kuma gashin kanta baki ne sidik ba yambo ba komai, haka yake halitarsa ce, ga cika ga madaidaicin tsayi, gaban goshinta ya fi cika da suma luflufluf haka yake, girar fuskarta har cajeta take ta daidaita ta yanda take so, hancinta ya ja ya tafi tsuwait har kusan dan karamin madaidaicin bakinta mai dauke da lebunna kalar pink, idannuwanta manya manya ne masu hasken fari bakin cikinsu mai girma ne sannan ko ranta ya baci sai dai su cicika da kwala, Shi kansa bai san da ya zuba mata ido ba sai da ta zauna saman kujerar zaman mutun daya bayan ta mayar da jakarta gefe ta dan jingina suka shiga zaman jiran fitowar Abdul da ya san da zuwansu tun jiya da sare A hankali ya karasa inda take zaune ya zauna shima, Sai da ya hadiyi yawun neman kwarin gwuiwa ya ce" fuahi ake da ni ne? Bata buda gazar gazar din gashin idannuwanta ba ta girgiza masa kai kawai, Kyakyawan dogon hannunta fari kal wanda baya dauke da gashi ko dis , damtsen hannun shar da shi du irin formation din da ta samu bai saka ya yi mundil mundil da shi ba, ya dan kara girma aman bai zama wannan kigi kigi din irin na maza ba ya bi da kallo, Sai da ya karewa wajen kallo sannan ya kai dubansa kan fuskarta, da son samunsa ne, ya watsa mata selfi a ajiye a gaban wayarsa ya ringa kallo idan ya samu lokaci sai dai ya san bama zai samu hakan ba dan haka a hankalin dai ya ce" yaya jikin ki? A hankali ta buda bakinta ta dane zuciyarta dan kar ta dankara masa magana ta ce" alhamdulilah Shiru ya yi shima, bai matsa a kusa da itan ba, bai kuma kara yi mata magana ba, yana mamakin irin yanda sam baya gabanta, ba wani ziga kai ba, ba komai ba irin yanda manyan yan matan cikin gari ke binsa yana jan su a kasa yana tafka masu iya shege da yaudarar soyaya sai gashi yana bin yar yarinyar nan tana faman jan sa a kasa, ko yanzu wace aka kawo ta canjeta babar bodyguard ce, kuma ta yi kudi sosai yanzu haka daga america aka daukota aka yo nan da ita, yar kwalisa , yar cakwas da ita, ita kanta soyaya suka yi ya yarda ita daga baya , ko yanzu yace su koma zata yarda da gudu ne, aman ita ga damarta a hannunta tana wasa da ita. Wasa wasa a nan a zaune sai da suka kai wajen karfe tara da mintuna, suna yi suna kallon agogo, aman ba Abdul ba alamunsa, Shi dai BS yana zaube bai yi gigin zuwa taso shi ba, hakama ba wanda ya yi gigin hakan domin dai su BS ne mai gidansu, umarnin da ya bada shi za.a bi dole, shi kuwa an fada masa waye Abdul din, dan haka yake kiyayewa Goma saura kadan alamun bude dakinsa suka bayanna , dan Haka da sauri BS ya mike ya koma wajen kofar ya tsaya hakama Hafsat ta mike tana jiran fitowarsa, inda BS ya shaidawa na wajen cewa zai fito dan haka kowa ya kama kansa Sai da Abdul ya gama wana kys din kofar sannan ya bude ya fito, A lokacin da ya fito maimakun ya tsaya ya bi abinda ake juransa dominsa, sai ya shiga dayan lungun da zai sada shi da dakin Muhammad, BS juyowa ya yi ya dubi Hafsat dake tsaye itama, Ai kuwa yannayin da ya nuna ita sai ya bata dariya ma, dan haka ta murmusa tana dubansa sannan ta kauda kanta, a ranta kuwa tana ayyana baka